WATTPAD @SIYAMAIBRAHIM
Mental stability:Dementia is a largely irreversible disease due to degeneration of the brain cells.there is intellectual impairment with defects in memory,judgment and orientation together with physical,emotional and personality changes.usually one's consciousness is preserved.
17.Pessimism
Zariya City
At the bride's homeYau thursday ya kasance rana da za a gudanar da bridal shower na amarya Saima Aliyu,duk da ba nan kusa wato da safe za a yi event din ba,amma ana ta shirye shiryen apartment daya da aka ware mata ita da kawayen ta da su kadai zasu halarci wannan event din..
Tun safen ake ta testing mini cotton nylon outwear din da za a saka a event din wanda ya kasance off white da flower design din multicolour roses..
Amarya dai na ta baccin ta sakamakon gajiyan kai kawo da take ta yi wai a hakan ma dan ta tsagaita wasu events din kenan da ta angon ne da tun ana sati guda to the wedding za a fara events but zama da tayi tayi nazari mai zurfi sai ta ga duk wahala ne mafi sauki a zabi biyu zuwa uku wanda hakan ya kasance dan daga kamu sai bridal shower sannan walima..
Fadilah ce zaune a kasa tana ta faman cin reheated tuwon semovita da draw soup da aka yi a cikin gidan jiya ma baki,fitowar ta wanka kenan ta zauna ta hau ci sai hada zufa take tana sharewa..
Ummitah dake zaune tana kallon wani series movie a wayar ta mai suna Empire,ganin jan hancin ya ki karewa ya sa ta dago kan ta tayi sai tayi ido hudu da tulin tuwon dake plate din,waro ido tayi ta kuma kallon Fadilah dake ta cin tuwon sai ta ajiye wayar ta bude baki tana fadin
"Lilah tuntuni tuwon kike ci ko dai yanzu kija fara"?bata dago ta kalle ta ba ta ce
"Wace irin tambaya ce wannan Ummitah kina jin yadda nake ta jan hanci tun dazu sakamakon zafin abincin nan amma ki ce wai yanzu na fara ci"!kasa boye mamakin ta tayi ta furta
"Lallai Lilah,cikin randa gare ki ne yanzu shin"!?wani haushi ne ya kama Fadilah ta amsa mata cikin fushi da
"Eh din in cikin randar gare ni ina ruwar ki da ni"?wata dariyar tsokana ta kece da shi har da dafe ciki kafin ta ce
"Lilah ni fah a da ina zargin wani abin but yanzu na gasgata ga proves da evidence ko ta ko ina"!dakatawa Fadilah tayi daga cin abinci ta dago ta kalli Ummitah har ta gama yi mata dariyar tsokanar da take mata sannan ta ce
"Ummitah zargin me kike min halan"?kallon ta Ummitah tayi sanna ta gimtse dariyar nata kafin ta bata amsa da
"Lilah ciki ne kuma da ke"?wani irin tsalle Fadilah ta daka ta dire ido rufe ta hau balbale Ummitah da masifa ta inda take shiga ba ta nan take fita ba kamar zata bugi Ummitah ita kuwa ban da dariya babu abin da take mata.
"Aniyar ki mummuna a gare ni ta koma maki Ummitah ta yaya ko hutawa daga yaye Azma da nayi ban yi ba ki fara shafa min wani bakin Tambarin"?!dariya kawai Ummitah tayi har sai da Fadilah ta koma ta zauna abincin ma ta ji ya fice mata a rai..
Cikin maganar hankali da lissafi Ummitah ta ce
"Amma Lilah ai ba aibu bane kika sani hala da abin ki a jikin ki but bai zauna da kyau ba sai bayan Barrister yayi molesting din ki"!harara ta bankowa Ummitah sannan ta ce
"Ai ke kasa gane maki nake yi wasu lokutan,tare da ni kike ko tare da shi"!dariya Ummitah tayi kafin ta tashi ta koma kan gadon ta dauko tablet pad din ta ta cigaba da kallon ta leaving Fadilah to be talking to her self all alone..
Haka dai bata jin dadin tuwon ta tura dan tayi kewar tuwon da gaske because rabon ta da zama yin tuwo a gidan ta tun ranar da Noor ta kai masu ziyara har ta kwana..Wani scene aka nuna a cikin movie din da take kallo inda Cookie Lyon ta birkice ta ki yarda da mijin ta Lucius Lyon a lokacin da yake ta mata bayanin kan sa akan laifin da take tuhumar sa da shi har ta kai ta sa aka harhado mai kayan sa aka biyo ta da shi zuwa Empire din ta sa aka zazzage masa kayan sa ta mai magana mai zafi a zuciya sannan tayi tafiyar ta kuma dalilin hakan sakamakon abin da ya faru ne a previous episode da aka gama..
Fadilah na cin tuwon ta kawai taji ta tayi kwafa tana magana da kan ta kamar haka.
"Maza..maza kenan,duk yadda zaka basu yarda da amincin ka ka sadaukar da farin cikin ka saboda su,rana daya tal zasu bude maki babin tijarar su da cin zarafin su"..
Kallon ta Fadilah tayi da mamaki sai dai bata ce komai ba har ta gama cin abincin nata sannan ta tashi tana tafiya tana tambayar ta
"Hala me ya faru kike ma maza kirari"?ajiyar zuciya mai nauyi Ummitah tayi sannan ta ce
"Dabi'ar maza ta cin amana,wani ko ka bashi yardar ka akan yayi abin da yake da kudirin yi dan dai ya bar ka kai ka tsira da mutuncin ka sai ya ki tsabar mugun hali da bakin nufi"!sarai Fadilah ta fahimci inda zancen aminiyar nata ya dosa sai dai ta kada kai ta fita tana fadi a ran ta
"Dama ai na fadi a bikin nan sai kin furta matsalolin ki kuma da kadan kadan a hankali kina ta zayyano su,saura kiris ma ki furta asalin abin da wannan azzalumi mai suffar babalawon garin nasu ke maki a badini" (hmm kiyaya kenan,kawai saboda ita dai ta tsani Asim mijin aminiyar nata sai ta rinka alakanta shi ko siffanta shi da wasu irin abubuwan ban haushi if not kowa ya kalli Asim ya ga namiji mai kyau daidai misali but tunda ya ce bai ga kyakyawar dabi'a ba toh ita Fadilah ta tsane sa tsane mai zafi)..
Duba yaran ta tayi ta ga duk sun yi bacci kuma basu jima ba dan still akwai murmushi saman fuskar baby Azma alamar daga baccin wasa na gaske ya shige ta kenan,kallon su tayi ta tofa masu addu'a sannan ta fita kai kwanikan waje wondering yaushe yaran suka fara baccin safe,sai wata zuciyar ta ce mata ai wasa suke yi daga haka suka bige da bacci,cire tunanin tayi a kan ta tayi tafiyar ta..
★★★
At the bridal shower event
YOU ARE READING
TAMBARI[The dark hunt]
HumorPeople round the world are being taunted and looked down on due to the feeling of misery and low self worth that is caused as a result of direct and indirect factors which gradually leads to so many social negligence and harassment in many situation...