WATTPAD @SIYAMAIBRAHIM
Mental stability:Internally Displaced Persons(IDPS)are group of people who have been forced to leave their homes in order to avoid the effects of armed conflict,violation of human rights,natural or human made disasters and who have not crossed an internationally recognized state border.
12.The game is on
The next morning
Da karfin ta ta tashi full of confidence dan ta san babu wannan bakin kumurcin a kusa da ita kuma sooner or later ta san nesa ta zo kusa dan da hawayen sa sai ya neme ta a lokacin da ita kuma bata ra'ayin sa dan ya janyo kiyayya mai karfi a tsakanin su,soyayyar sa a zuciyar ta ya rikide ya dawo guba dan haka a macigi take kallon sa ba masoyi kuma mijin da ta aura ba..Bayan ta ida addu'ar tashi daga bacci ta yi hamma,sauka tayi daga gadon ta fito zuwa parlor tana gyara rigar baccin ta hade da waige waige,can ta hango makullin motar da ta taho da ita sai ta dauka ta koma dakin.
Jim kadan ta kimtsa ta fito dan samarwa kan ta abin da zata saka a cikin ta because ta gama sakawa a ran ta batun soyayya ko kauna tsakanin ta da Asim babu shi kuma sai dai ramuko..
Fast food tayi ta hada tea da noodles ta dora bisa mini round tray ta dauko zuwa parlor din ta zauna,a nan tayi breakfast din ta ta kishingida har bacci ya fara daukar ta sai ta jiyo karar wayar ta a cikin bedroom..
Dauko wayar tayi ta dora idanun ta akan screen din wayar tana karema numbers din kallo,bata gane number din ba dan haka tayi ignoring call din,a gefe ta aje wayar ta koma ta kishingida abin ta..
Sai wayar ta sake kara,nan ma tayi ignoring sai da abin ya ishe ta ta ja doguwar tsaki,ta dora wayar a kunnen ta bayan ta daga cikin daga murya da fada ta ce
"Asim ka fita harka ta,ka taba ganin inda aka yi auren dole ne ko aka zauna da mugun miji ne?iyee ina tambayar ka?dan haka for the very last time kar ka kuskura hannuwar ka su kara danna numbers di na a wayar ka har kayi tunanin yin magana da ni,i know by now u must have been thinking about my trap on you ko ba haka ba?toh bude kunnuwar ka da kyau ka ji ni,aure dai a hannun ka yake right,toh ni da ake auren na ce bana yi,kwata kwata bana yi na tsane ka na tsane ka kuma ka jirayi sammaci daga kotu dan na rantse maka Asim sai na tona duk wasu abubuwan da kake min kuma a bainar jama'a ka ga ta nan duniya zasu san da zaman mummunar hallayar ka akan matar ka just wait and see The game is on"..tana kaiwa nan ta cire wayar da nufin kashewa sai ta ji wata murya daban tana fadin
"Please dan tsaya ki bani seconds"!..dumm haka ta ji gaban ta ya buga dan ko a bacci ta tashi ba zata manta muryar nan ba..
Salati ta rinka yi a zuciyar ta jin baranbaramar da tayi da wanda bata taba takaitacciyar magana da shi ba.
Muryar sa ta jiwo wanda hakan ya sa ta ji wani kunya mai tsanani ya kama ta rasa abin cewa tayi sai shiru da tayi tana sauraron jin me zai ce..
Cikin natsuwa da kamun hankali da kamala ya fara mata magana kamar haka.
"Da fari zan baki hakuri na kiran ki kai tsaye da nayi ba tare da hujja mai karfi ba,sannan ki gafarce ni na kira ki a lokacin da bai dace ba lokacin da ran ki ke a bace wanda yayi sanadiyar jin sirrin ki da bai kamata in ji ba da fatan zaki min hakuri ki fahimce ni"!!.
Ita dai uffan bata ce ba dan ta san ta faru ta kare,in dai mutum na da kaifin tunani da basira toh zai fahimci inda maganganun ta suka dosa because ta yi su ne in an outburst da ke nuna ran ta a bace yake..
Jin tayi shiru sai yayi magana yana mai ssukar da muryar sa kasa
"Noor kina nan?are you still there"?dan gyaran murya tayi tana fadin.
"Yeah"!daga haka shiru ne ya gifta tsakanin su sai daga bisani shi din yayi jarumtar kawo karshen shirun ta hanyar cewa
"Alright,dama kira nayi in ji ko lafiya na duba wurin aikin ku baki nan kuma ko a hanya ban gan ki ba sai na ce bari in kira in ji ko lafiya"!!maganar nasa mamaki ya bata,wai "bari in kira in ji ko lafiya" irin dama can yana da numbern wayar ta ne ko kuma sun saba da juna ne..
