INAAYA 3💖

466 38 1
                                    

INAAYA💖



Sound in alarm ne ya tayar da inaaya daga bacci ta tashi ta zauna kan gado na wasu seconds kafin ta shiga toilet ta dauro alwala ta fito, dogon hijab inta na sallah ta ciro tayi spreading prayer mat a kasa ta kabbara sallah tayi nafiloli sannan ta yi sallah asuba ta zauna a kan mat in tana karanta azkar inta har ta gama ta dauko al Quran tafara karanta suratul yasiin ta gama ta karanta suratul mulk cikin kira'ar ta me dadin gaske rufe Quranin tayi bayan ta gama karantawa da jawo wayarta taga karfe 6:30 komawa tayi kam gado ta kwanta har bacci yayi gaba da ita.karar buga kofa ne ya tashe ta daga baccin data koma ta tashi tana turo baki baccin bai ishe ta ba hakanan ta tashi ta bude kofa don ganin waye ya tashe ta da safen nan tana bude wa mamii tagani tsaye ta bata fuska tace sannu fatima kin kyauta sai ta juya ta wuce sai lokacin yayi mata occurring mamii tace zasu je gidan baffah ta tashi da safe, da sauri taje tana duba wayanta don ganin time tana dubawa taga past twelve da sauri ta fada bathroom ta yi brush da wanka ta fito ta shiga walk in closet nata taja stool wurin dressing mirror ta zauna tana shafa mai a jikinta da sauri take shafawa amma cike da natsuwa har ta gama ta fara neman kayan da zata saka wani lace ta ciro wanda akayi ma dinkin doguwan riga A line shape wani red sai daga kasan rigan anyi wani embroidery da black color saka shi tayi ya mata kyau sosai a jikinta ta shafa powder da khol kadai sai tasa lip gloss a bakinta daura dankwalinta tayi irin na zamani sannan ta dauko wata hand bag black ta louis vuitton a bag hanger dake cikin closet in, ta ciro takalminta na gucci shima black color sannan ta feshe jikinta da wani turare mai cool kamshi na cartier fitowa tayi daki ta ajiye hand bag inta da shoes ta sauka kasa tana sauri.mamii ce zaune kan kujera ta shirya cikin wani blue and silver lace dinkin doguwan riga yayi kyau sosai zama tayi kusa da mamii tace ina kwana mamiii shiru tayi mata sai ta kama kunnen ta tace "sorry mamii'am wallahi I overslept bansan time ya wuce haka ba but kiyi hakuri bazan sake ba"
Kallonta mamii tayi tace "naji ai sai ki wuce kici abinci mu tafi " to tace sanna ta nufi dining table ta zauna tana hada tea bude food warmers in tayi taga fries ne da plantain sai peppered chicken kadan ta zuba tana ci a hankali har ta gama. Parlour ta koma wurin mami tace nagama mamii sai tace mata to muyi sallah sannan ko? Tace eh tare suka hau sama kowa ya nufa daki domin gabatar da sallah zuhr,bayan inaaya ta gama sallah ta gyara dankwalinta ta fiddo black medium sized veil inta ta sa shi a right shoulder inta ta zo ta dauki wayanta da wallet tasa cikin jakan ta zira takalmanta ta fito parlour ta zauna jiran mamii batayi ten minutes ba sai ga mamii ta fito suka fita tare wurin mota inda driver ke jiransu gaida drivern inaaya tayi ta shiga gaba mamii na back seat suka tafii.Tafiya ce mai nisa daga gwarimpa gidansu inaaya zuwa sunnyvale estate inda gidan baffa yake haka suketa tafiya shiru babu mai magana sai karatun Quranin dake tashi a motan har suka isa.

