WATTPAD @SIYAMAIBRAHIM
Mental stability:Mania is an affective disorder characterized by elation of mood,rapid thought and speech,extreme over-activity and irresponsible behaviour.
3.Blurred
Kuka sosai take yi kamar me dan duk da ta so dannewa da boye bacin ranta ta hanyar hana hawayen ta su tsiyayo a yau da safen nan,abin bai yiwu ba sakamakon wani irin abu da ya tsaya mata a kirjin ta zuwa throat din ta jamar zai yi bursting mata chest wanda ba komai bane face bacin rai,gani tayi in ba kukan tayi ba toh lallai tana iya hadiyar zuciya ta mutu..
Ita ta sani within her heart reaction din ta na dazu was a little bit harsh a matsayin ta na daughter In-law tayi reacting a wannan manner din but again ta san da bata bar wurin ba toh da an mata mai kan kat din da ya fi wannan...
Ita dai har yau ta kasa tantance aibin ta daya tal da za'a ce bata da yancin kan ta a cikin gidan mijin ta sai yadda aka tsara mata rayuwa kamar wata tunkiya..
Sai da tayi kukan mai isar ta sannan ta tashi ta hau share hawayen ta tana mai karfafawa kan ta zuciya daga bisani ta shige toilet ta wanke fuskar ta ta fito dama wannan dalili ya sa ta ki tafiya sashen mother-inlaw din ta ta tsaya ta ci abinci if not hala throughout yau din nan ba zata ci komai ba dan bakin ciki...Gaban mirror din ta ta tsaya karema kan ta kallo tana ta nazari sai kuma ta ja kujerar madubin ta zauna ta hau yin kwaliyya har dai ta shafe damuwar dake kan fuskar ta ta dora rantsatssen adon ta mai kyau mai tsafta..
Tana gyara daurin ta ta hango sa ta madubi yana kallon ta kamar maye sai ta share sa kamar bata gan sa ba ta karasa daurin ta ta daga mayafin tata dora bisa kan ta ta shimfida sa ya zauna da kyau sannan ta juya ta kai hannun ta bag holder din ta dake kusa da ita ta dauko wata kyakyawar fancy bag samfurin Bonia mix colour blue and white,daukar wata key tayi daga lock din ta ta juyo gare sa..
Za a yi tunanin magana zata mai amma haka ta zo ta wuce sa da kadan sai yayi saurin shan gaban ta ya ja ya tsaya..
Fuskar sa da alamar tambaya bakin sa na dan bude da nufun yin magana sakamakon mamakin ta da ya gama kama sa..
Itama ja tayi ta tsaya tana jiran jin me zai ce da ita dan yau kam ba a gidan zata kwana ba sai dai duk abin da zai tafasa ya kone..
Sassautar da muryar sa kasa yayi kamar marar gaskiya ya ce
"Ummitah ina zaki tafi da sassafen nan,this is just past 10 na safe kuma kin shirya da shirin tafiya anguwa,ina zaki tafi?tukunna ma da izinin wa zaki fitan"?sai da ta rausayar da kan ta tana tauna kalaman da zata fitar mai da su gudun kar bacin ran ta ya sa ta furta mai kalmar da zai bashi damar ganin kaskancin ta...
Ajiyar zuciya ta sauke tana mai saka kwayar idanun ta cikin nasa kamar dai ba ita ta gama kukan ba dazu ta natsu tsaf sannan ta fara magana cikin kwantar da murya amma kuma maganar kamar wuta suke a kunnuwa da zuciyar mai sauraron sa..
"Asim...,fita zan yi,fita zan yi in tafi inda ake kauna ta kamar a bauta min,fita zan yi in je in samarwa kai na kwanciyar hankalin da kai ka kasa samar min bare ka bani har ya zamo dawwamammiya a rayuwa ta,na sha fada maka muddin za'a wayi gari ina cikin gidan nan kuma za'a bakanta min toh kai ma sai ka dandani bakin cikin daga gare ni dan ba zan dauka gabadaya in dorawa kai na ba,kamar yadda kake da kuma abin so ga kowa a gidan ku toh nima haka nake ya abin so ga kowa a namu gidan,dan haka na tafi kuma kar ka kuskura ka kira ni dan kana kira na na rantse maka da Allah sai alert yayi blowing"!!!..