Kasa amsa mai tayi sai shiru da ta cigaba da yi kafin ta ce
"Tohm na gode...sai anjima"!!sauri tayi zata katse wayar sai ya dakatar da ita yana fadin
"Would you like to talk about it"?sai tayi shiru,sarai ta gano inda ya dosa amma tayi kamar bata gane ba tayi shiru..
Silent impression din ta ya sa yayi zaton hala ma bata gane abin da yake nufi bane dan haka ya kara elaborating more akan maganar da yayi
"I mean,,about what happened earlier when i called you..would you like to share it"?duk dai kame kame yake yi duk da dama abin da yake son ji da sani kenan akan irin rayuwar auren da take yi da kullum fuskar ta cike take tam da damuwa da kadaici..
Kasa amsa mai tayi duk ta matsu ta sauke wayar daga kunnen ta dan abin ya shammace ta bata yi zaton bin kafar kwakwafin sa ya kai har haka ba.
Shi kam kamar dole instead ya rabu da ita sai ya kuma daukar maganar yana fadin
"I heard you saying something related to exposure,kuma na ji kina ta kiran Asim Asim Asim,and i learnt something out of your talks,kamar dai shi wannan Asim din shine mijin ki kuma daga dukkan alamu yana da nasaba da rayuwar kunci da kadaici da kike ciki presently kina nemar hanyar rabuwa ne da musabbabin wannan damuwa taki am i right"?..
Ajiyar zuciya tayi sai nan da nan hawaye ya taru a idanun ta dama ita din mai saurin kuka ne kawai tawakkali ne da imani ya sa take danne hawayen nata at times in ta ji ran ta ya sosu da al'amuran Asim da mother in-law din ta wato mahaifiyar sa..
Kamar ya san tana cikin damuwa kuma kuka take yi sai kawai ya ji ta bashi tausayi dan ita abin ya mata yawa,a sanin sa da ita yana iya bada shaidar cewa tana da zurfin ciki ba na wasa ba sannan ga damuwar yau da kullum da take fama da shi,da tana iya furta damuwar nata ma wani ko wasu toh da abin ya mata sauki amma sam ta fi ganewa binne damuwar ta a ran ta which is very wrong..
Gyaran murya yayi yana saka kan sa a situation da state of mind da take ciki
"I know you are hurt deeply,but da zaki min wata alfarma daya da zan baki tabbacin matsalar ki zai kau,ki yi hakuri ki sanar da ni wani abu akan rayuwar ki ko da kankani ni yin hakan ne zai yaye maki wannan kuncin da kike ciki"!!!.
Bata san ya aka yi ba amma ta tsinci kan ta da rera kuka mai cin rai da zafi wanda ita kadai ta san zafin da take ji a ran ta,ba komai ke dada ingiza hawayen ta bulbulowa ba illa in ta tuno good times din da suka yi sharing tare da Asim da kuma yanzu da abin yayi kamar an yi ruwa an dauke..
Jin kuka take yi sai ya shiga bata hakuri shi gani yake kamar shi ya janyo mata yin kukan kuma hakan bai kamata ba dan kamar zaluntar ta yayi,kafin yayi magana ta riga sa
"Please keep this conversation within us,ka rufa min asiri i still respect my marriage and my husband dan haka ka bar wannan maganar a tsakanin mu kar ka fadawa kowa and please pretend like nothing of such have happened ka ji"?muryar ta spot out her deaspiration akan al'amuran rayuwar ta kuma da gaske bata so maganar ya fita dan haka ya ce
"Is okey..is okey ba komai"!bata bari ya sauke numfashi ba ta dora da
"Nagode,sai anjima"!!har zata datse wayar sai ta tsaya na seconds sannan ta ce
"Thank you"daga haka ta kashe wayar ta zauna ta ci kukan ta mai isar ta sakamakon tunano abubuwa da dama da suka wuce a rayuwar ta..
A nan tayi spending day din nata tana ta tariyo abubuwa kala daban daban..
Da dare yayi kuwa sai ta kunna wayar ta ta kira aminiyar ta Fadilah wanda ita kadai take saka ran zata taya ta share bakin Tambarin da Asim ya bar ta da shi..
YOU ARE READING
TAMBARI[The dark hunt]
HumorPeople round the world are being taunted and looked down on due to the feeling of misery and low self worth that is caused as a result of direct and indirect factors which gradually leads to so many social negligence and harassment in many situation...