WATTPAD @SIYAMAIBRAHIM
Mental stability:Epilepsy/Seizure disorder is a fits/convulsions.epilepsy is a paroxysmal and transitory disturbance of the function of the brain which develops suddenly,ceases spontaneously,and exhibits a conspicuous tendency to recur.
32.Dark Hunt.
"Ni dai sunana Noor Sulaiman kuma alakar dake tsakani na da marigayi shine auratayya,ya kasance miji na kimanin shekaru biyar kusan shida a yanzu"..dan pausing tayi tana lumshe idanun ta kasancewar bitter part of her life that is yet to be revealed..
Sauraron ta ake yi Hajiya Sifa'u kam ta gama cika fam dan ba haka ta so shari'ar ta kasance ba a wurin ta all these formalities shouldn't be discussed a nan iyakar a yankewa Ummitah hukuncin kisa kawai kowa ya huta.
Muryar Ummitah ne ya dawo da ita reality sakamakon cigaba da tayi da bayanin ta..
"A shekarar da muka hadu a shekarar muka yi aure da Asim dan dama ya zo ne a dai dai lokacin da nake bukata kasancewar akwai wasu dalilai nawa da na barwa kai na,sai ban ja da yawa ba da ya tunkare ni da maganar auren,abu na farko da ya faru shine sanar da iyaye na da nayi akan sa,basu da matsala at all mahaifi na yayi welcoming Asim zuwa gidan mu ya dauke sa a matsayin dan sa ba wanda zai auri yar sa ba,a wun Asim ya so ne bayan haduwar mu da weeks a mana aure amma sai mahaifi na ya hana akan zai fi mu fuskanci junan mu,bayan kamar watanni hudu da haduwar mu Asim ya kuma dago maganar aure a cewar sa shima a gidan su a matse ake akan batun auren sa,nan ma na kuma sanar da mahaifi na sai ya ce ya amince amma ba za a yi bikin mu ba sai bayan kamar watanni uku,ni ban san dalilin sa na tsawaita bikin ba haka shima Asim,haka muka bar zancen kullum Asim bayan sati ko karshen sati sai ya dauko hanya tun daga nan Niger zuwa gombe ya zo ya gan ni ya koma,da haka muka rinka soyayya soyayya sosai ba na wasa ba har aka sako maganar bikin mu,kwata kwata bai wuce sati ba aka yi bikin nan washegari aka dau hanya daga gombe aka kawo ni nan Niger state cikin suleja"..dan numfasawa tayi sannan ta cigaba
"Tun ranar da aka kawo ni na fuskanci mahaifiyar sa mai son gargajiya ce irin na yaren ta wato yoruba because a ranar sai da aka yi performing wasu rites sannan nayi alwala na shiga gidan,da zuciya daya ta tarbe ni haka late father In-law di na ban taba ganin canji fuska daga wun kowa ba,a fannin miji na bana fuskantar sauyin family dan ya maye min gurbin komai a rayuwa ta,a haka muna zaune tare har shekara ta kai ta zagayo babu damuwar komai,iya matsala ta shine yadda ya hana ni zuwa gida ko sau daya dan ganin iyaye na abin na dami na,sai dai in na mai magana sai ya ce jira yake in lokaci ya kai zai raka ni da kan sa ya dawo har in gama ganin su sai ya dawo ya dauko ni,da haka yake rufe min baki,but kullum abin na dada gaba gaba ni kuma kewar su na dami na duk da ina da aminiya kuma kamar yar uwa ta a nan garin amma ina kewar iyaye na sosai sai dai bai taba bari kewar nasu ya mai tasiri a zuciyar sa ba in na dauko maganar zai fita abin sa haka zan hakura ya kyale sa"..