Dumm,,haka ya ji gaban sa ya fadi kan sa ya fara mai ciwo dan bai so a ce an kure ta har haka ba sai dai still ba zai bar ta ta tafin ba dan haka tana kare masa kallon kyama ta ja tsaki ta juya,step daya da ta taka ya kawo hannun sa da nufin taba ta amma wani tsawar da ta daka mai sai da ya saka sa maida hannun nasa cikin sauri..
"If you dare Asim....i swear i will surprise you"!!daga haka bata sake ce da shi komai ba ta sa kai ta fice..
Tsaye yayi yana bin hanyar da ta fita da kallo kamar sakarai haka ya juya ya zauna kan mirror chair ya dogara elbow nasa da saman table din madubin yayi ma kumatun sa madogari da ankle din hannun sa..
Duniyar tunani ya fada yana ta yi kamar bai da abin yi,ideally a day like this which is saturday,tana gida kuma duk abin da zai mata a wannan ranaku na saturday bata tanka mai duk da ya san akwai babbar bridge mai zurfi a matrimonial relationship din su kuma greater percentage din,he attributed to it but hakan na nufin ta gaya mai maganganu son ran ta har tana mai barazanar zata tafi ta samarwa kan ta kwanciyar hankalin da ya kasa samo mata,?!..
Yin wannan tunani da kuma kalaman ta da suka fado mai sai kawai ya tashi tsaye ya hau canza kayan jikin sa yana magana kamar marar lafiyar kwakwalwa...
"Ni...ni Asim Ummitah ke ce mawa zata tafi ta samarwa kan ta kwanciyar hankalin da na kasa samo mata?ni Asim saboda ta maida ni shashasha marar tunani ta saka kafa ta tsallame ni ta bar gidan nan har da yi min gargadin kar in kuskura in kira ta,lallai na mata sake da yawa kuma yau zan tunatar da ita matsayin mu a cikin gidan nan"...
A haka yana ta fade fade dai har ya kammal shirin sa cikin kaftan dusky pink ya saka hula da takalmi ya dauki makulli ya fito da karfin sa kamar zai tashi sama,ai ko yana yin kwana ya ji murya ana ce mai
"Ka kuskura ka fita daga gidan nan da sunan bin wannan yar mai farar kafar toh sai na tsine maka Asim in dai ni na haife ka,dan haka wala ka koma ko ka wuce wun aikin ka ban son shirmen banza da wofi"!!!zuciyar sa na tafarfasa ya juya ya koma ciki..
Wannan na daya daga cikin dalilin da ya sa ya ce ba zai zauna a gidan nan ba a lokacin da auren sa ya taso amma haka mahaifiyar sa tayi ruwa tayi tsaki akan shine babban da kuma shi ya kamata ya dasa tarihi,da ya nuna tsantsar damuwar sa sai ta ce mai bayan bikin ko wata takwas suka yi sai ya tafi duk inda zai tafi da matar sa toh a haka har tsawon shekaru biyar da auren nasa amma ta ki yarda ya bar gidan wai shine babba ita bata son yayi nesa da ita..
Yanzu ga irin ta nan ya zo da zafin sa akan ya je ya nemi Ummitah kamar yadda suke kiran ta dan ya hukunta ta amma abin ya gagara hala kafin ta dawo ya huce kuma hakan ba zai mai dadi ba...
YOU ARE READING
TAMBARI[The dark hunt]
HumorPeople round the world are being taunted and looked down on due to the feeling of misery and low self worth that is caused as a result of direct and indirect factors which gradually leads to so many social negligence and harassment in many situation...