INAAYA💖
Sai past 10 sannan duk suka fara baro garden din suna shiga cikin gida iyayensu suka tarar zaune a parlour sukayi joining nasu, what a beautiful family! Sai 11 saura kowa ya tashi don tafiya gida dukkan yan matan aka ce su tafi gidan baffah saboda su taya ummi aiki gobe saboda a can gidan zaayi meeting din duk suka shiga motoci banda inaaya da khady da aleena da basu sama space ba nan ko fareed yace suzo bakomi zasu ajiyesu a gidan wani irin harara aliyu ya maka mashi shi kuwa ko a jikinshi haka suka nufa wurin motan tashi suka shiga su uku inaaya ce tsakiya sai side inta khady sai aleena a dayan side din shiru kakejin motan sai can fareed yace "lee baki gaya mun sunan wannan sistern naki ba" yana nuni da inaaya dariya aleena tayi ta ce "wlh mantawa nayi kasan kannen namu dayawa ne wlh, itama dai namesake ina ce fatima amma kaji wani sunan yan gayun da ake kiranta ahh sunan nan one in town" tafadi tana dariya shima fareed dariya yayi sannan yace "wow wane sunane wannan" murmushi aleena tayi tace "inaaya, ni wlh ban taba jin sunan ba ma sai a kanta" kada kai fareed yayi shima yace "gaskiya lee nima ban taba ji ba" inaaya dai batace komai ba shiru kake jinta khady kuwa ta hade rai ita a dole haushi takeji aliyu ma shiru be tanka masu ba sai ji yayi aleena tace "wai ya aliyu ni wlh kullum shirun nan naka kara yawa yake to wai ma idan kayi shiru bakajin bakinka na kai-kai" Murmushi ya kakaro sannan yace "wannan sai ke kai-kai in miye bakina zayayi mutun yayi ta surutu kaman computer" dariya tayi wholeheartedly fareed ma dariya yayi ita kuwa inaaya mamaki ne ya kamata ashe dama yana magana this is the longest abun dataji ya fada tunda ta sanshi, aleena bata yi shiru ba sai ta sake cewa "habaa ai ba surutu nace kayita yi ba kawai dai a danyi labari tunda an dade baa hadu ba saidai gaisawa ta waya" fareed ne yace "ahh toh lee ki gaya mishi dai" hararansu aliyu ya danyi sannan yace "kun sa mani ido sosai wallahi" dariya aleena tasake yi sannan tace "to ya aliyu ya zaayi gaskiya ne yanzu da wannan irin shirun naka wacece zata yarda ta aureka, tab wallahi da tana da aiki babba ba karami ba" murmushi kawai aliyu yayi mata don ta tabo inda bayaso, kaman jira fareed yake yace "ai lee ni inajin yayan nan naki saidai kawai su baffah su yi mishi auren gida idan sun gaji da zamanshi haka saboda shi dai baya cikin agenda inshi" tsaki aliyu yayi yaji haushi miyasa zaya fada haka yaran can su raina shi dama dai aleena ce kawai ita mutuniyar shi ce har a waya suke gaisawa duk da baya zuwa nigeria "miye haka fareed kalla gabanka kayi tukin daya dameka ka cika mu da surutu" aliyu ya fada shi kuwa fareed tsab ya gane abunda yake nufi amma bai ce mishi komi ba. Shiru shiru motan sai aleena kaman daga sama fareed yaji tace "fareed please can i ask you a question" gyade mata kai yayi sai tace "how old are you" murmushi yayi yace "wannan babban tambaya ce lee but shaa I'm 29 will be 30 by December" smiling tayi tace "that's good" hade da kallon khady tana dariya ita kuwa ta daure fuska, haka sukayi shiru har suka isa gidan baffah aleena kawai tayi masu godiya sannan suka nufa cikin gidan.
