INAAYA💖
Inaaya ce kwance a daki ita kadai tayi shiru tana ta tunani abunta karan wayanta ne ya dawo da ita daga tunanin nata sultaana taga tana kiranta ba tsayawa ta dauka tace "hello babe" daga dayan bangaren sultaana tace "amaryaaaa how far" bata rai inaaya tayi tace "miye haka sultaana" dan dariya sultaana tayi tace "sorry sorry, so dama i wanted to tell you to get ready there's going to be a funfair at millennium park today and I think it'll be fun mu je" murmushi inaaya tayi don dama ta gaji da zaman gida sai tace "ohhk sounds good but kin gaya wa mimi and intee" sai sultaana tace "no na gaya ma mimi thought inteesar na gidanku" sai inaaya tace "no yau tunda safe taje gida kayanta sun kare zata dauko shaa ku biyo ku daukeni sai ki gaya mata" amsa mata sultaana tayi da "to get ready will be there in an hour with mimz and intee" sannan suka kashe wayan ta tashi ta nufa toilet ta yi wanka ta fito ta shirya cikin wani straight skirt blue da riga sleeveless black sai tasa ka abaya black plain ne sai wurin hannun kawai ke da wasu stones masu shining tasaka black turban da veil din jallabiyan sai ta fiddo jikanta black na dolce and gabana sai takalma hermes black color, zaune take a daki bayan ta gama shirin nata tana jiran zuwan su don ta dauka kusan one hour tana shirin. Sai after 2hours har inaaya ta gaji tayi sallahn laasar sannan sai ga su sunzo duk kaman hadin baki sun saka abaya kowannen su mimi tace "ohh ni amina kinga yanda kike shining inaaya kin kara wani haske" dukan wasa ta kai wa mimi tace "bansan wulakanci fa" haka saida suka gama yan surutansu sannan suka fito daga dakin da niyyan tafiya.
Mamii na zaune a parlour ita da aneesah tana ta bata labarin zuwan nasu gombe kai amarya sai ga su inaaya sun sauko kasa su duka hudun mamii a ranta take cewa ko ina zasuje parlour din suka zauna dayake duk sun gaisa da mamii da suka zo sai inaaya tace "mamii please zamuje wurin fun fair a millennium park" sai mamii tace "so?" Dan shiru inaaya tayi sai tace "tambayanki wai nayi mamii ki ban permission" wani murmushin takaici mamii tayi tace zauna nan tana mata nuni da kujeran dake opposite dinta sai tace "inaaya ke dai ba karamar yarinya bace kuma a zamanin nan da yara suka san komai ko aneesah nan da kike gani" sai mamii tayi pause tace "aneesah bamu wuri" sum sum aneesah ta tashi ta bar parlourn ta haura sama sai mamii tace gaba "ko aneesah bazata dinga yin wannan sakarci da rashin wayau da kike yi ba, amatsayin ki na musulma mai zuwa makarantar islamiyya duk ba littatafan da bakuyi mostly kinsani kuma malamai na fada kina ji" ita dai inaaya tayi kasa da kanta shiru don har ga Allah batasan me tayi ba mamii ta ci gaba "abun naki ma baxan saka shi a yarinta ba saboda ke dai ba wata yarinya bace a wasu kauyuka yara yan shekara 12 ake yi wa aure kuma su zauna ko yaran kauyen sun fi ku na birni ne ko miye ohon muku" sai ta juya ta kalla su mimi tace "yanzu ku kunga ya dace hakan" kallon mamii sukeyi in confusion sai kawai mamii taci gaba "yanzu ku dukkanku bara na maku wata tambaya, ke mimi da zaki baro gida hakanan kika fita kika tafi ko kin tambaya izini" mimi tace "mamii wallahi sai da na tambaya ummi da baffah duk suna tare na gaya musu kuma sun bar ni" mamii tace "very good ke fa sultaana" sultaana tace "mamii na tambayi ummah har tace ko driver zaya kaimu nace aa ni zanyi driving na daukesu mu wuce" nan ma mamii tace "very good ke fa inteesar" intee tace "mamii ammah fa tasani ki kirata ki ji kuma" mamii tace "aa kawai ba ce wa nayi zan kirata ba tambaya ne, ke fa inaaya" jiki a sanyaye tace "mamii shine nazo ina tambayan ki" cikin haushi mamii tace "kin rufemun baki nan ko sai na buge shi, ai ina ce nima dai ina da mahaifiyar nan tana borno idan zani fita ita kike ganin ina kira na tambaya permission" inaaya gabanta ya wani buga dum! Sai lokacin ta fahimci inda zancen mamii ya dosa mamii cikin fada tace "ba da ke nake ba hajiya kikaga ina kira na tambaya idan zani fita" hawaye ya cika idon inaaya ta gyade kai alamun aa da karfi mamii tace "da baki zaki bani amsa" har hawayen sun fara zubowa inaaya tace "Aa daddy kike tambaya" sai mamii tace "to kinsani kenan kuma ke ba mahaukaciya bace kinsan cewa kin fita daga hannunmu yanzu kawai dan dai baki tare a gidan mijinki ba doesn't mean mu zamu baki damar fita dukkansu nan sunje sun tambaya izini daga wanda suke kasansu sai ke, yes bance bazaki tambaya nawa ba tunda a cikin gidan ki kike but sai ki fara tambayan na mijin naki sannan ki tambaya nawa ko kin taba jin ance mace ta fita ba tare da izinin mijinta ba" mamii ta dinga ma inaaya fada ita kuwa inaaya hawaye ke ta zirarowa daga idanunta zuciyanta na mata wani nauyi wai yau itace mamii ke ma fada haka abunda bata cika yi ba sai idan ran ta ya bacii ba kadan ba which is rare, wai yau itace sai ta tambaya izinin