INAAYA 21💖

306 27 11
                                    

INAAYA💖







           Wurin karfe goma duk sun gama shiryawa cikin white gowns dinsu aleesha gown ne na lace anyi hannun da net lace din white da golden sai jewelry dinga na gold ne tasha an daura mata turban an hada shi da dankwalin lace din sai bridal veil din nan kaman net haka tayi kyau sosai makeup din dan nude haka, sai aleena kuma wani mermaid gown ne na fabric white shima an daura mata turban dinta itama jewelries dinta na gold ne sai ummi lace ne white da golden yellow tayi A-line gown itama an daura mata turban an hada da dankwalin ta tayi kyau sosai da jewelries na gold itama duk sunyi kyau ba karya amma daka gansu kaga jiki a sanyaye karfe 4 ne jirgin zuwa gombe da an gama daurin aure zaa tafi da aleena sai ummi kuma 4:30 ne flight din sai aleesha da a nan abuja zaa ajiyeta saida yamma za a kaita. Duk anata shiri yan matan yau friends kowa kayanshi ya saka sukuma sisters ankon lace ne kowane peer group da color din su but same design ne dinkin skirt da riga peplum sukayi inaaya dai hakanan take komai ba karfi saboda ita dai gata nan wani iri iri takeji tunda ta tashi ga yanda takejin zuciyan nata na bugawa da sauri sauri,basuyi makeup ba yau yan matan duk simple.




              Tunda aliyu ta tashi yau yake jin ba dadi a ranshi kuma hakan yana da hadi da abunda su baffah suka kirashi suka sanar mishi kwana biyu da suka wuce duk komai jiki ba kwari yakeyinshi karfe 11 amma bai shirya ma daurin auren ba sai ga fareed yazo ya shigo dakin nashi ya tarar dashi zaune yace "habaa mana aliyu ya akayi baka shiryaba ni da ba daurin auren gidan mu ba ma na shirya har na fito saboda 11 yanzu already kuma 12 ne daurin auren aliyu kallonshi kawai yayi ya kada kai yace "fareed at first banyi niyyan gaya maka ba but now i just felt the urge to tell you i have a problem" kallonshi fareed ya tsaya yi sannan yace "problem kuma aliyu wani irin problem na me and why didn't you tell me all this while" shiru yayi baice komai ba sai kuma nan ya fara sanar mishi halin da yake ciki. Cikin mota daya suke fareed na driving aliyu a gaba yasa wani sabon shadda fari da aikin golden yasa matching hula da takalma daka gansu kaga tsadaddu ga agogonshi designer sai kamshin turaren nashi daya saba yakeyi dolce and gabana  ko kai ka ganshi sai ya burgeka ka kara kallonshi the only thing missing was smile kwata kwata babu smile a fuskan shi kuma ba daurewa yayi ba just a straight face 11:40 suka isa an noor mosque wanda yake cike cike da jama'a duk girman masallacin saida mutane suka cikashi wasu har a waje anata gaisawa da iyayen amaren da duk sukenan su baffah da mahaifin aleena da mahaifin ummi, daurin auren dai an samu halartan din bin manyan mutane.



          Karfe 12:00pm dot aka daura auren Fatima isah sani gamawa da Hilal muhammad damagum daidai lokacin message ya shigo wayan aleena suna zaune hilal ne ya turo mata "Alhamdulillah officially mine" ai kuwa kuka ta fashe dashi nan aka fara bata hakuri inaaya kuwa ta na zaune tunda aleena ta fashe da kuka bayan ta duba wayanta sai kuma taga 12 yayi zuciyan ya dunga bugawa itama heart dinta na squeezing ta rasa dalili, mubarak ne shima yayi ma aleesha message "finally mine and only mine" itama water works din nata ya fara ai ummi tun kafin tayi receiving wani message itama sai kuka ana ta lallashin su can sai ga message din nazeer ya shigo "babyn ya nazeer it's official i own you see you soon i love you" ai kaman ana tunzura su kuka anty fareeha tace "dillah can kun cika ma mutane kunne da kuka ana baku hakuri ma baku ji ba ku kuka ce kuna so ba habaa" dariya kowa yayi banda amaren da inaaya da tunda 12 din ta buga duk ta kara shiga wani rudu ta rasa miye dalilin ji takeyi kaman wani abun ya sameta duk bata a cikin hayyacin ta ta rasa gane miyasa kawai wani uneasiness takeji.



