INAAYA💖
Aliyu na shiga dakin nasa closet ya nufa ya rage kayan jikinsa ya yi wrapping towel a waist dinsa ya shiga bathroom yayo wanka sannan ya fito ya saka kaya ya kwanta a kan gado ya fara tunanin abunda yayi ya dace kokuwa kaman he's being harsh on the poor girl yana ta tunani kala kala. Inaaya wayanta ta dubo sannan ta kwanta a kan gado ta daga wayan ta kunna data ta kwana biyu ma bata kunna ba messages sukayi ta shigo mata masu yawa ta ma kasa dubasu saboda yawa kawai tasa alarm ta ajiye wayan ta kwanta amma sam ta kasa bacci tunanin kalaman Aliyu take wasu zafafan hawaye na saukowa a idonta a rai take tunanin yanzu her dream to to marry a lovely and romantic husband to have the best marriage is shattered she's stucked with someone who doesn't like her a bit in the name of marriage tunanin wannan yasa hawayen nata suka karu idanunta duk sun kumbura sunyi ja a zuciyanta tace "ya leena was wrong thinking it'll work by me trying nothing is going to work" ta sha kukanta can taga dai ba abunda kuka zaya mata ta lallashi kanta ta tashi ta dauro alwala ta kabbara sallah da takai sujjada ta jima tana kai wa Allah kukanta na ya kawo mata sauki a rayuwanta sai wurin 12 ta gama ta koma ta kwanta sai daya ta wuce ta samu bacci ya dauketa da tunani kala kala a ranta. Shima aliyu yana kwance yana ta tunane tunane daga baya ya fada toilet yayo alwala yazo da dinga salloli yana miqa bukatunsa da kukansa ga Allah ya gama ya zauna ya fara karatun qurani in his serene voice har sai 2 sannan ya kwanta bacci yayi gaba dashi.
Bayan sallah asuba inaaya wurin 6 ta koma bacci karfe tara ta farka tana tashi ta jawo wayanta ta duba lokacin sannan ta shiga closet ta cire kayan jikinta ta shiga bathroom ta jima tana wanka sannan ta fito a hankali take shafa mai kan fatar ta mai laushi ta gama ta bude akwatunan ta tana duba kayan da zata saka wani voile ne purple da red dinkin doguwan riga cinderella style ta daura dankwalinta babu wani kwalliya a fuskan ta fayau kwalli kawai ta shafa da lip balm ta fito daki ta zauna ta ja wayanta ta fara duba messages tana replying duk yawanci congratulatory message ne tagama ta fara duba status duk friends da yan uwa duk data duba hotunan su ne na biki tana ta kallon posts din mimi sai taci karo da video din couple dance dinsu na ranan dinner tasaka tayi caption "love lives here❤️💏" haushi ma inaaya taji ganin caption din sai tayi ma mimi message "habaa mana mimz you know this caption doesn't fit in here ki cire shi" tayi sending amma bai je ba mimi bata online kawai ta kashe data din ta ajiye wayan tarasa me zatayi duk taji babu dadi kadaici ya mata yawa kawai sai tayi deciding da ta sauka parlourn kasa haka ta sauka ta ta zagaya ta shiga kitchen din ta fito ta shiga dakunan kasa sai kuma tayi wurin dining table nan taga kwalin pizza sai wani leda dauke da shawarma da grilled chicken ta dan tabe baki tuno jiya datayi sai ta kwashi kayan ta je ta bude fridge ta saka su tana fitowa daga kitchen ta ji karan ana knocking kofa wurin kofan ta nufa bayan ta dauka key din ta bude kawai sai taga mimi da inteesar har wani ihu tayi ta rungume su biyun a tare inteesar tace "ke malama get off me ko bacci bamu gama ba kinsa Ammah ta tado mu" mimi tace "hmm i feel like crying sef" sakinsu tayi sai lokacin ta kula pyjamas ne jikinsu da hijab ko wace sai ta fashe da dariya tace "kun ganku kuwa" mimi tayi hissing tace "abeg take ko shigowa bamayi" basket ne babba dauke da kuloli a ciki mimi ta miko ma inaaya ita kuwa inaaya kallon alaman miye ta maata inteesar tace "what else da yunwa zaku zauna breakfast ne which ammah bazata iya ba driver ya kawo ba sai ta hado da mu muna dan baccin mu na safe" inaaya tace "ai ta kyauta ku shigo to" ta fada tana basu hanya mimi ta ce "mu yi meee? Rufa mana asiri mana wannan faran safiyan muna zuwa gidan amare" dariya inteesar tayi tace "ahh ahh to kuma dama ammah ce wa tayi driver ya jira mu ya dawo da mu just kallanmu a pajamas muke fa" shagwabe fuska inaaya tayi tace "habaa mana ai nan din ma gida ne da toilet kuna iya wanka and ba sai ku saka kayana ba ai ba wani abu ne ba kallon juna sukayi su biyun sai inteesar tace "come on inee don't be a baby wlh ammah tace muje mu dawo and zamuyi wanka and come back with lunch it's a promise wurin 2 zamu dawo