INAAYA💖
"Ya sa'id I'm tired fa miyasa kake mun haka come let's go I want to see my tsaraba" inaaya ce zaune kusa dashi tana magana tana turo baki shi kuwa dariya yayi mata sannan yace "you'll never change baby sis nace ki bari sai gobe InshaaAllah" sake turo baki tayi zatayi magana sai mimi tace "to! Hajiya shagwaba save your shagwaba please ki bar mamu yaya ya huta kin takura mishi" dariya ya sa'id yayi shi da inteesar da ba laifi ta sake suna ta labari gaba daya "uhmm mimz just leave this girl sometimes in tana abu kamar wata jaririya ko kunya bata ji" hararansu mimi da inteesar inaaya tayi batare da tace masu komai ba sai ya sa'id yace "to yanzu dai lil sis final magana zanyi I'll rest sai around 9pm ku sameni a part ina then I'll give you" sake fuska tayi tana murmushin jin dadi kaman ba ita ta ke ta daure fuska ba tace "yeeey that's why i so much love you bro" dariya ya sa'id yayi ya tashi ya bar parlour ya nufa part in shi.mamii ta sa aka kira mata su inaaya kitchen tace suzo su kama ayi abinci cux su ammi da mommy sun kusan isowa nan suka shiga taya wa ana hada abinci kala kala har zobo inaaya tayi making da fruit parfait mimi kuma tayi corndog inteesar tayi pancakes dama mamii tasa anyi tuwon shinkafa da egusi soup yaji nama kala kala da kuma farfesun kayan ciki da peppered chicken da masa sai fried rice da yaji hanta shima sai aneesah ta hada salad inda tafi kwarewa sai sandwich da different kinds of snacks duk sunyi abincin ne ba quantity mai yawa ba daidai yanda zaya isa sukayi saboda dan mini dinner da zaayi na family in Alh abubakar geidam a gidansu inaaya zaa hadu aci a sha ayi fira sosai shi kuma family meeting zaa tattauna ne kan abubuwa muhimmai da zaya amfani zuri'ar tasu. Duk sun gama jera komai a cikin wani babban garden in gidan inda aka sa kujeru kowane da table a tsakiya kujeru goma suna zagaye da table wurin yayi kyau sosai jera abincin sukayi kan wani dogon table sannan duk suka nufa sama domin yin sallahn la'asar bayan sunyi sallah ne inteesar take cewa "wai what are we going to wear later ni gaskiya dole ma naje gida cux banida kaya" inaaya ce ta amsa mata "ke I'm so tired wlh ni babu gidan da zani rakaki yanzu ku zauna mu huta i have some new gowns you guys can choose a cikinsu" mimi ce ta ce "ina gowns in tun yanzu muyi choosing not sai anjima azo ana jiranmu muna dressing up" dariya inaaya tayi tace "dama su wa ke taking time wurin shiryawa if not you guys" inteesar kam shiru tayi sai kuma tace "uhmm i hope i can choose ma cikin gowns in naki you know how all your clothes can be dull colors kawai babu bright ones" hararan wasa inaaya tayi mata tace "sannu anty brighty idan kinso ki sa bright orange da combination of parrot green saboda brightness kinji" dariya suka saka su duka sai inaaya tace "abeg lets go and check the gowns out" closet in dakinta suka nufa suka shiga ciki gowns kala shidda ne ta fiddo different colors da design tace kowa yayi choosing wani red fitting gown da short sleeve inteesar ta dauka sai shining yake da stones a jiki tana taba shi tana "wow! Wannan gown din ma sai switzerland tazama tawaa" dariya kawai inaaya tayi sai tace "we'll see how you'll go with it ke ba anty brighty ba" mimi dai shiru take tanata duba wasu biyu dake hannunta da wata black da shiny fabric shi straight gown off shoulder amma ba irin off sosai ba sai dayan kuma ash color ne and fabric in plain ne kaman wani ball gown haka yake tana cikin dubawa inteesar tace mata "go for the black one ash in is too plain wlh" nan ma inaaya ta gyade mata kai alamun eh black in tayi choosing ita kuma inaaya closet ba bude ta dauko wani navy blue gown sai shining yakeyi kaman na amare fitting gown ne kawai simple style da long pencil hand yayi kyau sosai "wow!!" Inteesar da mimi suka fada a tare mimi na cewa "kaii inee to fair sai da kika dauke me kyau a ciki sannan kika bamu wannan" "eh mana mimz kyaleta ma" inteesar ta fadi ita kam dariya tayi masu tace "wlh aa wanda na fiddo maku ban taba sa shi ba shi kuma wannan na sashi shiyasa baya ciki" dariya sukayi suna ce mata ai wasa sukeyi fa sai tace "ohhk