        A cikin babban masallacin nan waliyyan amare da na anguna sukayi exchanging maganganu aka daura aure imam ne ya fara anouncing an daura auren fatima isah sani gamawa da angon ta hilal muhammad damagum a bisa sadaki dubu dari biyu da hamsin, sai akayi anouncing na aleesha cewa an daura auren maryam usman abubakar geidam da angon ta mubarak hassan malumfashi abisa sadaki dubu dari da hamsin, sai akayi anouncing na ummi an daura auren Aishatu sanusi bichi da angonta nazeer Mukhtar kofar mata abisa sadaki dubu dari uku bayan an gama anouncing mutane kowa ya zata shine na karshe sai suka ji anyi anouncing wani da yasa duk wanda suka sani zare idanu suna contemplating abun kamar a mafarki sukaji ana anouncing "AN DAURA AUREN FADIMATU UMAR ABUBAKAR GEIDAM DA ALIYU IBRAHIM ABUBAKAR GEIDAM A BISA SADAKI DUBU DARI BIYU" duk su adnan, naseer,sameer,abby da sa'id da duk sauran yan uwan suka fara kallon juna cikin rudu tashin hankali da rashin fahimta kan furucin da sukaji anyi if they're not mistaken sunan aliyu sukaji da kuma na inaaya kuma aure? Kowa da tambayoyi kala kala a ranshi suka juyo su duka suna kallon ya aliyu shi kuwa ana anouncing ya rufe idanunshi yana jin yanda heart dinshi ke yi sai ya fara tuno abunda ya faru *flash back
Aliyu yana zaune bayan zuwansu nigeria an fara hidindimun biki ranan Wednesday sai yaga abbah na kiranshi a waya ya dauka sai yace "ka samemu a parlour na na sama yanzun nan" ba bata lokaci ya nufa parlourn abbah yana zuwa yaga abbah da daddy da baffah da baba ya gaidasu cikin girmamawa ya zauna kasa sai baffah yayi gyaran murya yace "aliyu watanni kusan 5 dasuka wuce mukace mun baka wata biyu ka fiddo mata ko ba haka ba" zuciyar aliyu ta buga ya gyada ma baffah kai yace eh sai baffah ya ci gaba da cewa "toh! Miyasa bakayi abunda muka saka ka ba?" Yace "baffah ayi hakurii ban samu ba ne" sai baffah yace "to kasan bazamu saka maka ido ba ko shekara 30 zakayi ba mata kullum sai kunci kakeyi akan abunda ya faru shekara shidda da suka wuce ka ki daukar kaddara har yana barazana da lafiyar ka, dan haka kaman yanda muka baka wata biyu yanzu har wata kusan shidda ma kenan mun yanke hukunci zamu aura maka matar da muka zaba maka" wani abu ya hadiye a makoshi ya dago yana kallon baffah cikin rudani ya fara kaman zai bada hakuri abbah yace "dakata aliyu babu abunda zakayi ya canza abunda muka yanke kuma munyi hakanne saboda kai da lafiyar ka kuma munsan cewa za kayi mana biyayya" kasa samun bakin magana yayi bayan abunda abbah ya furta sai kawai yasamu kanshi da cewa "wacece" baba yace "yar uwarka ce fatima ta wurin daddy" da wani tashin hankali ya dago yana dubansu yace "abbah dan Allah kuyi hakuri kar ku aura mun ita wallahi yarinya ce shekararta duka bata wuce 16 ko karatu bata gamaba dan allah ku barta tayi karatun ta ni naji ku aura mun ko wacece zan zauna da ita na maku biyayya" daddy yace "ya isa aliyu idan bakaso muna iya fasawa amma saboda mun damu da kai mukaga hakan ya dace domin kai da ita dukkaninku need a spouse" abbah ya dakatar da daddy yana cewa "babu maganar fasawa a cikin wannan maganar InshaaAllah aliyu bakada mata sai inaaya  don haka saidai idan rashin kunya zakayi mana kace baka auren ta" kada kai yayi idanunshi sunyi jaa yace "aa abbah kayi hakuri bata kai haka ba Allah yasa haka ne mafi Alkhairi ya kara girma" Murmushin jin dadi sukayi abbah yace "I'll forever be proud of you my son Allah ya cigaba da yi maka albarka" ciki ciki aliyu ya amsa sai baffah yace "mun yanke shawaran zaa daura aurenku tareda danasu aleesha amma sai bayan tayi hutun semester sannan za ta tare dakinta" aliyu ko fahimtar su bayayi kada kai kawai yakeyi sai ya samu kanshi da cewa "amma baffah an sanar ma yarinyar ne itama ai yakamata dan kar a shiga hakkinta" daddy yayi saurin cewa "duk abinda nacewa fatima bazata bijire mani ba dan haka babu matsala" kada kai kawai aliyu yayi ta fito daga parlour ya nufa part dinshi ya fada kan gado ya rasa me yake mashi dadi ko two minutes baayi ba sai ga ammah ta shigo dakin nashi ta karaso ta zauna kan gado tace "aliyu nasan kayi magana da abbahn naka shiyasa kake haka inaso nace maka kayi hakurii komi mai wucewa ne kuma duk abunda Allah yayi sai ya faru don haka sai ka rungumi kaddara hannu biyu inaaya yarinya ce mai hankali karama kuma nasan halinta na san ta zatayi maka biyayya sam batada fitina idan har ka sameta ka dace mata ta gari kuma uwa ta gari ma yaranka" yana jin ammah na magana ya dai kasa cewa komai yana kwance ammah tasa hannu cikin gashinshi tadan baje shi kaman karamin yawo sai ta tashi zata tafi a hankali ya kira sunan ta ta taso yayi hugging dinta tayi hugging danta back kafin ta bar dakin shi kuwa alwala ya dauro ya zo ya dinga salloli har da istikhara yayi da karatun qurani sai ya samu saukin abunda yakeji a ranshi.
*end of flashback
A hankali ya bude idanunshi ya sauke su kan yan uwan nashi da suke kallon shi kasa kawai yayi da kai sannan ya juya ya kalli fareed da yayi mashi smiling assuringly da murmushi shima ya kakalo yayi ma fareed din sai ya tuna maganan su na daxu kafin a tafi daurin auren da yagaya ma fareed