Da sallama suka shiga gidan baffah babu kowa a parlour sai kamshin turaren wuta dake tashi da Ac sallama suka kara yi sai ga mai aikinsu janette ta fito daga kitchen gaishe su tayi ta nufa sama ta gaya ma ummi parlourn gidan su inaaya da mamii suka zauna saiga ummi ta sauko tana murmushinta mai kyau ahhh yau su mamiin aneesah ne muke gani mun dade bamu ganku ba dariya mamii tayi tace ai kuwa dai gidan naku ne da niisa "wlh bari haj aisha akwai nisa" cewar ummi kenan pouting lips inaaya tayi tace "bara naje inda zaa yi noticing ina" dariya ummi tayi tace habaa inani ina manta diyata ai fushi nike dake shiyasa ko kizo mana hutu sai tace toh ummi ai zanzo su aneesah basa nan shiyasa tafada kaman zatayi kuka "to shagwaba ce ta taso inee smiling tayi tace to ai kece ummi sai kuma tayi dariya tace "uhmm kar fa nayi rashin hankali ummi ina wuni ban gaida ki ba ya gida" dariya sukayi gaba daya su ummi da mamii tace lafiya lau daughter ya hutu tace Alhamdulillah ta tashi tsaye tana ummi ina mimi "mimi na daki bacci take daughter" sama tayi da gudu bata jira ummi ta ida magana ba ta bude dakin mimi da khadija ta shige fadawa tayi kan gadon mimi ta na mata ihu a kunne mimzzzzzzz get up am here tashi wadda aka kira da mimi tayi tana hararan inaaya tace come on ineee why are you a kill joy ina dream me dadi kinzo kin tada ni dariya inaya tayi tace "uhh hakanan ake cewa inasan bacci mimz you're x20 of me wurin son bacci" smiling tayi tace "na u sabi"ta tashi daga kwance ta zauna kan gadon yarinya ce kamar inaaya a tsayi dan ita ba fara bace black beauty ce da dogon hancinta da lips inta yan kanana da manyan idanunta mashaAllah da shape inta mai kyau wani irin gashi gareta mai tsayi sosai tayi parking inshi in a messy bun,tashi tayi tsaye ta nufa hanyan toilet nasu dake cikin dakin ta gama abunda zatayi tafito ta zauna kan sofa dake dakin tana cewa ineeeee oya kin tada ni what's up meye labari ahhh intee is coming next week fa zaro ido mimi tayi tace please da gaske kike? tace of course dear! Ihu ta sa ta tashi tana tsalle biye mata inaaya tayi sai da suka gaji suka zauna suna sakin ajiyar zuciya sai mimi tace "dama abba ya barta a nan ta ida holidays wlh da abuja will be too small for us sai mun hada da kaduna and kano infact har yobe sai munje"
Hmmm! Wlh can't even start thinking of crazy things in da zamuyi OMG! So much fun Allah ya sa abba ya yarda dai Amiin sukace a tare sai inaaya tace "ke na manta ma sultana na gaishe ki kuma ansa bikin yaya sarah" ohh my dear sultana mun dade bamuyi magana ba kinsan tunda wayana ya lalace komai seems not so good kuma gashi baffah yace am a destroyer sai nayi learning lesson zaya bani wani
"Owww sorry sweetheart its not  good gaskiya to kije ki sama ya abby ki ta mishi pity face har ya siya maki"
"Hehhhhehe this girl you're such a darling haka zanje nayi ma cux everything is boring without my phone"
"Ke if we continue talking we'll talk for the whole day ina ya khadija da ya leesha?
"Uhmm wa in nan ki barsu kawai am so angry at them wai suna kara encouraging baffah a bar ni nakoya lesson first instead of them to be helping me shiyasa na sharesu fa" dariya inaaya tasa tace ina bayansu ta fita da gudu daga dakin don tasan sauran idan ta tsaya.
Dakin dake kusa dana su mimi ta shiga aleesha ce kwance kan gado tana kallo da mackbook inta sai khadija tana kan sofa tanata chatting tana smiling  sallama tayi a tare suka dago suka kalleta inaayatu kune kukazo yakenan ya kike ya mamii cewar aleesha .
"Mamii tana lafiya tana kasa tareda ummi"
"Su inee university babes inji khadija tana dariya don tasan inaaya batasan a ce mata uni babe
"Kaii ya khady bawata university babe fa ni da secondary school nake ma"
Dariya khadija tayi tace tou ya hutu is it nice
"Wallahi babu dadii ya. Khadijo har na gaji fa" stucking toungue inta tayi ma inaaya tace serves you right tana dariya haka sukayita fira da khadija da aleesha suna dariya suka ji an bude dakin mimi ce ta shigo habaa inee inata jiranki kinzo kin zauna a nan lets go.
Tabe baki su khadija da aleesha sukayi a tare suka sa dariya sai mimi ta kara hade rai ta ja inaaya suka bar dakin suka koma dayan dakin sunata fira na school da rayuwa har aka kira sultana da inteesar suka hada conference call suka yi ta fira har saida janette ta shigo tace ummi na kiransu sannan suka kashe suka nufa kasa, mamii ne da ummi zaune sai ummi tace masu"kun shige ku kun hadu da juna to kuzo muci lunch ko shima kun yafe"
Smiling sukayi su biyu mimi taje tana rungume mamii tana gaisheta suka gaisa suka hau dining table don cin abinci jollof rice ce da shredded beef sai coleslaw da zobo mai sanyi dama kuwa inaaya nasan zobon ummi its the best in town sun fara cin abinci sai ga aleesha da khady sun zo sun zauna suma suka gaishe da mamii suka gaisa sanna suka fara cin abincin shiru kakeji sai karan spoons har suka gama kowa ya koma abunda yake. Haka har dare yayi bayan magrib su inaaya zasu tafi basu ga baffah ba don ya tafi kaduna wani aiki mimi ta sauko stairs da gudu da dan karamin trolley inta tana cewa ummi danAllah ummi ni su inaaya zani bi nagaji da zama shiruu dariya ummi tayi tace to shikenan ai yanzu dakun shirya da su khadijan na ganki kin dawo smiling kawai mimi tayi tana ma su khady da aleesha stucking tongue haka tabi su inaaya suka tafi.
Bayan sun koma gida sun gama sallahn isha da cin abinci har daddy ya dawo lokacin sun gaisa da mimi yake cema inaaya ta shirya idan zataje kano in ranar monday za aje daukan aneesah har da tsallenta da jin dadi nan take mimi itama tace zataje sunata jin dadi haka suka tafi daki amma basuyi bacci ba har wurin 2am sun maida room in mini cinema da popcorn insu da ice cream sunata kallon "money heist" a macbook in inaaya sai past 2 sukayi bacci da kyar suka tashi asuba saboda bacci suna gama sallah suka koma har sai to one suka tashi dama inaaya ta gayama mimi yau zasuje gidansu sultana, haka kowanne su yashiga yayi wanka suka shirya cikin black abaya almost the same sunyi kyau MashaaAllah! Haka suka sauka parlour babu kowa sai kamshin dake tashi kitchen inaaya ta nufa taga mamii tsaye suna abincin lunch ta gaisheta da fara'a amsawa mamii tayi tace ina mimi
"Mimi na parlour mamii"
"Tou kuje kuci breakfast ko"
Eh tace kafin ta bar kitchen in takoma parlour wurin mimi tace suyi breakfast  to mimi tace kafin ta tashi ta nufa kitchen ta gaida mamii sannan ta koma wurin dining table inda taga inaaya zaune har ta fara cin breakfast inta pancakes ne da syrup "yeey pancakes" cewa mimi zama sukayi suka gama ci sannan suka koma daki don gabatar da sallah. Bayan sun gama sallah suka sauka parlour domin gayama mamii zasuje gidansu sultana mamii bata parlour saida suka shiga dakinta suka gaya mata "to banda yawo kuma kar kuyi dare kuje baba hassan zai kaiku"
A tare sukace to mamii suka fita da sauri suka gama shiri suka tafi.

