Heartfelt

264 50 0
                                    

WATTPAD @SIYAMAIBRAHIM

Mental stability:Anxiety Neurosis is a diffuse apprehension that is vague in nature and is associated with feelings of uncertainty and helplessness .

23.Heartfelt

Sallama Ammah ta yi a bakin kofar dakin amma ba a amsa ba,cigaba da yi tayi but still babu response sai ta saka hannu ta murda handle din kofar sai ta ji shi a bude.
  Tura kofar tayi ciki ya budu ta sa kai ta shiga bakin ta dauke da sallama still.
Ganin duhu ya mamaye dakin ne ya sa ta kai hannun ta kan switch din dakin ta kunna light nan take haske ya mamaye dakin,sai dai abin mamaki ko kafin ta maido duban ta ga dakin har duhu ya sake mamaye dakin..
Kai hannun ta tayi da nufin sake kunna switch tsammanin ta ko bata kunna da kyau bane amma sai ta ga switch din is on kawai daukewa haske yayi..
  Fitowa tayi daga dakin dan dubawa ko wutar gidan ne yayi sparking dan da wuya su yi rashin wuta because da an dauke solar ke cigaba da aiki so is some how kind of wired a ce the light went off haka nan..
  Bata gama fitowa completely ba ta ga haske ko ta ko ina,sai a sannan zuciyar ta ke raya mata maybe Ummitah idon ta biyu kuma ita ce zata kashe light din da hannun ta...
  Girgiza kai tayi ta koma cikin dakin,bata tsaya ba ta wuce zuwa bed side drawer ta saka hannu ta dau remote dake nan kamar antenna connector tayi switching light din dakin,da fari normal general light ya kawo sai ta sake dannawa nan fari yayi appearing..
  Maida remote din tayi ta ajiye tana mai juyawa dan kai duban ta ga gadon..  
  Wani abin dariya sai ta ga hannun Ummitah na lalubar remote din daga cikin blanket da nufin kashe light din dakin..
  Dakatar da ita Ammah tayi ta hanyar dan daga murya tana fadin
  "Tashi ki zauna Noory ina da magana da ke"..daga cikin blanket din ne ta ji gaban ta ya fadi dan har sai da kan ta ya buga ta ji wani tsoro ya kama ta sai ta hau nanata addu'ar Allahumma ajirni fi musibati wa akhlifni khairan minha..
Fitowa tayi daga cikin blanket din idanun ta duk sun sauya launi sakamakon kukan da ta saka kan ta yi na dole da shi kadai ne option din da take jin zai magance mata matsalar ta at this very moment.
  Ammah na zaune a gefen royal bed din nata tana kallon facial reaction din ta dan samo wasu amsoshin tambayoyin da take son yi mata..

  Zama tayi jikin ta duk a sanyaye tana mai yin kasa da kan ta dan kar Ammah ta gane damuwar da take ciki,sai dai kash,ta makaro dan tuni Ammah ta gama fahimtar kuka tayi mai sosai...
  Kasa furta komai tayi sai kan ta dake duke a kasa tana ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi..
  Ido Ammah ta bi ta da shi tana nazarin yanayin ta,kusan 5minutes silence ne ya wakana a dakin kafin Ammah ta fara magana..
  "Noory...,me ke faruwa ne?me ke damin ki?wani abin ne ke damin ki a zuciyar ki da baki son in sani"?shiru tayi tana sauraron mahaifiyar nata gaban ta na fadi...
  Ganin yanayin ta ba lalle bane ta amsa mata tambayoyin ta ba sai ta cigaba da jefo mata tambayoyin..
  "Noory wai ko dai dama ba da niya kika zo mana ba ne?ina a matsayin mahaifiyar ki uwa a gare ki da nake ganin duk yawan mutanin duniyar nan bana jin akwai wacce ta san ki ta kuma fahimce ki sama da ni haka kuma ni kadai na cancanci sanin matsalar ki amma sam tun jiya da kuka iso garin nan Noory walwalar ki ragagge ne,kwata kwata ba ki sakin jikin ki kamar ba gidan ku kika zo ba?shin ko ni ce na bata maki baki son sanar da ni"?saurin dago kai Ummitah tayi tana riko hannun mahaifiyar nata tana girgiza kai..
  "Ammah ba a halicci diyar da zata dube ki ta kara ta ce baki cancanci sanin matsalar ta a matsayin ki na mahaifiyar ta ba..,Ammah ki yafe ni ba dan hali da dabi'u na ba...,,Ammah.....ina....,ina....huh...Ammah ki yafe min but i don't think am ready for this,i can't lie to you as well but...,ki yafe min Ammah bana jin zan iya fada maki damuwa ta a yanzu"..kuka ne ya ci karfin ta har ta kasa karasa maganar nata ta fada jikin mahaifiyar ta ta cigaba da yi so heart touching...
  Rasa abin yi Ammah tayi sai kawai ta ji kamar ta kasa ne a matsayin ta na uwa a ce diyar da ta haifa ta raina ta aurar da kan ta tana da damuwa amma ta kasa sanar da ita matsalar ta kuma ta fadi mata akwai matsalar amma bayyana mata shi ne dai ba zata iya yi ba...
  Tuni hankalin Ammah ya tashi ta ji kamar itama tayi kukan amma ta danne nata hawayen daga fitowa ta hau rarrashin diyar nata da bata kalaman saisaita zuciya da rage radadi..
  "Noory i believe in you,na san ko mu jima ko mu dade watan watarana zaki fada min kuma na san ba zaki boye min abin da zai cutar da ke ba haka ba zaki so rai na ya baci ba dan haka na baki space din da kike bukata kuma ba zan takura ki sai kin fada min ba but always remember that my shoulders are always ready for your Heartfelt disclosure"..wani irin tausayin mahaifiyar nata ne ya kuma kama ta sai ta ji duk duniyar nan babu wacce take tsananin kauna da muradin kasancewa tare da ita a duk fadin duniyar nan sama da mahaifiyar ta abim alfaharin ta mabudin rayuwar ta cikin duniya...

TAMBARI[The dark hunt] Where stories live. Discover now