*flashback
"Wane irin problem gareka aliyu" fareed ya tambaya sai ya fara ce mishi "fareed su baffah aure zasu man kuma yau zaa daura auren" kallon kana lafiya fareed ya shiga yi mishi yace "what! Aliyu aure yau shine kake gaya mani yanzu" yace "sorry man I couldn't tell you saboda nima just two days ago suka gaya mani and that too yarinyan daddy wallahi I'm just pitying her she's just young ko karatu yanzu ta fara I'm way too older than her ina laifin su sama yar 24/25 haka idan ma hadani auren zasuyi" fareed dai da mamaki yake kallon aliyu da keta maganan yace "sorry bro kayita addua Allah yasan abunda yasa hakan ya faru yasan itace Alkhairin ka ba wata ba I'll advice you ka rungumi aurenka da za a maka she's young zatayi maka biyayya sosai I barely know her but wallahi she's a nice girl so cool and simple also she'll make a good wife for you zakaga tana iya abunda yar 24 bata iyawa age is just a number she's matured enough" tsaki aliyu yayi yace "I'm telling you the problem kana ce mun haka told you she's too young tsaran su inteesar fa ce how do you expect me to live  with her as a wife just how? she's a sister to me" fareed yace "pls ango tashi ka shirya ni dai na baka shawara" hararanshi aliyu yayi ya tashi ya shiga closet domin shiryawa.
*end of flashback
Mutane da yawa sai zuwa suke suna ma su baffah murna suma angwayen abokannan su sai murna ake yi masu aliyu kuwa yanuwan nashi suka zo suka tsaya su ji mi ke faruwa sai bayansu suka ji baffah na cewa duk kowa mu hadu gidan daddy bayan reception ya wuce kawai sun sha mamaki amma ba yanda zasuyi haka suka nufa wurin reception jiki a sanyaye.




           Da kyar aka sa amaren sukayi shiru sannan aka dan kara gyara masu makeup jamaa sai shigowa akeyi ana congratulating din su wasu guda sukeyi, inaaya tun da ta shirya gadai ta nan kawai har anty fareeha ta kalleta tace "inee lafiya" ta kakalo murmushi tace "lafiya lau" kallon tausai kawai fareeha ta dan yi mata domin ummi ta sanar mata abunda ke shirin faruwa bayan su baffah sun gaya masu, ta bude kofan closet ta shiga kan kujeran dake a closet ta zauna jingina kanta a kujera ta na rufe ido tasa hannunta daidai saitin zuciyarta tana jin wani iri, karfe 1:00 khady ta shigo tace ga angwaye su sauko ayi hotuna a parlour din daddy dake kasa aka saukesu kawayen su sukayi masu rakiya sannan suka bar su suka basu wuri. Saida suka yi maganan su for like 10minutes sannan wani abokin mubarak, shamsu yace to lovey dovey din ya isa haka dariya kawai sukayi ya shigo da photographer aka fara hotuna sisters, cousins, friends da family da kyar su inteesar suka samu inaaya ta sauko ayi hoton bayan mamii ta tambaya ina take ta sauko picture bai fi uku tayi ba taja ta tsaya gefe mamii tace "inaaya lafiya mi ya sameki ko kin ji wani abu ne" kallon mamii tayi da confusion tace "mamii wani abu wane abu kuma? Ni banjin dadi ne shiyasa" gyade mata kai kawai mamii tayi sai ta dan bata tausayi.












Hello lovelies❤️ yeey! It's a double update💃dan dan dan dan dan............. what just happened to our inaaya💔 🙆‍♀️, what is going to happen now🤷‍♀️.


Please please and please don't forget to
VOTE
COMMENT
FOLLOW AND
SHARE

LOTS OF LOVE❤️🔐

INAAYA💖Where stories live. Discover now