INAAYA 22💖

287 29 11
                                    

INAAYA💖







               Duk kowa ya ka gara yaji abunda ke faruwa dukkansu gidan daddy suka wuce straight bayan reception suka tarar ana photo session suka shiga akayi da su sannan suka wuce parlour din daddy dake sama cux yafi shiru suna zuwa suka tarar da iyayen nasu maza duk suka samu wuri suka zauna sai baffah ya kallesu yace ahmad kaje ka ce wa fareeha duk yan matan suzo banda inaaya ahmad ya amsa da to yaje ya gayawa anty fareeha nan da nan ta hado kansu har da amaren banda inaaya da ta koma closet abunta ta zauna duk suma parlour din suka samu wuri suka zauna baffah yayi gyaran murya yace " toh godiya ta tabbata ga Allah(SWT) da ya nuna mana wannan ranan muka aurar da yaran mu Allah yayi maku albarka" amin suka amsa a hankali nan ya dora da yi ma amare nasiha sosai akan aure ya masu fada da gargadi sai kuma yace "nasan ku matan bakusan abunda ke faruwa ba mazan kawai suka sani dasukaje daurin auren, a yau ba ku uku kawai muka daurawa aure ba bayan shawarwarin da mukayi mu duka da iyayenku mata mukayi coming up da solution, lokacin da na ba su ummi lokaci baku kadai ba aliyu ma na bashi sannan sai bai fiddo ba kafin lokacin shine muka bashi mata muka yanke shawara hada shi da ita sannan kuma muka daura auren a yau amma ba zata tare ba sai nan da yan watanni" kallon mamaki sukeyi ma baffah sannan suka juya suna kallon ya aliyu da yayi kasa da kanshi mazan kuwa wani rudu suka shiga  saboda sunsan da wa aka daura, khady tace "toh baffah amma wacece amaryan" murmushi yayi yace "ba wata bace ba illa yar uwarku gaba daya inaaya" wani irin tashin hankali kusan duk mutuwan zaune sukayi a wurin inteesar da mimi har wani shaking hannayyensu keyi saboda tashin hankali ba su da ko bakin magana daddy kuma ganin haka yace "ku tashi kuje Allah yayi maku albarka, sannan ku kira ita inaayan da mamiin ku nan" dakyar suka iya barin parlour din kowa shi yasan tashin hankalin da ya shiga tuni inteesar da mimi sun fara hawaye haka suka isa dakin inaaya sultaana ce zaune kan bed suna shigowa duk ta kula yanda suke taga mimi da inteesar na hawaye tuni hankalin ta ya tashi ta fara magana tana stammering "miii....m...mii me ya faru wani ya rasu ko wani abu ya fara" kada mata kai kawai khady ta iyayi inteesar din ce ta shiga closet din da inaaya take duk hawaye ya jike mata fuska kawai ta fada ta rungumeta tana sakin wani kuka mai cin rai ita kuwa inaaya kasa gane mata tayi sai tace "intee what is it kike kuka wani abun ya faru ne" da kyar tayi gathering courage tace "su baffah na kiranki suna parlourn daddy na sama" dum! Taji zuciyanta ya buga sai tace "intee ki gaya mani me ya faru miyasa su baffah ke nema na ki gaya mani intee" inaaya ta fada hawayen dake idanunta suna saukowa dan daidaita kanta inteesar tayi tace babu komai tashi ki je, tashi tayi ta fito dakin tana goge hawayen taga duk fuskokinsu ba walwala hankalin ta ya kara tashi taga mimi tayi sauri ta juya mata baya hawaye na saukowa a idonta sai kallon tausayi sukeyi mata a haka jiki ba kwari ta dinga takawa a hankali har ta isa parlour din tana shiga taga su baffah zazzaune da mamii da Ammah kasan carpet ta samu ta zauna tana gaishesu kanta a kasa amma zuciyanta sai bugawa takeyi daddy ne ya fara magana "mamaana, kinsan ita rayuwa a kullum ba yadda ka tsara ta take tafiya ba sai yanda Allah ya tsara maka kuma no body can change it" gyade kai tayi daddy ya cigaba yace "duk musulmi ana son ya zama mai daukan qaddara mai kyau da mara kyau idan Allah ya tsara maka abu kasaka a ranka shine mafi Alkhairi a gareka ka yita gode mishi" nan ma kai ta gyade ita ta fara kagara taji me ke faruwa haka mamii ta dinga gaya mata jiya to mi yake faruwa daddy yaci gaba da cewa "ina so