INAAYA💖
Washegari cikin jindadi inaaya tayi shirinta wani doguwan riga na atamfa light purple da olive green cinderella style yayi kyau sosai style din ga hannun long pencil hand ne tayi daurin zahra buhari style sai ta ciro wani veil olive dan babba haka sai tasaka shi a kan kai kawai taji tana son sakawa ya mata kyau sosai handbag na lv da takalmi na lv tasaka da Apple Watch a hannunta tagama shirinta tsab gwanin burgewa tayi kyau ta sauka kasa mamii na parlour kallon diyar tata tayi gwanin ban sha'awa tayi murmushi tace "yau dai ina fatan ba ni kikazo ki gaya ma zaki fita ba kin tambayi wanda ya kamata" dan murmushi tayi sai tayi kasa da kanta tana gyade kai mamii taji dadi ta dafa kanta tace "Allah ya miki albarka" a zuciyarta tace amiin sai sukaji karan bude kofa da sallama mimi ce da inteesar suka shigo gaida mamii sukayi suna zama wani kallo sukeyiwa inaaya datasha gyale a saman kai, mamii tace "to ko kun fasa tafiyar" dariya sukayi suka tashi suna aa zasu tafi mamii tace to su gaishe mata amaryan sukace to! Suka nufa waje kaman suna jira ana shiga mota inteesar tace "inee lafiya dai wannan sabon salo gyale saman kai" murmushi kawai inaaya tayi mata mimi kuwa dariya tayi tace "ke kuwa intee aure ba wasa ba" suka saki dariya nan haka sukayita tsokanan ta ita dai bata ce komai ba har suka isa gidan su sultaana suka dauketa itama saida tayi maganan gyalen inaaya. Wuni sukayi ma aleesha taji dadi sosai sai bayan magrib suka baro gidan kamar kar su tafi har take cewa ai bayan isha zasu je gidan abbah ma yi musu bankwana kudi ya mubarak ya basu kowa 10thousand suka mishi godiya suka tafi, a ranar mimi da inteesar gidan su inaaya suka kwana sukayi having fun sosai yanda suka saba daren da su inteesar zasu koma sunyi kallo da games mostly inteesar da inaaya ne suke yi mimi sai waya take da love din nata ko gajiya basa yi har inaaya tayi mata magana tace "wai ke mimi ki isa mutane kaman zaku cinye juna haba" Murmushi kawai tayi tace "ba laifin ki bane fa wait till you fall in love with ya Aliyu I'll ask you ya kikeji" dariya inteesar tayi ita kuwa inaaya shiru tayi gabanta na duka sosai jin abunda mimi ta fada just the mere thought of being in love with him makes her heart beats at a faster rate, haka daren nasu ya kare sai 2 sukayi bacci. Da safe karfe 10 suka tashi duk suka shirya sukayi breakfast flight din su inteesar 2:00pm ne don haka sun dan kara spending time together dayake nan su abbah zasu biyo su dauketa duk ta gama shirya kayanta and all 12:30 su abbah sukazo gidan har lunch sukaci ammah har wani kara ji tayi da inaaya ita kuwa kunyanta ma takeji ahmad kuwa sai tsokanan inaaya yake yana cewa "anty inaaya gashi har zamu tafi bamu ci girkin amarya ba" duk sauran dariya sukayi banda inaaya da ke feeling uncomfortable saboda aliyu dake wurin. Karfe 1 suka kama hanyan airport wurin 1:40 suka isa su mimi da inaaya kaman suyi kuka dan rabuwar da zasu yi kuma inteesar ce tace "come on don't cry if not nima I'll just 3months fa and I'll be back for the biki wow mimi we gotta start preparing call me everyday on facetime bamuda time sosai dole mu shirya sosai Fa wedding of our one and only inee" Murmushi kawai sukayi a haka suka rabu an fara boarding plane suka yi ma su Abbah Allah ya kiyaye sai abbah ya kalla aliyu yaga idan zasuyi magana da inaaya ganin haka aliyu ya matsa kusa da ita yace "I'm leaving call if you need anything" a hankali tace "Allah ya kiyaye" yace amiin ya kakalo Murmushi abbah da daddy sunji dadin hakan wucewa sukayi sunata daga masu hannun suna waving har suka bacce masu gani kafin duk suka juya sukayi wurin motocinsu don komawa gida.
*five days later
Inaaya ce zaune tare da mamii a parlour ta sa ta a gaba tana ce mata sai ta zaba furnitures ita kuwa inaaya ko maganan ma bataso tace ma mamii kawai ta zaba kowane tayi order she's Ohhk with it amma ina mamii bata rai tayi shiyasa babu yanda ta iya ta karba wayan mamii tana kallon furnitures din different kinds of furnitures ne irin na turkey wasu complete set ne na bed,wardrobe,dining table,tv stand, sofas,da centre table wasu kuma bed ne kawai wasu sofas kawai haka tayita kallo tagama sannan ta ce ma mamii "mamii kawai a dauka me complete set din yafi" itama mamii shi yayi mata kyau don haka ta amince, shirin biki mamii tafara sosai tun bayan tafiyan su abbah har waya tayi da yar uwarta dake a maiduguri anty Baraka wadda duk yaran ke kira anty Bee sunyi magana har tace ma mamii zata turo wata mai gyaran jiki yar chad ta iya sosai tazo ta zauna a nan gidan ta dinga mata gyaran jikin tunda 3months ne kawai bikin mamii ta amince shirye shiryen su sukayi sosai wanda inaaya tanaji tace ma mamii ita wallahi bata wani gyaran jiki sai da anty bee ta ce mamii ta ba inaayan waya ta ce mata bata isa ba sai anyi shi kar ma ta bata mata rai babu yanda ta iya dasu haka ta amince akan saura two months bikin matan zatazo. Suna gama selecting kayan da mamii ta nufa sama ta shiga dakinta cikin sauri tayi shiri tayi sallah saboda lectures din da take dashi by 2:00pm ko da ta sauko kasa mamii na kitchen ta sanar mata ta tafi school mamii tace to ta bi a hankali kuma sai yaushe zata dawo, tace zatayi 2pm-4pm sai kuma 4-6pm mamii tace mata kar tayi dare ta amsa sannan ta fita ta nufa wurin mota elantra hyundai 2018 ta shiga ta tada nan da nan mai gadi ya fito ya bude mata gate yana daga mata hannu ta fita daga gida ta kama hanyan baze university.