INAAYA💖
Karfe tara suka tashi washegari duk a gajiye dai suke sukayi breakfast sai mai gyaran jikin amaren tazo aka fara gyaran jiki saura kuma duk sukayi wanka suka shirya cikin kayansu sabodaa babu wani event a ranan, saida suka shirya su duka da inaaya da aminnan nata sannan suka ce zasuje su dawo gidan abbah zasuje a parlour suka tarar da mamii da yen mutane kada suka gaisheta suka sanar mata inda zasuje tace to kar su dade tana so ta aike su suka amsa mata da toh sannan suka fita suka nufa gidansu inteesar inda mutanen are less dakin inteesar suka nufa bayan sun gaida Ammah ta amsa masu da fara'a ba jima wa duk suka kwanta dama bacci ya kaisu gidan dan sun san idan har suna can babu bacci, sai da sukayi baccin kusan 3hours karfe daya na rana suka tashi sukayi sallah sai a lokacin inaaya ta tuna da wani abu ta jawo wayanta tayi dialing numbern ihsan ringing hudu ta dauka tana cewa "hello yan hidiman biki ya dai" forming vex inaaya tayi tana cewa "ihsan wlh kin kyauta like sosai shine jiya na ji ki shiru ko" Murmushi tayi tace "habaa sorry sweetheart wlh maama ce ta hanani zuwa wai yayi dare sai dai yau, kinsan yanzu ma na gama shiryawa ina tunanin na kiraki nazo sai after kamu din maama tace sai na kira malam ya'u yazo daukana" smiling inaaya tayi tace "to! Kiyi sauri please mu ma yanzu zamu koma gida daga gidansu inteesar but please kiyi sauri" ihsan tace "ahh babbar bakuwa tazo kenan finally! I'll get to see her not in labari" sallama sukayi suka kashe wayan sai a sannan mimi tace "ni wlh inee sai yanzu ma na tuna da school mun dai samu an yi mid semester, let me call that useless girl ma, na ta binta tazo amma kinga bata zo ba yanzu zatace bata samu wanda zaya kawota ba from hostel" tana kiran firdausi kuwa hakan tace mata babu wanda zaya kawota sai anjima amma zata zo sallama sukayi su ma suka kashe wayan. inaaya ta sauka kasa zuwa kitchen saboda yunwan da taji bata kai da ida saukowa ba kaman ance ta daga kai ta hango aliyu zaune yana magana da Ammah har ramewa yayi nan da nan gabanta ya shiga duka da sauri sauri kaman zuciyanta zaya fado dan tunda suka zo yau ne farkon data ganshi, ba shiri ta juya zata koma da gudu taji Ammah ta kira sunanta babu yanda ta iya haka ta juyo ta karasa parlourn kanta a kasa tana wasa fa yan yatsunta ita kadai tasan halin da ta shiga Ammah tace "daughter ya kin sauko zaki koma kuma meya faru" muryanta na rawa tace "Amm...Amm..ahh da...maaa yun..wa yasa na sauko amma yanzu na daina ji" Murmushi kawai Ammah tayi tace "ba ayi haka ba an taba jin yunwa aka daina maza je kitchen ke nema abinci" da rawar murya ta amsa ta to tayi hanyan kitchen din sau Ammah tace "daughter kaman dai baki ga yayanku ba" a lokacin inaaya ji tayi dama kasa ta bude ta shiga saboda duk basu gane halin da take shiga idan ta ganshi da kyar ta juyo ta kakalo Murmushi ta kalla aliyu da yake zaune yana danna waya ko kallonsu bayayi tace "in...in...ina wuni ya aliyu" bai dago ba kawai yace "lafiya" ta juya da saurinta kaman gudu gudu ta nufa kitchen Ammah dai kallonsu tayi duka ta kada kai, tana shiga kitchen din ta nufa wurin sink ta tsaya hannu ta kai a chest dinta tana taba saitin heart dinta tana jin yanda yake bugawa gashi she hates the feeling with passion bata ankara ba taji hawaye ya silalo mata ta bude tap ta wanke fuskan ta tana dan siririn tsaki ta yi abunda zatayi ta fito kitchen din taji dadin ganin ba kowa parlour da gudunta ta koma sama.
