INAAYA 27💖

259 28 6
                                    

INAAYA💖









Mamii ce ta sauko da sauri su ma su aneesah da twins sun fito daga karamin parlour jin ihun yayar tasu aliyu suka tarar dashi a parlourn tsaye kaman an dasashi mamii tace "ahh ahh son yaushe ka shigo" dakyar ya dan natsu yace "mamii yanzun nan na shigo" mamii tayi murmushi tace "to sannu da zuwa" Murmushi ya kakalo sannan ya zauna mamii ma zama tayi ya gaisheta suka gaisa ta tambaye shi ya Ammah yace lafiya qalau sai ga su aneesah sun karaso parlour ta gaishe shi ya amsa mata twins kuwa inda yake suka nufa suka zauna dayake sun saba dashi suna shiri sosai ayman yace "uncle aliyyy yau kam sai munyi game da kai munyi winning" murmushi yayi ma yaron yace "can you beat me" ammar yace "yesss just try playing with us yanzu we just finished winning and ya neesah lost" Murmushi yayi masu kawai yace ok then, mamii ce ta kalla aneesah tace "aneesah je ki kira inaaya" amsa wa tayi da to sannan ta nufa sama zuwa dakin inaaya. Tana shiga taganta a tsaye tana kai koma cikin dakin kallon aneesah tayi sai aneesah tace "ya inee mamii na kiranki" inaaya tace "meya faru" tace "nothing ya aliyu ne yazo" the mere mention of his name saida gabanta ya buga katon hijab dinta na sallah ta jawo ta saka sannan ta nufa kasa tana zuwa ta tarar ba kowa parlourn sai aliyu kasa tayi da kai sum sum ta shigo parlourn da nesa ta zauna dashi tace "ina wuni" kanta a kasa ya amsa mata da "lafiya qalau, miye na yi wa mutane ihu cikin gida da wani gudu kaman wata yarinya taga dodo" shiru tayi har saida ya kara tambayanta tace "I'm sorry i was frightened that was why" shiru yayi baice komai ba sai kuma bayan minutes yace "uhmm how're you" da mamaki ta dago tana kallonshi sai kuma ta maida kanta a kasa a hankali tace "fine" shiru ya ratsa kusan 10minutes sannan ta tashi tana tafiya a hankali ta nufa kitchen ya bi ta da kallo yanda take tafiya kaman tana tausayin tiles din har ta shige kitchen ruwa da drinks da snacks harda fruit parfait ta hado kan tray ta kai ta ajiye kusa da shi ta koma ta zauna inda take ruwa kawai yasha kusan 30minutes babu wanda yace wani abu can sai yace "we have nothing much to say to each other, I'll be going back day after tomorrow I've given you my card you can use it for everything, your needs and for the wedding preparations and I'll leave my house keys with you in case you need to go and see the house for somethings, and feel free to use the card for school needs and everything cux its my responsibility" sauraronshi kawai takeyi ita dai ya gama tace "ok a hankali" sannan yace mata "if you need anything you can call me" nan ma dai ok kawai tace a haka wani shiru ya ratsa har mamii ta sauko still yana nan tace "son ta kawo maka abinci ko" Murmushi yayi yace "Aa mamii Alhamdulillah na koshi da dai akwai zobon nan ne" yafada yana shafa kai mamii yace "ahh ku da abunku a ga mai zobon nan a gaban ka ta tashi tayi maka" kallon inaaya yayi surprised dan bai san itace keyi ba tsaye ya tashi yana cewa "aa mamii babu komai ni wucewa zanyi yanzu" mamii tace "to ai sai ka dawo anjima ka karba ai ba wani abu" sake ce wa aa yayi saida mamii tayi insisting sannan yace zaya dawo after isha sannan ta amince ya tafi har bakin kofan parlour inaaya ta tashi sum sum ta rakashi saboda kallonda taga mamii nayi mata daidai bakin kofa ta tsaya tace "Allah ya tsare" yace amin ya wuce a ranshi yana tunanin not bad tana da hankali ya kula ya tada mota ya kama hanya zuwa gidansu fareed.tana shigowa ciki mamii tace taje tayi mishi zobo asa fridge yayi sanyi kafin ya dawo ta amsa da to ta nufa kitchen ta shiga aikinta a natse.