yanzu lets try them on before the time" dukkan su kowa gwada gown in datayi choosing tayi and MashaaAllah suk sunyi masu kyau kaman don su akayi su ba kamar inaaya tayi mata kyau MashaaAllah gashi ta kara fito da tsantsan kyawunta nan sukayi mirror selfie suka tura ma sultaana nan da nan ta kirasu tafara cewa ina zasuje haka babu ita suka bata labarin dinner in dazaayi sukayita fira har 6 tayi sannan suka kashe wayan kowa ya maida kayanshi suka sauka kasa inda suka tarar da su ummi har sunzo da aleesha da khady suma duk sunyi kyau MashaaAllah! Suna zama sukaji karan bude gate mimi ta tashi ta leka da saurin ta motan su ammi ne taga ya shigo compound in bata jira sauran motocin sun shigo ba da gudu tayi hanyan waje tana ammi sun iso duk sauran suka tashi akayi waje don tarbarsu. Wata mata ce tafito daga cikin motan daka ganta suna kama da baffah sosai ta sha laffaya yellow and brown da murmushi a fuskanta dayan side in kuma yarinya ce kimanin shekaru 23 ta fito sanya da dogon riga na atamfa da veil da handbag nata na lv fara ce sol da kananun idanu da hancin ta dogo ga gasin giranta bakii sosai irin bushy giran nan ne da ita, da gudu su inaaya suka rungume matan nan suna ammi sannu da zuwa da murmushin ta a fuska ta amsa "yawwa yaran nan ohh ni ku sake ni zaku ya da ni bakwa ganin na tsufa wai" sakinta sukayi suna dariya suna cewa "kai ammi a hakan ne kika tsufa" gyaran murya sukaji anyi suka juya sukaga aleena ce dan bata fuska tayi tana fadin "ai dama kullum ammin nan dai ita aka sani babu wanda zakaji yafara ga aleena da aleena" dariya suka yi mata sai inaaya tace "habaa yaa leena my only namesake yazanyi na manta dake" karasawa tayi hade da hugging aleena duk sauran ma suka zo sukayi hugging inta aleesha na cewa "leeee kin ganki kuwa kaman baturiyya iyye what's the secret tell me" dariya tayi mata tana cewa "toooo leesha zaa fara kaman kema baki kallon mirror miye fa secret in daya wuce stella pomade" aleena a fadi tana dariya nan suka karasa cikin parlourn gidan suka zauna. Basu jima da zama ba baba ya iso da iyalanshi baba,mama,hanifa da ishak duk sunyi murna sun tarbesu da kyau 6:35pm aka kira sallah magrib duk suka nufa daki domin gabatar da sallah dakin inaaya cike da yan matan sai hayaniya kakeji aleena,aleesha,khady,hanifa,mimi,inteesar da inaayan itama duk alwala suke dauro wa one by one suka gama suka gabatar da sallahn su bayan sun gama aleena ta kalla aleesha tana cewa "sis wlh mun tsufa ki ji fa duk yaushe aka haifa su mimi duk sun girma yo yanzu sune fa yen mata" dariya aleesha tayi tana "bari kedai sis ai tsufa sai wani kuma yaran nan duk sun girma yanzu kii ji sun fara tunanin aure dan kila ma daya daga cikinsu yanzu baa rasa me saurayi" suna maganan nan inaaya da inteesar suka hada ido suka kalla mimi da tayi shiru tayi zuru da idanu ai sai suka fashe da dariya kaman wasu wanda basu lafiya "kingani ko sis" aleesha ta fada ita kuwa aleena dariya tayi tana fadin "bar su suyi lokacin su ne kinsan soyayyyan irin lokacin nan dadi yake dashi, uhmm gaskiya muzo mu rufawa kan mu asiri mu fiddo mazaje mu basu wuri tun kafin suyi tunanin fara overtaking inmu" dariya aleesha tayi sosai tana fadin "ahh sis ya dai kamata ke zan fada ma wannan dan ni an kusa ma InshaaAllah ko basu ba kina ganin su khady da hanifa manyan kansu ne ai su ma sun fara tunanin overtaking inmu" haka suka dan ci gaba da labarin su suna shewa har mamii ta aiko a kirawo su suna sauka kasa suka tarar parlour cike uncle adnan ya iso da matanshi anty fareeda da twins insu kyawawa adorable twins sai anty fareeha ma ta zo da yaronta areef nan suka gaishe su da murna da jindadi har tsokanan su fareeha ta farayi rayuwar family insu gwanin burgewa with so much love da zumunci zama sukayi aka fara labari dan saboda dinner insu sai kowa ya iso around 8:30pm ne. Suna cikin firan nan su mommy suka iso yaran sunyi murna sosai da gudunsu suka tarbi mommy itama tareda ya sameer,ya feenah,ya ummi,farhana da saleema, daka kalle kowannen su suna cikin farin ciki da jin dadi sai da 7:30 yayi aka watse kowa yaje yayi sallah a shirya zaa hadu can garden din.