Blandish

500 65 4
                                    

WATTPAD @SIYAMAIBRAHIM

Mental stability:Dejavu is a sense of having previously experienced new events or seeing it before.

5.Blandish

Duk inda natsuwar ta yake ya kau a wannan lokaci idanun ta rufe da kishi ta banko kofar parlor din ta ta shige ta saka mai lock ta ciki ta zauna a kasa nesa da attracted set of chairs din ta,cire spec din idanun ta tayi ta cire veil din dake kan ta ta hau rusa kuka kamar an mata sakon rasuwar wani nata na jikin ta...
  Kuka wiwiwi haka ta rinka rera sa tana jin zafi a zuciyar dan ba karamin baci ran ta yayi ba ganin wannan fitsitsiyar yarinyar da bata kai matsayin da za a saka ta layin mata manya ba ta zo ta yi tsaye gaban mijin ta tana kwarkwasa tana wani murmushi shima ya biye mata yana yi irin dama tun asalin filazal sun san junan nan...
  Ta dade a haka tana kukan tana tanadar mai abin da zata mai a zuciyar ta dan yau sai ta hukunta sa yadda ya dace haka kawai ya rinka bata hawan jini ana zaune siddam..
  Daga haka ne barawo bacci yayi gaba da ita duk da cikin baccin tana kuka ciki ciki kuma hawaye na zubo mata...