A daki ya tarar da fareed kwance yana what he knows best waya da khady zuwa yanzu they're inseparable lovers shigan aliyu yaji fareed yana cewa "come on baby k, you know how much i love you no one can separate us please stop saying that" tsaki fareed yaji a bayanshi sai lokacin ya dago yaga aliyu ya dan wara ido he wasn't expecting him sai yace ma khady yana zuwa ya kashe wayan ya kalla aliyu yace "malan lafiya daga zuwa sai tsoki" aliyu yace "kaine da ban haushi mana kullum bakada aiki sai waya da diyar mutane" murmushi fareed yayi yace "uhmm in mutum yaji zafi ya yi da matarsa mugani, kai ni wlh yaushe zaka rakani zuwa gaida baffah irin na formal introduction din nan nace mun daidaita azo ayi kawai" duka aliyu ya kai mishi yace you're jobless sukayita firansu na abokai sai da magrib tayi sannan aliyu yace "shit banso magrib ya sameni a nan ba wanted going home gashi kaja mun" kallonshi fareed yayi yace "kanada appointment ne" aliyu yace "no naso nakoma nayi sallahn magrib acan nayi isha sai naje gidan daddy idan ban je ba na bani da mamii nace mata ....." bai karasa ba fareed ya fashe da dariya yace "kai guy ba sai kayimun corner ba kace zakaje kaga matarka kawai" harara aliyu yayi masa yace "idan ganinta zanije yi tsoranka nakeji da zan boye maka" dariya fareed ta dinga yi sai aliyu ya mashi dukan wasa sannan ya bashi labarin yanda akayi yace ya gane. A tare suka je masallaci sukayi sallah sannan fareed yace suje tare shima yanason fita duk yau bai fita ba a haka ya shirya a tare suka tafi saidai mota daban ko dasuka isa gidansu aliyu an fara kiran sallah masallaci suka nufa sukayi sallah sannan suka wuce gidan su inaaya, suna zuwa a parlour suka tarar da daddy da mamii suka gaishesu har daddy yake cewa "yau su fareed ne gidan namu" murmushi kawai fareed yayi daddy yake ce masu to dama dinner zasuyi dan haka duk sai sunyi joining a haka babu yanda suka iya sukayi joining table din mamii tasa aka kira inaaya da take daki tun bayan ta gama hada zobon saida taji zuciyanta ya buga data sauko ta tarar da aliyu bata ma kula da fareed ba sai da ta ida karasowa da Murmushi ta gaisheshi ya amsa mata, mamii tace ta fiddo zobo ta kawo kan dining din, taje ta dauko kujeran dake opposite aliyu kadai ya rage haka ta zauna ba yanda ta iya but duk uncomfortable takejin kanta haka sukaci abinci in silence sai karan spoons kawai kakeji suka gama daddy da mamii sukayi parlourn sama ita kuwa inaaya kiran fauziyya tayi ta tayata clearing table saida suka gama sum sum ta shigo parlour din fareed ne yace "amaryan mu wannan shiru shiru haka ban sanki da shi ba fa" kakalo Murmushi kawai tayi tace "kai ya fareed ina yayarmu" dariya yayi nan ya dunga bata labarin khadija this and that da irin yanda yake son ta sukayita fira inaaya harda dariya wanda ya ba aliyu mamaki ashe ta iya magana har haka shi dai nashi ido har wurin 9 sannan aliyu yace ma fareed su je ko tashi inaaya tayi taje ta sanar ma mamii suka sauko sukayi bankwana sannan inaaya taje ta dauko jug din zobon ta bi su a baya dashi sun kai bakin kofan parlour fareed ya karba jug din yace "to amaryan mu kawo na rike kar ki fito dare yayi" Murmushi tayi ya miko hannu ta bashi sai yayi gaba ya basu wuri, Aliyu ne ya juyo yana facing dinta tana tsaye a bakin kofa yace "thanks for the drink" a hankali tace "never mind" yace "alright bye" har ya juya ya tafi itama zata shiga ciki kaman wacce ta tuna wani abu da sauri ta juyo tace "ya Aliyu!" Da dan karfi dan yaji shi kuwa har tsakiyar kanshi yaji yanda ta kira sunan nashi juyowa yayi yana kallonta sai tace "uhmm dama inaso ne zamuje gidan ya aleesha gobe please" kallonta yayi for a minute duk a tsorace take muryanta har wani shaking yake yace "yes it's ok you can go" sannan ya juya ya tafi ita kuwa tayi cikin gida tana sakin ajiyar zuciya ta wuce zuwa dakinta.











Please please and please don't forget to
VOTE
COMMENT
FOLLOW AND
SHARE

LOTS OF LOVE❤️🔐

INAAYA💖Where stories live. Discover now