Tun bayan zuwansu nigeria aliyu ya kara wani shiru maganan da kyar ake samu yayi har dan ramewa yayi daka ganshi kaga mai damuwa kwance yake a kan wani makeken gado bayan ya baro wurin Ammah ya nufa gidansu fareed ne, yana kallon ceiling yayi shiru sai aka bude kofa ko kallon kofan baiyi ba saboda yasan mai dakin ne ya shigo har wurin gadon fareed ya iso sannan yace "wai kai aliyu na kasa gane kan ka miye haka kakeyi ma rayuwan naka wallahi sometimes in kana wani abun sai ace bakayi ilimin addini ba" juyowa kawai aliyu yayi ya kalleshi baice komai ba haka fareed yayi ta mishi fadan shi har ya gaji ya kyaleshi ya zauna ya bude wayanshi ya kira khady suka cigaba da wayan su ya yi kaman ba aliyu a cikin dakin.
Wurin 2pm suka koma gidansu inaaya suka tarar da amare da kawaye yanda suka saba zama a dakin inaaya sukayi joining suna fira bayan sunyi lunch can sai ga ihsan ta kira inaaya tace mata tana kofan gidansu da jin dadi inaaya ta fita tarbo ta dasuka shigo saida ta kai ta parlour ta gaida mamii sannan suka nufa sama dakin inaaya suna shiga ta ajiye kan kujeran dakin tace ta zauna saida ta zauna da fara'anta ta gaishe dasu aleesha smiling ya ummi tayi tace "kaga mai hankali harda gaishe mu" dariya sukayi mimi tace "mu kuma mahaukata ko" aleena tace "eh something like that" sukayi dariya ihsan da kawai smiling tayi sai tace "ahh su mimi manya kwana dayawa ba a jin ki" smiling mimi tayi tace "kedai bari ihsan hidiman dayawa" da dariya tace "ke da inaaya yanda kuke fadin hidiman nan kaman ku zaayi wa auren ko kuma kune iyayen bikin" dariya kowa na dakin yayi sultaana kuwa forming anger tayi tace "sannu ihsan su kadai kika gani" dariya Ihsan tayi tace "habaa my sulty sorry wlh gaisuwan naki daban ne shiyasa nafara gaisawa dasu, ya kike and everything" sai a lokacin sultaana tayi smiling ta amsa mata da lafiya qlw sai ga inaaya data fita daga dakin ta shigo tace "Ihsan meet the greatest zainabuu that you've been hearing of" ta dan matsa gefe tana nuna wa ihsan inteesar dake Bayan ta ita kuwa inteesar ta harare inaaya ta wuce ta nufa wurin ihsan tayi hugging dinta tana cewa "finally got to meet you dear! It's so nice" smiling ihsan tayi tace "ayy thanks babe nice meeting you too" suka gama gaisawa kaman sun saba suka dan fara surutu ba sosai ba duk da harda sauran yan dakin akeyi. Karfe 3 amare duk sunyi wanka za a fara masu makeup yau kam kowada mai makeup dinta photographer ma da me videography sunzo sun fara aikin nasu making video of how the event preparation is going on da kuma speech from friends da sisters sai kuma snapping din kayan amare daga clothes, shoes, jewelries komai dai da amare ke saka wa duk yana ta video yana dauka, Nate genius ne mai video din sai photographer kuma artilary photography ne shima ya fara aikin nashi, a daki daya ake masu makeup din kowa da side din da suke aleena lbvmakeover keyi mata sai aleesha kuma dazeita ita dai tanason makeup din dazeita simple sai ummi kuma genovera makeover duk sun fara magic din su a face din amaren su kam photographer da videographer sunata aikinsu na capturing. A can dakin inaaya kuwa masu makeup uku ne suna ma friends da sisters casual da rjtmakeup pro da bookie lavida sai ronaldthe7th, inaaya bataso yin makeup ba kawayen nata suka ce sai tayi da kyar ta yarda tace masu amma babu brows just lips sai little foundation and powder and little eyeshadow and eyeliner haka kuwa akayi mata amma sai kace tayi full make up sosai tayi kyau suka yita MashaaAllah suna yaba kyawu irin nata asoebe dinsu suka saka na sisters atamfa ne irin exclusive embellished super wax dinnan sai shining takeyi sun saka shi ne saboda kamu traditional event ne dinki sukayi duk iri daya wani simple fitted gown me dan tail kadan a baya da dogon hannu ba dogo sosai ba ya wuce quater dai dukkan an daura masu dankwali an hada shi da wani raw silk coffee haka an daura irin na zamani yayi kyau sosai
Khady👆👆 with her anko.
