INAAYA 33💖

279 27 7
                                    

INAAYA💖










A can daki inaaya ko magana bata yi duk a hankali take ta abubuwa ta dauro alwala tazo tayi sallah ita kadai tasan yanda zuciyanta ke mata ji takeyi kaman ta rufe kanta tayi bacci kar ta kara haduwa da Aliyu inteesar da ta kula da yanda takeyi ta dan bata space bata ce mata komai ba suna zaune shiru sai ga aneesah ta shigo dakin tace mamii tace su sauko ayi dinner haka inaaya ta tashi jiki ba kwari suka sauka kasa a tare duk suka tarar kowa zaune a table din aneesah ta karasa ta zauna kujera gefen Ahmad, da kyar inaaya take takawa a hankali inteesar tayi gaba ta barta ta ja kujera gefen mamii ta zauna inaaya na karasowa mamii tace ita zatayi serving kowa abun bai mata dadi ba amma babu yanda ta iya ta fara da su Abbah da daddy tayi serving dinsu creamy shrimp pasta sai chicken soup as a starter tazo tayi serving ammah da mamii sai inteesar dake kusa da mamii tace "I'll serve my self nayi saving dinki wahalan" murmushi kawai ta dan kakalo tayi mata aneesah da ahmad ma duk sunyi serving kansu sai inaaya tayi serving twins da ya sa'id wanda yake zaune close to empty seat daga empty seat din sai Aliyu inaaya dai kaman ta zuba ihu saboda dole a seat din zata zauna dan shi kadai ya rage haka ta daure ta taka zuwa wurin Aliyu ta fara zuba mishi a kan plate kanta a kasa tana cikin zubawa taji muryanshi a hankali yace "it's ok" sai ta tsaya har zata zauna kaman wacce ta tuna wani abu sai ta nufa fridge ta bude ta jug ta ciro na zobo ta taho dashi a hankali tazo ta dauka cup din dake gaban aliyu ta juya shi ta aje ta zuba masa a cup din sannan ta zauna tana zama ya sa'id yace "uhmm mu ba a bamu zobon ko kuwa ba namu bane" saida yaba kowa dariya a wurin ita dai inaaya shiru tayi ta dauka jug din ta mika mashi duk ya sakata jin kunya abinci da diba dan kadan tasa kan plate dinta mamii ta kalleta tace "ke inaaya mi ke damunki tun breakfast bakici komai ba zaki saka dan abincin nan kan plate kin kara ko sai raina ya bace" ta gefen ido aliyu ya kalla plate din nata yaga dan abincin da saka haushi abun ya bashi kawai ya ja serving spoon ya diba abincin dayawa ya kara kan plate din ta sam hankalin shi baya kan kallon da kowa keyi masu ya saka sannan ya ajiye ya dauka fork ya fara cin abincinsa.Bayan sun gama dinner anyi clearing table Abbah da daddy suka nufa parlourn daddy na sama domin tattaunawa twins da sun sa ahmad gaba dole yayi game dasu haka suka nufa part din ya sa'id yin game din harda aneesah sai ya sa'id da ya aliyu suna zaune nan parlour suna kallo suna fira inaaya kuma da inteesar daki suka nufa, mamii ce ta leka ta ga sa'id da aliyu kawai a parlour sai ta nufa dakin inaaya tana shiga ta gansu kwance suna kallo mamii ta hade rai tace "ke inaaya so nawa zan miki fada sai kawai ki tafi daki ki bar mutum kina abu kaman bakida wayau" shiiru tayi batace komai ba har mamii ta gama a hankali tace "kiyi hakuri mamii" bata ce komai ba ta fita a dakin dan kwalla ya sako a idon inaaya tasa hannu ta goge inteesar tayi dan patting bayan ta tana lallashin ta tace su je tare, a tare suka sauka kasa sukaje parlourn suka tarar da ya sa'id da ya aliyu zaune sai suma suka sama wurin suka zauna shiru ba wanda yayi magana sai ya sa'id yace "haj. Intee big girls shikenan dama da kin tafi Switzerland sai ki manta da mutane sai kinzo kasan namu ko" dariya inteesar tayi tace "habaa ya sa'id bahaka bane ba fa kasan school sai a hankula fa" sa'id yace "uhmm yen university kenan to ya school" a haka sukayita fira tsakanin sa'id da inteesar ita kuwa inaaya tana zaune shiru batace komai ba tana zaune a one seater dake gefen inda aliyu yake zaune shima shiru yake rike da wayanshi bayan few minutes sai ya dan ajiye wayan shiru shiru sai can muryan shi a hankali ko fita sosai batayi a hankali kaman yana rada yace "uhmm so, ya school" bata yi zaton zaya yi mata magana ba shiyasa maganan tazo mata a ba zata itama a hankali ta amsa masa "lafiya Alhamdulillah ya aiki?" Shima ya amsa da "lafiya qlau" sai shiru ya biyo baya sai kuma yace "i see so haven't used the card i gave you and i am sure kina zuwa school why" shiru shiru ta rasa me zatace ma muryanta na kyarma tace "ermm uhmm daa...ma da..ma ai nayi using na account di...na ne" aliyu yace "eh ai nasan da na account din naki na baki card dina" shiru tayi ta kara kasa da kanta shi kam aliyu tabe baki yayi yace "anyway you can tell me if you need anything for the hidima and i hope you know there's going to be a dinner" tanajin zancen dinner batasan sanda ta dago ta kalleshi ba kallon rashin fahimta irin dinner kuma yaushe tana stammering tace "ahh ahh a'a ban sani ba" aliyu shikuma bai damu ba yace "well then i am telling you now kin sani" batada objection babu yanda ta iya haka tayi shiru tana ta tunani iri iri a ranta. Sai 10:30 su abbah suka bar gidan bayan sun sha firan su.







INAAYA💖Where stories live. Discover now