wani a matsayin miji kafin ta fita data tuna haka sai hawayen su karu, daga karshe mamii tace "tashi ki bani guri ki wuce kije ki nema izinin mijinki idan ya barki idan kuma bai bar ki ba ko baki nema ba babu inda zakije" da kuka ta tashi ta nufa sama su mimi nan suka shiga ba mamii hakuri kafin suma suka nufa sama. Inaaya na kwance a bisa gado kuka take kaman ranta zaya fita tana shessheka duk sai jikinsu yayi sanyi suka zauna a kan gadon mimi ta dafata tace "sorry sis please don't make us cry" sultaana tace "yess inee please stop it I'll start crying now too" inteesar tace "inee please clean those tears sorry get up and wash your face and we will sort things out" hakanan inaaya ta daure ta tsaida kukan nata ta dago tana kallonsu da jajjayen idanu tace "sorry don't be sad I'm ok you guys should carry on it's getting late go and enjoy yourselves, i have to face my reality and fate the sooner I accept the fact that I'm not the same with you guys now the better it'll be for me didn't you hear what mamii said i can never step out without my husband's permission so just go and enjoy yourselves" tagama tana kakalo murmushin da iyakanshi kan lebe ita kanta saida taji abun wani iri a bakinta wai husband, kallonta sukayi da ban tausayi inteesar tace "inee being married doesn't mean you won't enjoy or be happy mamii is just insisting on the permission thingy that's all and I'm very sure ya aliyu will not refuse please just call and ask him here is his number" tana fada tana nemo numbern shi a wayanta ita kuwa inaaya wani Murmushi mai ciwo tayi tace "no intee forget it you guys should go kawai" sultaana tace "how can we go without you" mimi tace "exactly atleast try just call him" inaaya tace "please no! For my sake you guys should just go ahead" kawai inteesar tayi dialing numbern ya aliyu.
Kwance Aliyu yake kan kujeran dakin shi ya dan rufe idanu yana ta tunani kala kala na past da na wanda ke faruwa da yanda future zata kasance gashi jiya abbah ya kirashi yace he should start preparations zaayi hidiman bikin nashi nan da 3months amarya zata tare after that zasu tafi switzerland idan ta koma makaranta sai ta dawo nigeria kuma zaayi mata jera a nan nigeria a gidan aliyun dake nan wuye acacia estate so idan da abubuwan da zayayi wa gidan duk ya shirya kuma yayi lefe da komai da komai duk ya lissafo mishi sannan dora ya mishi nasiha akan kar ya wulakanta auren da suka yi mishi kar ya wulakanta masu diya dan yaga hakanan suka bashi aurenta, yana cikin tunanin nan wayanshi yayi ringing yayi tsaki ya duba yaga inteesar ke kira har ta kusa katsewa kaman bazaya dauka ba sai kuma ya dauka yace "hello" a dayan bangaren inteesar har ta fitar da ran zaya dauka sai taji ya dauka inaaya dai shiru take tana sauraro dayake a speaker inteesar tasaka, inteesar tace "hello ya aliyu ina wuni" yace "lafiya qlau, ya dai" inteesar tace "uhmm ya aliyu dama zamuje fun fair ne" sai yace "so? How is it related to me?" A hankali tace "can we go with inaaya" haushi ma maganan ta bashi hakanan yara su raina shi a kufule yace "how is that my problem is not like am holding her legs" inteesar tace "no! Dama mamii tace bazata je ba till she asks for your permission" yace mata "ohhh i see what did mamii said?" Inteesar tace "she should ask for your permission" sai yace "very good! And I'm sure you're inteesar not her right" a hankali inteesar tace "yes" yace "great and mamii did not say inteesar should ask for permission for her she said she should ask permission her self" a hankali inteesar tace "yes but ya aliyu pleas.." bata karasa ba yace " so let her do it not you" kashe wayan yayi bai jira me zata ce ba ita kuwa inaaya kuka ne yaci karfinta cikin kukan tana stammering tace "plea....se yo..u shoul...d go" kallon juna sukayi suka kalleta da tausayin kawar tasu sosai mimi tace "please inaaya just call him and ask yourself please please" ta tsaida kukan nata tace "no please I don't want to go anymore please you guys should just go I just need some time alone now" haka sukayi ta insisting basusan time ya wuce ba har magrib yayi saida suka fasa zuwa dukkansu sai da sukayi sallahn magrib bayan sun sha lallashi sannan duk suka nufa gidajensu. Aliyu kuwa haushi maganar inteesar ta bashi wato ita ta raina shi da bazata kirashi ba saidai tasa inteesar ta kirashi wannan ai raini ma ne su abbah suka jawo mishi shiyasa ya ce ma inteesar ai ba ita akace ta tambaya ba ya kashe wayan yana jin haushi yayi wurgi da wayan kan gado.
Taqabbalallahu minna qa minkum❤️
ALHAMDULILLAH! Eid ul adha mubarak beautiful people! May Allah(SWT) spare our lives to witness another eid...Ameen
This is a barka da sallah from me to you guys
hope you're all good? What do you think about this chappy💕Please please and please don't forget to
VOTE
COMMENT
FOLLOW AND
SHARELOTS OF LOVE❤️🔐