INAAYA 35💖

288 24 2
                                    

INAAYA💖










Da suka koma gida mamii tasa aka kai masu abinci daki dan duk rannan basuci abinci sosai ba kaman tasan sunajin yunwa duk sukaci banda inaaya da taci kadan duk tayi shiruuu kawai tana tunanin gobe zata bar gidansu data tuna sai hawaye su cika mata idanu ta gama cin abincin ne ta tashi kawai ta nufa dakin aneesah ta tarar da su biyu a dakin daga ita sai saleema tace ma aneesah "anee I came to talk to you" aneesah tace "uhmm su ya inee me nayi kuwa" smiling tayi tace "come and sit" zuwa aneesah tayi ta zauna inaaya tace "you're a naughty girl you know but you're still my only and best sister I can't tell how much I love you lil one but that won't change the fact that i am more beautiful" murmushi aneesah tayi hawaye sun fara taruwa a idonta dan dama tunda aka fara bikin take avoiding inaaya dan saboda she'll get emotional kasa rikewa tayi ta fashe da kuka ta rungume inaaya tana cewa "ya inee you're always the best can't still believe you're going to leave me everything will change without you the house will be boring i will miss you so much i love you" itama inaaya kasa rikewa tayi hawayen nata suka fara saukowa saleemah dake gefe duk taji wani iri tace "ya inee mana don't be a cry baby kunga nima zaku saka ni kuka" goge hawayen inaaya tayi tace "come on neeshasha stop crying you can always come and see me and I'm just a call away and if you want to we can even move in together" dariya taba aneesah sosai tayi dariya ta manta da kukan tace "habaa ya inee so kike a koroni Aa na dai dunga zuwa everyday everyday har sai kin gaji" Murmushi tayi tace "thats my sister" sai ta tashi ta bar dakin tayi masu sai da safe ta nufa part din ya sa'id a parlour da tarar dashi zaune da waya a hannu yana ganinta yace "su sis an tuno ni" tace "haba ya sa'idoo yazan manta ka" dariya yayi yace "super story kenan" cikin nishadi sukayita magana kafin ta kwantar da kanta kafadan shi hawaye ya fara zuba yana jin digan hawayen ya dagota yace "inee habaa mana what is this why are you crying" fashewa da kuka tayi ta rungume shi tace "ya sa'id i am going to miss you" dago ta yayi ya lallasheta yace "I'll be coming everyday kawai ki dunga dafa mun delish" Murmushi tayi saida sa'id ya tabbatar ta warware sannan as an elder brother ya mata nasiha sannan ta bar part din nashi har tayi deciding taje wurin twins sai ta fasa dan tasan idan suka fara kuka daren nan sai a hankali cikin gida ta wuce ta nufa dakinta tana shiga duk suka juyo suna kallonta yumnerh tace "uhmm inee ina kikaje kika dade haka is it our husband that came" kallon kinada lafiya Inaaya tayi mata tace "ke kika sani yumnerh" dariya kowa yayi wuri inaaya ta samu ta zauna ana ta fira ita dai shiru take duk tunaninta na kan yanda zata bar gidan nasu har dare ya karayi sukayi bacci.






Washegari anty bee ta shigo ta tada su tana cewa "ku tashi yau kunsan yinin biki ko yanzu zaa cika gidan kee inaaya tashi kinsan yau kike gyaran jiki na karshe ko kiyi maza agama kiyi wanka ki shirya" duk haka ta tada su suka tashi yagana tazo ta fara mata gyaran nata da ta ma saba dashi zuwa yanzu ta gama mata sannan tayi wanka karfe 12 tayi karfe daya dazeita tazo tayi mata makeup wani lace tasaka purple na fitting gown an daura mata turban sai bridal veil din ta tayi kyau very simple sukayi ta clicking pictures ne dan event din cikin gidane na mamii so no need suyi sauri yau sauran friends dinta kowa kayanshi yasaka banda cousins da sukayi anko na super wax embellished wata blue da flower red a jiki sunyi kyau sosai sai karfe 3 suka sauka kasa zuwa waje inda akeyin event din mutane nata daukan amarya hoto wasu na dauka tare da amaryan.







Saboda hayaniya aliyu ya bar gidansu yana a gidansu fareed sai 11 ya tashi bacci yayi wanka ya shirya yana zaune wayan shi yayi kara ya duba yaga abbah ne ya dauka ya gaishe sa da girma mawa abbah ya amsa sai yace "aliyu kana ina" yace "abbah ina a gidansu fareed" abbah yace to yanzu kazo ka samemu gidan baffah" ya amsa da to sai bayan yayi sallah la'asar sanna yace ma fareed ya rakasa gidan baffah, a tare suka je gidan suna zuwa duk ba mutane dayawa duk bakin da aka sauke kowa ya tafi gidan bikin yana zuwa a parlour din baffah ya samesu su duka iyayen nasa baba,baffah,abbah da daddy da kakannin su baaba da daada duk cikun girmamawa ya gaishe su suka amsa masa shiru ya biyo baya daada tace "to mijin nawa anyi amarya inadai kishi amma Allah ya zaunar daku lafiya" kowa yayi Murmushi sai baaba ma yace "yanzu sai kaji da amaryarka a kyale mun mata" nan ma duk sukayi dariya aliyu kuwa Murmushi kawai yayi baffah ya gyara murya yace " uhmm to Aliyu dama fadane da gargadi zamuyi maka mun dauka diya mun baka ba wai dan ba a santa ba ko bata da gata ko ta rasa masoya dan haka aliyu ka sani fateema amanah ce muka baka dan haka idan baka rike amanan nan ba kasan Allah bazaya barka ba ka saba amana muna son yar mu sosai muka baka ba dan ka cutar da ita ba dole ne ka kula da ita sannan ita yarinya ce har yanzu sai ka kara da hakuri da ita da wasu halayan yarinta ka kula mana da ita ku zauna lafiya ka rike ta da mutunci ka kyautata mata koma tsoran Allah zakaji wurin yin hakan" shiru aliyu yayi kansa kasa abbah ma yace "aliyu ya zama dole ka kula da amanar da muka ba dan wallahi ka saba mata ni da kaina zan saba maka kar kaga wai dan hakanan aka baka ita ka wulakanta mana diya dan bazan amince da wannan ba kasan hakkinta a kanka kuma kasan yanda zaka sauke hakki Allah ya taimaka" ciki ciki aliyu ya amsa Amin daddy yace "toh! Daa na Allah ya baka ikon yin daidai kawai zan ce" shima yace amiin baba yace "to duk dai kaji aliyu yanda suka fada hakane ka kula mana da yar mu sannan kuyi hakuri da juna Allah ubangiji ya baku zaman lafiya da zuria dayyaba ya hada kawunan ku" kowa na parlour din yace amiin sannan suka sallama aliyu ya tafi, acikin mota yayi shiru fareed yace "lafiya " yayi shiru sai kuma yace "wlh fareed ina tsoron kar Allah ya kamani abun na bani tsoro i am helpless I don't know how to see her as my wife ko nayi kokari bana iyawa amma fadan da su baffah sukayi mani suna cewa sun bani amanah naji tsoron Allah na sauke hakkinta dake kaina shike tada mun hankali bansani ba abun baya yiwu ne i can only see her as a younger sister I don't why I can't" fareed yace "kayi hakurii komai zaya daidaita InshaaAllah kaci gaba da addua.







INAAYA💖Where stories live. Discover now