InshaaAllah yanzu ma we left our phones at home" har inaaya ta dan fara hawayenta saita goge su tace "promise" mimi tace "yess it's a promise InshaaAllah" sai ta dan kakalo masu murmushi ta karba basket din sukayi mata sallama suka tafi ita kuma tayi cikin gida bayan ta rufe kofan taje ta cire kulolin daga basket ta ajiye a dining table ta bude babban taga fries ne a ciki sai dayan gizdo(gizzard and plantain) ne a ciki sai dayan kulan chicken sauce ne duk ta gama gani ta rufe ta dauka basket din ta kai kitchen ta fara bude drawers din kitchen din ta dauko plates biyu da serving spoon da forks ta kai a dining table ta ajiye sannan ta bude fridge ta dauko wani farm fresh yoghurt da ta gani da cup tana ajiye cup din ta ji ana knocking kofa ta fara tunanin waye yazo ta je ta bude mimi ta gani da flask a hannu ta mika mata tace "sorry har mun tafi ashe mun manta da flask din Ammah tace it's for ya aliyu every morning coffee yake fara sha before breakfast" inaaya ta karba ta gyade mata kai sai mimi tace "bye muna sauri" ta ce mata bye sannan ta rufe ta koma ciki shima flask din a dining table ta ajiye shi ta zauna gizdo din ta diba ba dayawa sosai ba a plate ta bude yoghurt din ta tsiyaya a cup ta fara ci a hankali. Karfe 11 daidai aliyu ya farka daga bacci ya karanto addua sannan ya tashi ya shiga toilet yayi wanka da brush sannan ya fito wani jallabiya ne fari ya saka bai ida kai mishi kasa sosai ba ya fesa turaren nasa sai yaji cikinsa na kuka ya fara jin yunwa ya bude kofa a hankali ya fito a zatonsa inaaya bata tashi ba dan kar ya tada ta tana bacci ya sauko kasa ya nufa wurin dining tsayawa yayi ganin mutun zaune yana mamakin ta tashi haka ya kara sa wurin dining ya ja wani kujera zaya zauna ita kuwa inaaya tana cikin cin abincin nata bata ji zuwan kowa ba sai turarensa da ya dake hancinta da sauri ta dago ta gansa ya ja kujera ya zauna da sauri tayi kasa da kai tana cewa "ina kwana" ba yabo ba fallasa ya amsa mata da "lafiya lau" tunawa tayi bata dauko cup din shan coffee din ba sai ta tashi a hankali ta fara tafiya taji muryansa yana cewa "get back and finish your food" murya kasa kasa tace "cup zani dauko" bai ce mata komai ba sum sum ta kara kitchen ta dauko mug ta dawo ta ajiye gefensa yana bude kulolin yace "where did you get all this" tace "Ammah ce ta aiko" kada kai kawai yayi ya ja flask yaga cup din da ta ajiye mashi ya dan kalleta briefly kanta a kasa tana cin abincin a hankali ya juya ya bude flask din yaga coffee cikin ranshi yaji dadi yana ta godewa Ammah ya tsiyaya a mug din ya dauka ya fara sha ya gama ya diba dankali da chicken sauce kadan ya fara ci inaaya kuwa duk taji abincin ya fita ranta da kyar ta cinye ta kwashe kayan ta kai kitchen ta wanke ta zo sum sum ta wuce ta hau sama ta shiga dakinta ta zauna ta jawo wayanta ta shiga Instagram ta fara kallon stories din mutane har tazo kan yan uwanta da friends duk pictures din bikin ne sukayi posting different pictures da videos ta gama kallo sai tazo kan wani status kawai taga video dinsu na couple dance anyi posting a arewafamilywedding sai ta shiga page din sai taga pictures dinsu na biki duk anyi posting tun daga day one har ran budan kai kan na dinner din ta shiga pictures ne da video na couple dance na cutting cake video din da me make up ta mata duk anyi posting over 2,000 comments ta gani sai ta shiga ta fara dubawa ta dinga ganin different comments wasu na masu Allah yasa Alkhairi wasu na wow wow and yan awwns association tana ta scrolling sai taga wani comment "my heart💔 Wlh I've been looking for this guy tun ba yau ba i so much love him" wadda tayi comments din ta samu replies dayawa wata tace "wayyo baiwar Allah sorry amma bai kamata ki dinga fadan haka ba mijin wata ne who knows ko tana ganin comment din is not nice" exchanging comments sukayi tayi yarinyan tace "idc shi din ai namiji ne mijin mace hudu kuma I won't stop looking for him zan gano shi and get married to him InshaaAllah" comments dai iri iri mutane na allah wadan wadda tace sai ta nemo shi haka dai wasu comments din yanmata ne keta faman wow the husband is hot inaaya dake karanta comments din tarasa miyasa amma zuciyanta zafi yake mata tana jin haushi "mtswww" tayi tsaki ta kashe datan ta wurga wayan a kan gadon ta kwanta tana ta tunani kala kala.