Da safe sai wajen karfe 10 suka tashi ummi tasa duk su sauko kasa a hada breakfast dayake sunada yawa cikin lokaci kadan suka gama hada komai sannan suka zauna a dining gaba daya kowa yayi breakfast. Ummi ta ce dasu kowa ya je yayi wanka wurin 1 zasu fara shirya abincin rana haka suka nufa sama zuwa dakin khady da mimi, duk suna zaune sai ga aleena da aleesha sun shigo suka zauna kan couch din dake dakin sai aleena ta kalla aleesha tace "leesha kinga knock some senses into khady abunda takeyi bata kyautawa kinga dan handsome din nan abokin ya aliyu sai wulakanta bawan Allah takeyi, yanzu ma abunda yasa na jawoki dakin nan saboda ki mata magana yanzu ya kirani yana rokona DanAllah ince mata ta dauka wayanshi tun jiya take misbehaving dayace ta bashi numbern yarinyar nan tayi banza dashi har 10minutes sai da naje sannan ni na bashi yanzu kuma yanata kiranta bata dauka, wai kinji wani banzan excuse wai ita ya kusa diya da ita bata iya auren wanda ya bata 10years sai dai 5years below kiji hauka DanAllah matured mutum dai gashi da hankali so jovial amma taki ta saurareshi ni wallahi kila ummi ma zan gaya ma wa" duk shiru sukayi suna sauraron aleena har ta gama sannan aleesha tace "habaa khady miye kikeyi haka kinsan dai ke ba yarinya bace ko miye wani 10years mi kake nema dai me hankali wanda zaya rike ka da mutunci wallahi duk ki ajiye nonsense din nan kiyi facing reality ba wai movie bane na turawa da kike ganin sunayi kiji kema haka zakiyi" turo baki khady tayi tace "ni wlh you guys are not understanding me at all ina gaya maku ne I can't I can't ni wallahi kunya ma abun zaya rika bani ya fa girma ya abby no gaskiya tsakani da Allah banso" hanifa ta harareta sannan yace "ni wlh kin bani kunya ma sis wai ke kike fadan haka wai kunya sannu hajiyan kunya" farhana dake fitowa daga cikin closet tace "i heard everything,habaa khady at least give him a chance talk with him age is just a number it doesn't matter kikasan ko shine mijin" inteesar tayi dariya tace "sis inlaw is right plss pick his call ya khady Allah you won't regret it he's nice beyond explanation gidanmu ya zauna a switzerland i can count on him just give him a chance talk to him you'll see what am telling you" watso mata harara farhana tayi tana cewa "wlh ki kiyayeni" dariya sukayi ma farhana su duka mimi kam cewa tayi "uhmm ku rabu da ya khady yaro takeso ta aura tayita mishi wayau" dariya sukayi su duka khady ta jawo pillow ta buga ma mimi da gudu ta tashi tana dariya sai aleena tace "see your life har su mimi sun fi ki sanin ya kamata kina nan zaune idan kikayi wasa kiji ana gama bikin aleesha an saka na mimi" rufe fuska mimi tayi tana blushing aleesha ta taba hannu tace "innalillahi wlh aure takeso kinga yanda take blushing, ah lallai yarinyar nan" dariya aleena tayi tace "ya son ranki leesha" inaaya dake can gefe kaman bata dakin tace "ni wlh ya khady i can relate ko ni idan ni ce bana iyawa haba 29 years fa ta ina zaka iya kallonshi a matsayin miji idan kam dan 4years ya baka ku yita yarintan ku" kallonta dukkan su sukayi baki a bude banda khady da tayi murmushi tace "seriously shiyasa nake sanki inee we're so similar ki gaya musu dai Allah those yarinta da lovey doveys ta ina zaka fara kallonshi kayi ta mutun ya girme ka nesa ba kusa ba ai saidai kaita ce mishi uncle sama uncle kasa" taba hannu aleena ta shiga yi tana salati "namesake yaushe kikayi baki haka lallai kin girma an samu ana shawo kanta kinzo zaki kara mata da naki mentality din to wallahi kuci gaba kila ku biyun nan dukkan ku yen 29 dinnan da bakuso zaku aura" ke kuma ta nuna khady tana cewa "it's me and you in this house idan bakiyi picking call nashi ba kuma daga yau Addua zan dunga yi Allah yasa ya zama mijin naki muga yanda zakiyi, ke kuma inaaya da zaa bi shawarata ma a hadaki da ya aliyun kawai ayi na zumunci muga karshen wannan mentality din naku" turo baki kawai khady tayi ita kuma inaaya tana jin abunda ta fada heart dinta yayi wani beating da karfi ta zaro idanu tace "habaa ya leena Allah ya sawake mani" dariya sauran sukayi su duka sannan su aleena suka tashi suka bar dakin zuwa dakin aleesha suyi wanka. Karfe 1 na rana duk sun gama wankansu sunyi sallah sannan suka nufa kitchen suka fara aikin daya kamata sai 4 saura suka gama lokacin har su daddy da abba sunzo, daki suka nufa domin shiryawa.