Saurayi ne dan kimanin shekaru 29 dogo ne sosai ba fari bane kuma ba baki ba irin wa inda ake cewa chocolate color hanci gareshi dogo da cute lips in shi ga eye brows inshi very thick and arched, yanada full and thick beard da gashin kanshi black sosai kaman na larabawa yanada idanu farare tas ga kwarjini a tare da su.tafiya yake da sauri har ya isa bakin mota ya bude ya shiga ya tada ya wuce. Wani gate ya tsaya dan madaidaici yayi horn mai gadi ya bude da sauri shiga yayi da motan yayi parking ya fito suka gaisa da mai gadin ya wuce cikin gida bai tsaya ko ina ba sai wani daki babba ne dakin da king sized bed a ciki white color sai study table da dressing mirror a gefe sai kofan closet da bathroom a cikin closet in towel ya daura ya fada toilet ya sakan ma kanshi shower ya kusan 30 minutes a cikin kafin ya dauro alwala ya fito wani dark blue moroccan jallabiya ya saka ya feshe jikinshi da turare sannan yasa abun sallah ya gabatar da sallahn isha ya gama yayi folding mat in ya koma kan gado ya kwanta yana lumshe ido.bayan kamar 20 minutes kaman wanda ta tuna wani abu ya jawo wayanshi kirar iphone 11 pro max midnight green color dialing number yayi ya sa a kunnen shi ringing biyar aka dauka "hello son" akace daga dayan bangaren "ammi" yace in his cool voice that ladies can die for😉 "ammi barka da dare" "yawwa alii ya aiki" lafiya ammi but it's stressing "sai hakurii son it'll be worth it InshaaAllah" eh ammi InshaaAllah ya abba? "yana nan lafiya we're going to Nigeria ma on Friday InshaaAllah" kaii ammi ai da kun gaya mani it's been long da naje nigeria fa almost 17 years fa "yes son yakamata kaje very soon gaskiya" to ammi InshaaAllah I'll try and take a leave from work naje hutu ko one month nayi "ok Allah ya taimaka ya tsareka son" Amin ammi Allah ya kara girma my regards to everyone goodnight "ok son night bye"
Kashe wayan yayi yayi murmushi sannan ya gyara kwanciya yayi addu'a sai bacci yayi gaba dashi.










Hello loves❤️ its been a while hope you're all good! So chapter 3 is here please tell me what you think about it.

Please please please please don't forget to
VOTE
FOLLOW
COMMENT
SHARE

I LOVE YOU ALL❤️🔐

INAAYA💖Where stories live. Discover now