INAAYA💖
Zaune inaaya take hankali kwance tana kallonta taji karan kofa ana knocking ta tashi a hankali ta nufa ta bude kofan wa inda ta gani ne tsaya ya sa ta ihu tana tsalle tana rungume su a tare Aminnan nata ne inteesar da sultaana da mimi sai ya khady tayi kusan 10days bata gansu ba dama duk kadaici ya isheta shiyasa tayi farin ciki sosai da ganin su mimi tace "ke malama sakemu kar mu koma sauran kuwa dariya sukayi mata yanda tayi da fuska kaman zatayi kuka khady tace "habaa inee kaman wata jaririya please let's go in a tare suka shiga ciki suna murmushi a parlour suka zauna sai a lokacin suka gaisa inaaya na cewa "wallah you guys have the perfect timing dama I'm bored" kaman jira mimi take tace "dama married couple na zama bored" hitting dinta sultaana tayi tace "corrupt lady" duk sukayi dariya, inaaya ta tashi ta nufa kitchen ta hado masu su ruwa da drinks da kayan motsa baki dai ta kawo ta ajiye masu tray din nan da nan suka hau ci dan dama ba bakon su bane gidan suna ci suna kallo suna labari. Sai da aka kira zuhr prayer sai ga aliyu ya sauko daga sama fuskan nan tasa neutral suka gaishesa ya amsa masu a sake ba laifi sannan ya nufa wurin kofan zaya fita yace "fateema come and close the door" sum sum ta tashi tabi bayansu su inteesar kuwa boye dariyar dasuke san yi sukayi, a tare suka isa wurin kofa ya bude zaya fita tace "Allah ya kiyaye" yace mata amin ba yabo ba fallasa har ya fita sai ya juyo kafin ta rufe kofa yace "uhmm please fareed is coming over for lunch can you cook something please" da dan Murmushi ta gyade kai tace "sure" sannan ta rufe ta nufa ciki su sultaana ke mata dariya wai tayi hankali yanzu ta iya ma miji rakiya ita kuwa sharesu kawai tayi sai tace "uhmm you guys please muyi sallah muzo kitchen ku tayani muyi lunch" mimi tace "ai mun dauka sayo miki akeyi har yanzu" dariya ya khady tayi tace "ku dai kun sa inaaya gaba ku tayata mana" inaaya na jin haka tace "kai ya khady har da ke fa" khady tace "lallai ma kinada aiki ni zani tayaku girki ba gidana ba" bata fuska inaaya tayi tace "ni ya khady ai bana yin lunch da yanzu sai dinner zanyi da yamma amma duk saboda ke ne yasa zaniyi kuma kice baki taya mu" yar dariya khady tayi tace "lallai ni ce glutton da zakice saboda ni zakiyi" inteesar tayi dariya tace "ahh to ai tasan mu bama ci" sultaana tace "help me see oo" inaaya tace "no ba wani glutton duk dalilin ki ne zaniyi girki ba husband to be dinki bane zayazo lunch kuma dan yasan kina nan shiyasa yace zayazo dan so daya ya taba zuwa gidan nan yanzu dalilinki yasa zayazo kinga dole ki taya" ai tun kafin inaaya ta gama maganan su mimi suka fara dariya mimi harda tafa hannu tace "ohh inee ke kuwa his heart his soul zayazo gani" khady kuwa har ta fara wani blushing kaman tana ganinsa sam ta kasa cewa komi ta barsu sunata fama teasing dinta a haka har sukaje sukayi sallah suka nufa kitchen inaaya tace "toh ya khady yanzu ki gaya mana favorite din na shi sai a dafa" khady tace "kun rainani dayawa yaran nan shaa biryani ko casserole da chicken salad da fruit parfait but na grapes preferably" inteesar tace "wow kiji love tasan komai kanshi" sultaana tace "love is cute" mimi tace "hmm bakusan its sweet bama tukunna" sunata dariya banda inaaya a gefe da ta shiga tunani kowa has a normal happy life banda ita Khady already knows alot about her husband to be da abunda yakeso but ita she can't say ga abinci daya fi so apart from he likes zobo kaman tasa kuka haka taji tana tunanin wace irin rayuwa ce haka inteesar ta tabota tace "lafiya malama" tace "uhm..ahh..aa ba komai let's get started ayi casserole din da biryani da salad and parfait and i have some cupcakes it'll be for dessert mimi tace "cool lets get started ya khady tayi biryani din ni kuma da sultaana zamuyi casserole and inteesar should make the salad inaaya kuma parfait" haka sukayi deciding kowa da fara aikinsa inaaya tace ma inteesar "inteesar i already have marinated chicken kawai kiyi grilling dinshi" duk suka fara aikin nasu cikin two and half hours suka kammala sun fara jerawa a dining inaaya kaman ta tuna wani abu tace "ohh I have something to do" da ido kawai suka bi ta ta dauki karamin pot a wanke ta bude wani drawer a kitchen ta fiddo ganyen zobo ne ta zuba a ciki saida ta wanke shi sannan ta dora a wuta mimi tace "ohh abunda mijin naki keso kika manta kiyi shine harda sauri ohh ni aminatu aure me canza mutane" duk suka sa dariya inaaya ta daure tace "mimi mimi wlh ke ba hmm!" Nan ma dariya sukayi sultaana tace "ya kika kasa cewa komai inee" sukayi ta tsokanan ta cikin 20minutes ta gama hadan zobon tasa a jug tasa fridge sannan suka nufa sama zuwa dakin inaaya ta shiga tayi wanka ta fito ta shirya cikin dogon riga na voile mint green da ash yayi kyau sosai khady tace "hmm dolen ya aliyu yayi drooling" sukayi dan dariya sannan ta kuma ce "kaii nima i need a bath I'm smelling kitchen" mimi tace "dama ya khady dolen ki tunda husby to be zayazo" share ta khady tayi ta shiga tayi wanka ta fito cikin closet din inaaya ta nemo wata sabuwan abaya maroon tasha stones ta saka sosai tayi kyau tana ta faman kallon mirror tana blushing.