★★★
Some hours later
8pm

Shigowar sa gidan kenan duk tension da anxiety na nemar dagula masa lissafi kamar marar gaskiya haka ya daure ya nufi sashen iyayen sa yana tafe yana dari dari..
  Da sallama a bakin sa ya shiga parlorn,yau ma kamar kullum suna zazzaune ana hira dukkan su sai dai babu mutum daya alamun ta koma gidan ta kenan..
  Kallon dattijuwar nan ta jiya yayi ya matso kusa da ita ya zauna bayan ya cire takalmin sa..
  Murya a sanyaye kamar maraya ya ce da ita
"Hajiya barka da dare"!!Juyowa tayi ta kalle sa ta kure sa da wani irin kallon da sai da ya gane ya kuma tabbatar da cewa batun abin da ya faru a boutique din sa dazu yayi nasarar zuwa gare ta sauran na gaida sa amma bai iya amsa masu ba sai gyada kai,ganin tana nan zaune kuma babu alamar zata masa zazzafar fada dan haka ya kuma marairaice fuska kalar tausayi ya ce
  "Hajiya aunty Amira ta koma ne"?cigaba tayi da kallon sa hade da bashi impression din wato ka dai aikata abin da gaske kenan...
  Wannan grimace ta mahaifiyar nasa ya dada dulmuyar da tunanin sa sai ya rasa me zai ce kuma me zai yi dan ta gane cewa an sami akasi a wun fahimta dazu da abin ya faru kuma ya san ko ya tsaya yi mata bayani daga yanzu har nan da shekara ba yarda zata yi sai dai in ita Saudat din ce da kan ta ta mata bayani ta warware daurin goron da aka mai...
  A dan dame ya kawo kan sa da nufin dorawa bisa kafar ta sai muryar ta ya katse sa daga yin abin da yayi niya
  "Tashi ka zauna Sadauki"!!haka kawai ya ji gaban sa ya fadi dan takan jima bata mai magana da wannan tune din ba,shi ya zai yi yau ga mahaifiyar sa ga matar sa duk akan bridge of communication ya zai yi toh shi...
  Gyara zaman yayi ya langabar da kai ya nade kafafun sa kamar mai zaman karatu ya hade hannayen sa wuri daya  ya dora saman kafar sa wearing a heart broken face...
  Kallon sa mahaifiyar tasa ta cigaba da yi kamar bata san sa ba sai yanzu shima ita yake kallo,bayan wasu seconds ta sallami sauran dake zaune a wurin sannan ta fara magana da sigar fada fada da nasiha nasiha..
  "Sadauki ka yiwa kan ka adalci kenan?a ce duk natsuwa da hankalin wannan matar taka amma ka bude ma idon ka toka ka wanke su tas saman wata mace...ya dace Sadauki?Saudat ta cancanci haka daga gare ka Sadauki?wai ni yaushe ma ka rikide ka zamo haka ne"?shiru yayi dan bai da bakin magana saboda Hajiyar tasa ta hau kuma one word from him can demoralize his facts...
  Yana nan shiru sai ya jiyo murya na fadin
  "Toh ke Fulani me ya sa kika kasa yi masa uziri ne haka kika hau shi da fada alhalin kin san dole akwai dalilin sa da zai yi proving nasa innocent"?abin da aka fada kenan daga daya side din wanda yayi necessitating dagowar kan sa..
  Sauke idanun sa yayi akan mahaifin sa dake sanye da medicated glasses fuskar sa duk grey hair ne haka kan sa da aka ma matsakaicin aski shima ana iya hango grey hair din dake wurin,da ganin sa an ga dattijon da bai da wani matsala sosai dan MashaAllah jikin sa akwai hutu a tattare da shi haka ba zai gaza 75years ba a duniya but kwanciyar hankali ya sa tsufar tasa bai bayyanu sosai ba...
Tashi tsaye yayi ya isa ga wannan mutumin ya rungume sa cikin farinciki yana fadin
  "Baba na yaushe ka dawo ba tare da sani na ba?ba ya dauko ka"?murmushin fuskar sa ya fadada yana fadin
  "Sadaukin Hajiyar sa irin wannan tambayoyi haka kamar dan jarida,hala bayan bana nan barin kasuwar kayi ka je ka koyo ilimin jarida"?cikin sigar raha yayi maganar wanda ya saka ita kan ta Hajiyar murmusawa amma bata bari sun gan ta ba dan so take ta mai fada akan kar ya jijjibo mata rikici cikin gida dan kalau take zaune da daughter In-law din nata...
Gyaran murya tayi ta ce
"Au sai yanzu ka tuno da wadannan tambayoyin kenan?toh ba kowa ya je ya dauko sa ba sai matar taka da kake da shirin juyawa baya,Sadauki kar ka shiga harka ta dan zan saba maka"!!..
  Shi kam kasa ce mata komai yayi yana dai rike da hannun mahaifin nasa ya cigaba da yi mai tambayoyi har dai mahaifin nasa ya tari numfashin sa ta hanyar ce mai
"Sadauki yaushe ka koyi surutu da yawa haka kamar aku,ko zama fah baka bari na yi ba"..sai a sannan ya sosa keyar sa yana ma kan sa dariyar wautar sa..
  Zama mutumin yayi kusa da Hajiyar Sadauki sai kuwa ta budi baki dan cigaba da yi mai fada ganin kamar ma bai bada maganar nata muhimmanci ba tunda har dariya yake yi,sai karaf muryar ta ta datse
  "Haba Hajiya kin bi kin tasa sa gaba sai fada kike mai kamar wani karamin yaro,ni fah ba karar sa na kawo dan ki rinka yi mai irin wadannan maganganun ba,haba Hajiya,ni kawai karar sa na kawo dan kafa shaida amma ni ban ce ki mai fada ba ai in fadan ya kamata a mai ni zan yi amma ai ban yi ba"!maganganun da ya fito daga bakin Saudat kenan yayin da take karasa shigowa cikin parlorn cikin doguwar hijabin ta har kasa fuskar ta fayau babu kwalliya ko digis sai natural beauty din ta...
  Bude baki Hajiyar tayi tana mamakin ta dama ita ta sani amma ganin kullum in yayi laifi ta saka sa gaba tana mai fada sai matar sa ta hau kare sa har dai tayi shiru ya sa yau ta ga ya dace ta nuna mai illar abin da yake ma Saudat din amma sai gashi an kuma maimaita irin ta kullum alhalin ita ta kawo karar amma yanzu ta ce ba fada ta ce a yi masa ba toh in ba fada za a masa ba me ya dace a mai..
  Tambayar da Hajiyar ta yiwa kan ta kenan cikin zuciyar ta..
Muryar dattijon nan ne ya fito cikin raha ya ce
"Toh ke Fulani kin dai gani,matada miji sai Allah ba a shiga tsakanin su wanda ya shiga ma kunya zai sha,shin har yanzu kina kan bakar ki na hukunta Sadaukin naki"? Kallon ta ta mayar kan Saudat din hade da fadin
  "Amma ke kam an yi diya marar jan aji ce maki aka yi ana kare miji haka a gaban sa?ai nan gaba kadan sai ya raina ki ya rinka abin da ran sa ke so dan ya san ko yayi akwai mai mara masa baya abin ba zai dame sa ba"cikin shagwabe fuska Saudat ta ce
  "Ni dai eh na ji Hajiya ki bar shi haka nan ai ya ji kuma kuskure ne"kallon ta Hajiyar ta cigaba da yi kafin daga bisani ta ce
  "Uhum Allah ya kyauta Saudat"shiru tayi sai kuma ta tashi tana fadin
  "Abincin ka zai yi sanyi tun dazu na gama arranging maka"!!tayi maganar tana mai fuskantar mijin nata wanda shi kam ya gama sarewa da al'amarin Saudat din dan some hours ago she was like,,a mad dog but yanzu har kare sa take yi kar a masa fada lallai Allah ya cece sa yau a hannun ta kar ta mai gashin kuma...

TAMBARI[The dark hunt] Where stories live. Discover now