Duk sunyi kyau gwanin burgewa suka fara snapping pictures da wayoyin su, abokanan amare ma sunyi kyau anko din wani atamfa sukayi mai round shape light pink and light purple sai white ne color din atamfan tayi kyau sosai suma they all looked peng. A bangaren amare kuma wani iro and buba suka yi su duka na ya ummi coral sai ya aleesha red sai ya aleena coffee sunyi kyau sosai makeup dinsu yayi kyau sun gama shiryawa tsab! Photo session ya shiga don duk sauran yan matan sun zo dakin ganin amare tun anayi a daki har aka koma parlour ana photo session sannan aka kawo motocin tafiya mutane suka fara tafiya suma grooms din saida suka zo akayi photo session dasu suma sunyi kyau sosi ya mubarak yasa wani white shadda mai kyau ka kamshin cool turaruka yanayi da tsadaddar hula mai kyau, haka ya hilal shi kuwa irin yadin maza me kyau da tsada brown ya saka shima yayi kyau ba kadan ba, sai ya nazeer kuma yasha white shadda da aikin wani color kaman golden kaman ba golden ba duk sunyi kyau sosai tubarakallah sai wurin 5:30pm sannan suka nufa zuwa inda za ayi event din blue velvet marquee ne ga decoration din yayi kyau sosai, su inaaya already sunje wurin amare kawai suke jira ayi entrance din sai wurin 6:30 sannan amare suka shigo anyi grand entrance sosai yayi kyau friends ne farko sai some of the brides sisters sai brides sai sauran sisters duk kowa ya nema sit number dinshi ya zauna event ya cigaba and just like yanda akeyin kowane kamu haka akayi abun nasu yayi kyau da tsari kowa da souvenir nashi under seats aka ajiye su saidai mutun ya duba ya dauko nashi, ansha pictures dan iyayen amare ma baa barsu a baya ba duk sunyi attending ankon wani switzerland lace sukayi mai kyau iri daya kowa da color din nashi.Aliyu ne zaune gefe tunda yaje event din yake zaune shiru da phone sai faman pressing yakeyi sai daya gaji ya ajiye wayan can karshe ya hango fareed zaune da khadija sai faman gaya mata wani abu yakeyi tana blushing shi kuwa tabe baki kawai yayi, sai 10 sannan duk an watse mutane sai dai yasu yasu yan uwa suka dinga rawa har suka gaji inaaya dai dama wuri ta samu ta zauna dan tasan jiya da tasha rawa ciwon kafan da tasha. Zuwa 10:30 duk suka bar hall din suka nufa gida a gajiye suna zuwa sallolin su kawai sukayi suka saka nighties sunyi shirin kwanciya saboda gobe will be a long day tunda safe su abbah and others zaa tafi kano daurin auren ya sameer duk su ammah da mamii zasuje suma kanon da sauran yanuwan su daddy da maama saboda dauko amarya dayake shi babu wani event sai an kawo amarya Saturday za ayi budan kai sai dinner da dare, kafin kace me wasu sun fara bacci cikin su wasu kuwa da waya anata posting ana update duk suka gama around 12 duk sunyi bacci.
Hello beautiful people❤️ hope you're all good still on the wedding I know you must be tired of it by now but I'm sorry it'll soon be over
So please please and please don't forget to
VOTE
COMMENT
FOLLOW AND
SHARELOTS OF LOVE❤️🔐