"A shekarar mu ta biyu da aure Allah ya jarabce mu,mahaifin Asim ya rasu a daidai gabar da muke jin dadin zamar mu,wannan rasuwa ya janyo matsaloli kala kala da bana jin na taba fuskantar irin sa tunda nake"..ajiyar zuciya ta yi hawayen da ya sauko mata ta saka yatsar hannun ta karami ta share cikin total heart break murya na rawa ta dora..
"Bayan rasuwar mahaifin Asim mahaifiyar Asim ta sauya gabadaya ta canza kamar ba ita ba komai bata so kowa bata son ya kusance ta ko ba da ita kake magana ba zata dau zafi ta hau fada,ban taba bata laifi ba dan danganta hakan nayi da rashin da ta shiga amma sai abin yayi replicating ya fiye tunanin kowa,tun ina bata uziri har na gane sauyawa tayi na gabadaya dan ta tsaya ta min abinda ran ta ke so ko a gaban waye ba komai bane a gare ta,sai a lokacin aka fara fuskantar matsala ta samu da sai da aka kai ta asibiti,for that long period of time ni kadai ke kula da ita,in kusance ta in kula da ita ta zage ni ta habtare ni wasu lokutan ta dake ni,i never complained and reveal it out ko ga miji na bare family di na,ana haka ne har ta warke muka dawo sai ta fara fiddo sabbin halaye gare ni a kullum in na kai mata ziyara kamar da sai ta aibata ni ta saka ni gaba da zagi da gori,babu abin da ya fi daga min hankali sama da irin aibata ni da take yi kuma miji na na ji na gani bai taba sanyaya min ba sai dai ma ya zo ya kara min da nasa".
"Muna haka shekarar nan ta kara wucewa makong 2 years amma Allah bai azurta mu da karuwa ba,tun lokacin mahaifiyar Asim ta kuma taso ni gaba cin zarafi babu wanda bata min haka nake daurewa dan Asim bai kuma dago min maganar zuwa ganin iyaye na ba sai dai mu gaisa a waya kuma ina gudun fada masu halin da nake ciki kullum in aka min abin da ya daga min hankali sai in kira mahaifiya ta in roki addu'ar ta akan samin haihuwar ko zan huta,ana haka ne dai still komai na tabarbarewa sai wataran mahaifiya ta ta kira shi Asim din ko me ta fada mai ban sani ba amma na ga sauyi kadan na wasu lokuta kafin yayi resuming halayyar sa na da"..
"A third year din mu da aure ne na fuskanci kaskanci da wulakanci daga wun Asim fiye da yadda mahaifiyar sa ke min,ban taba fadawa kowa ba sai mahaifiya ta da na rinka roko da ta dawo nan suleja da zama dan in rinka ganin ta amma ta ce ai haka ake aure,ganin ba zan sami yadda nake so ba sai na kira mahaifi na na roke sa da ya nemowa mahaifiya ta gida a nan ta rinka zuwa ina ganin ta dan Asim ya ce baya so in dawo gida sai na haihu,na kare Asim din shi kuma mahaifi na yayi zaton cikin ne da ni sai ya biye min ya sa aka samo mai gida a nan suleja ya ma mahaifiya ta dabara ta zo suleja dan duba mai wani kasuwancin sa akan in ta zo akwai gidan da zata zauna a nan,ita kuma sanin nature din aikin sa sai bata mai jayayya ba ta yarda ta zo nan suleja akan zata duba mai business for 2weeks sannan ta koma,nayi zaton zata kira ni in ta zo amma bata yi hakan ba sai ni ce da na gaji da jiran jin kiran ta na saci hanya wata juma'ah na tafi inda mahaifi na ya min kwatancen gidan"..hawaye ne ya kuma sauko mata sai ta share ta dan yi shiru sannan ta cigaba
YOU ARE READING
TAMBARI[The dark hunt]
HumorPeople round the world are being taunted and looked down on due to the feeling of misery and low self worth that is caused as a result of direct and indirect factors which gradually leads to so many social negligence and harassment in many situation...