WATTPAD @SIYAMAIBRAHIM
Mental stability:Illusion is an involuntary perception in which a transformation of real object take place.
This page is all urs Matar Manaja tnx alot i really luv ur comments.
31.Innocent.
Ana zazzaune ana jiran zuwan alƙali de accused client which is definitely Ummitah,Hajiya Sifa'u na ta saka fuskar tausayi tana ta shan kamshi a gefe daya dan ta san da irin kwararren lauyan da ta dauko ko wacece Noor sai ta batar da ita a wannan shari'ar.
Kimanin mintuna ashirin sai alkali ya shigo a tare aka tashi aka bashi girman sa sai da ya zauna sannan kowa ya koma ya zauna ana jiran jin rahoto..
Duk masu media press sun takarkare sun taro kwazon su da basirar su wurin ganin sun kwaso ingantattun rahotanni da ba a saba daukar irin sa ba because it is a very special case..
Karanta jawabi aka yi hade da presenting ma alkali case din dake cikin wani takarda cikin board..
Bayan kalle kalle da dube dube sai alkali ya bada damar presenting alkalan two opponent din inda Barrister Mika'il Sa'id Tagwaye yayi mike yayi introducing kan sa a matsayin lauya mai kare wanda yayi kara wato wanda aka kashe,bayan zaman sa sai Barrister Imran Yarima Majidadi ya mike yayi bayanin kan sa a matsayin lauya mai kare wanda aka yi karar ta wato accused client..
Wasu karance karance alkalin yayi for a moment sannan ya bada damar a shigo da accused client..
Jim kadan aka shigo da Ummitah dake sanye da wannan hijabin nata,kan ta a kasa dan har jiri take jin yana debar ta sakamakon yawan mutanin da ta gani a fitowar ta na farko..
Ana fitowa da ita Fadilah ta ji wasu hawaye masu dumi na gangaro mata sai ta saka hannu ta goge da sauri dan bata so zuciyar ta ya karaya..
An kai ta inda ya dace a kai ta ta tsaya sai alkali ya bada izinin a kawo mai karar accused client which was a blast because ba karamin scene Hajiya Sifa'u tayi creating ba daga tashin ta daga kujerar da take zaune har zuwa kan matakalar da ya sada ta da inda zata tsaya..
Da yawan mutani sun tausaya mata sun ji mata zafi dan sun san a yanzu abin ke kara shigar ta da aka dauko mata maganar mutuwar dan nata...
Sai bayan ta tsaya an tabbatar ta natsu sannan alkali ya ba Barrister Mika'il Sa'id Tagwaye damar koro bayanin inda a nan ya zayyane komai bai rage ba game da mutuwar,yana jawabi alkali na rubutu har ya kammala sannan aka ba Barrister Imran Yarima Majidadi damar yin nasa bayanin shima yayi bayanin similar to na abokin aikin sa sai dai bambancin ra'ayoyi a karshen bayanin sa na rashin yarda a ba client din sa laifin da ake tuhumar ta..
Bayan wasu rubuce rubuce alkali ya kalli Hajiya Sifa'u sannan ya tambaye ta ko tana da abinda zata kara bayan bayanin da lauyan ta yayi nan ta gyada kai aka bata dama ta hau koro bayani kamar haka.
"Your honour,wannan yarinya da kake gani ba a matsayin suruka na dauke ta ba a matsayin ya na dauke ta yar da nake ganin na isa da ita kuma zan iya saka ta in kuma hana ta yin abu kuma ta hanu,your honour,i have never been selfish to her all through her stay under my control as a mother sai dai abin da ta daukarwa kan ta ya san na rinka jan hankalin ta akan ta daina biyewa duniya ta saki jikin ta,ni a nawa tunanin so da kauna ce duk ta kawo hakan ban sani ba ashe bata so ashe kullum in na mata wannan maganar azabtar min da da take yi silently akan laifin da ba shi yayi sa ba ni da nayi fadar bata hukunta ni sai da na,your honour a duniyar nan baki daya ban da wani farinciki da abin alfahari sama da da na,duk wani so da kaunar da zan mai ai ba zai taba nunawa duniya ina mai su ba sai ya mallaki nasa yayan ni kuma na sami jikoki,toh a kullum tun bayan auren su da shekara daya da na lura bata da komai na kira ta na mata fadar in ma shi ke hana ta daukar cikin kar ta yarda ta biye mai shi namiji ne in ya so yana iya auren wata matar ta haifar mai yara da yawa ita kuma ya gama cutar ta amma bata taba ji ba,har sai da na kira na tambaye sa da kai na ya min nuni da shi bai hana ta ba sai dai in ita ce ke yiwa kan ta wani abin,toh fah tun daga lokaci sai in rinka kiran ta ina mata nasihar daina yin abin da take yi a boye amma ashe da na take azabtarwa a duk lokacin da na mata wannan maganar,your honour bana jin ina iya zayyane maka irin rayuwar musgunawar da yarinyar nan ta rinka dandanawa da na all i know shine countless times without number ta sha tabbatar mai da cewa sai ta ga bayan sa in har yayi mata abin da bata so,your honour i was away and was called to be informed that my only son has been murdered by who?by this lady all because ina mata fadar haihuwa shikenan sai ta zabi raba sa da duniyar nan instead ta fito karara ta nuna min son shi ne bata yi ai da sai a rabu cikin lafiya tunda ita kan ta ta san tana da bakin Tambari a rayuwar ta amma da na ya aure ta ni na yarda da auren kuma nayi welcoming nata amma sai ta saka min ta hanyar zana min Tambari mai muni a rayuwa ta,your honour this is not fair is not just this serves as a _darka hunt_ in my life please fight for my justice your honour"...!ta ida tana kukan fitan hankali..
YOU ARE READING
TAMBARI[The dark hunt]
HumorPeople round the world are being taunted and looked down on due to the feeling of misery and low self worth that is caused as a result of direct and indirect factors which gradually leads to so many social negligence and harassment in many situation...