ki zama me tawakkali mamana da hakuri kuma kisan cewa mu iyayen ki ne masu sonki bazamu taba cutar dake ba" tace "eh daddy nasani" baffah ya ce "toh! Inaaya a yau munyi daurin aure amma ba yanda kuka sani ba na mutun uku na mutun hudu mukayi, sannan ke ce ta hudun A yau mun ga mun isa dake mu iyayenki ne muka yanke hukunci kuma mun daura aurenki da yayan ku ALIYU"ai inaaya ji tayi kaman tana mafarki kwata kwata taji kanta ya na wani juya kaman ba a parlourn take ba dum! Dum! Dum! Zuciyanta ke bugawa da karfi kafin kace me idanunta sun kada sunyi jajjawur kusa 5minutes sannan ta dago tayi murmushi tace "abbah abbahna da wasa suke ko" kallonta sukayi da tausayi ta juya tace "mamii kinji me baffah yace wasa yake shi da daddy wasa suke mani ko" mamii ta shiga kada mata kai alamun aa rudu ba karami inaaya take ciki ba hawaye ya fara zuba daga idanuwanta ta tashi tsaye wani juyawa taji kanta yayi kafin taga blackout ta fadi a firgice mamii tayo kanta tana kiran "inaaya inaaya" tana jijjigata ammah ta tashi da sauri ta bude fridge din dake parlourn ta jawo roban ruwa ta mika ma mamii, mamii ma duk ta rude da kyar ta iya bude roban tasa a hannunta tana yayyafa mata shiru bata tashi ba mamii ta dunga yayyafa mata har kayanta ya jike dan ta kusa juye ruwan roban, tana kara yayyafa ma ta amma shiru duk suka rude ammah na cewa "mu kai ta asibiti dan Allah kar wani abun ya sameta" mamii kuwa ko magana ta kasa saboda tashin hankali daddy yace "ahh umm..umm yan..yan..zu a kira Aliyu" duk ya rude yake maganan abbah ne ya samu natsuwan dauko wayan shi yana kiran aliyu yana dauka yace mishi yazo yanzu ba bata lokaci ya amsa da to mamii na rike da yar tata tana ta jijjigata tana kiran sunan nata Amma ko motsi batayi suna cikin tashin hankalin nan aliyu ne ya shigo da sallama a bakinsa ko amsa masu basu samu sunyi ba Ammah ce ta taso tana rike aliyun tana cewa "Aliy kaa..kka..ka duba ta bata motsi bamu san me ya sameta ba" shima aliyu wani shock ya dan sameshi yana takowa a hankali inda mamii ke rike da ita hannunta ya rike ya taba wurin pulse dinta yaji normal ya taba chest dinta yaji heartbeat dinta na tafiya duk da da sauri sauri daukanta yayi cak ya ajiye kan kujera yasa hannu ya danna chest din nata ya mata sprinkling ruwa a fuska amma shiru bata tashi ba yayi repeating haka kusan so biyar Abbah yace "kunga mu kai ta asibiti tunda bazaya iya ba kar wani abun ya sameta" mamii dai tsaye take gefe daya kaman an dasa ta ko motsi ta kasa ga hawaye idanunta, wannan karon hannu duka biyu aliyu yasa da danna chest din yayi sprinkling ruwan ai kuwa sai ta ga ta ja wani dogon numfashi ta na bude idanunta a hankali duk wani numfashi su baffah suka saki da basusan suna rike wa ba, tana gama bude idanunta suka sauka a kan Aliyu wata kara ta saki mamii tayi saurin zuwa tana riketa Aliyu ya matsa gefe abunda ya faru duk ya dawo mata sai ta fashe da kuka tana kankame mamii tana cewa "mamii danAllah wasa ne ko mamii kicema daddy ya bar irin wannan wasan" mamii da dan karfi tace "get a hold of your self inaaya wa yake miki wasa a nan wurin" kuka takeyi mai cin rai tana ta "mamii, ammah ku ba su daddy hakuri dan Allah su bar ni in zauna da mamii kar suyi mani haka" abbah yayi ma ammah alamu da hannu su tafi da ita mamii tayi gaba sai daddy yace ma ammah "danAllah ku bata baki sannan ta shirya mai hoto zayazo yayi masu hoto ita da aliyun saboda tarihi, kai ammah ta daga tace to sannan tabi bayan mamii suka bar su daddy sai abbah yake cewa "gaskiya sai nake ganin kaman bamu kyauta wa yarinyar nan ba munyi kuskure" daddy ne yace "aa babu wani kuskuren da mukayi in Allah ya yarda kawai shock ne da take ciki ba wani abu ba" baffah da baba suka amsa alamun eh haka ne.




INAAYA💖Where stories live. Discover now