WATTPAD @SIYAMAIBRAHIM
Mental stability:Puerperal Psychosis is a mental disorder in women which is characterized by lost of mindset,lost of contact with reality and vague behaviour .
20.Lost
6:45pm
Daidai exact time din da suka turo kan motar su zuwa cikin farfajiyar gidan kenan,.
Karar kashe motar yayi daidai da fitowar Saudat daga part din su,wacce niyar ta shine ta kai abincin dare da tayi zuwa part din mother in-law din ta..
Da fitowar ta kawai sai tayi kicibis da motar,bata gama gasgatawa ba ta ga fitowar auta Farmanullah daga baya sai mijin ta ya bayyana...
Kasa cigaba da tsayuwar tayi sai ta tako har gaban su ta ja ta tsaya tana kallon sa dan Farman ya juya kwaso masu kayan su zuwa cikin gidan..
Tana ta kallon shi har sai da muryar Farman ya fargar da ita.
"Aunty da fatar mun same ku lafiya dai"!?cikin murna da farinciki ta amsa mai hade da tambayar su ya hanya,bata amsa yayi shima yana mai jan jakar yayan shi zuwa part din su..
Kallon kallo suka koma exchanging a tsakanin su,ita kallon kewar sa take mai yayin da shi kuma yake mata kallon tausayi da kauna dan har a fuskar ta damuwar ta ya nuna..
Gyaran murya yayi yana mai kawar da kan sa gefe kamar ba shi ya gama yi mata kallon kuril ba da tausayi..
Ganin haka sai itama ta dawo reality ta hau inda inda tana harhada magana har dai tayi nasarar gaida shi da yi mai ya hanya.
Dan jan aji yayi kafin ya amsa ta yana wani daddaure fuska ita dai ko a jikin ta,kwaao sauran kayan tayi bayan ta mika mai tray din abincin a hannun sa tana mai fadin
"Dama part din su Hajiya zan tafi but bari in karasa shigar maka da kayan in ya so in na fito sai in kai mata"..kallon tausayi ya bi ta da shi daga bisani ya matsa ya jingina da motar yana kallon ta har ta wuce sannan ya dawo da hankalin sa ga kulolin abincin da suke guda biyu masu dan girma..
Kada kan sa yayi tunowa da irin matar da Allah ya bashi mai son shi da iyayen shi...
Farman ne ya zo ya wuce gaban sa yana fadin.
"Yaya na karasa ciki wanka zan yi jiki na duk zafi yake min".gyada mai kai kawai yayi alamar ya ji.
Yana nan tsaye ta fito da fara'ar ta wanda ya san duk dalilin dawowar sa ne ya sa take wannan nishadin...
"Kawo mu tafi ka gaida su Hajiya,dazu take ta kiran ka amma baya shiga hankalin ta ya tashi".jin haka sai yayi saurin kallon ta dan ya san har da ita kan ta nata hankalin ya tashi sai dai bata furta ba.
Tana gaba yana baya haka suka zo sashen iyayen sa inda a nan Hajiyar su ta rinka yi mai barka da dawowa dan ta tsorata matuka ganin layin shi bai shiga ba kuma mahaifin shi har dazu din bai dawo ba...
Bai jima ba yayi sauri ya koma part din su,gyara zama Saudat zata yi sai Hajiyar ta dakatar da ita game da ce mata
"Na yafe zaman yar nan,wuce ki ga mijin ki ku har yanzu baku da wayo,tun jiya miji baya nan ya dawo ysu kuma wai baki san ki je ki masa tarba ta musamman ba"..
Kasa Saudat tayi da kan ta tana murmushi hade da tashi a hankali ta fita ta bar sashen zuwa nasu..
Ko da ta iso nasu sashen har yayi pulling kayan sa ya shiga toilet dan taking warm shower..
Saurin fito mai da kayan da zai saka tayi ta ajiye mai sannan ta kara gyara little bit squeezed bed sheet din sannan ta kuma kara sandal wood din dake dakin cikin electric burner dan dakin ya kara kamshi mai armashi..
Fita tayi ta harhado mai abincin sa ta jere su a parlor nan ma ta sake kara turaren kamshi sannan ta dawo ciki.
Ganin sa tayi har ya fito daga wankar da ya shiga ya ma saka suturar da ta fitar mai da shi hakan ya mata dadi ba kadan ba ganin ya yaba zabin ta..
Tsaye tayi tana jiran ganin abin da zai yi,kan ta a kasa gaban ta na fadi kamar ba mijin ta ba,sanin halin ta na saurin bada kan ta laifi sai shi ya kawo kan sa gare ta cikin sanyin jiki..
Yana zuwa gab da ita ya kawo hannun sa ya janyo nata hannun yana kallon ta,still kan ta a kasa bata dago ba sai ya saka tafukan hannun sa ya dago fuskar ta bai jira ta ba ya saka idanun sa cikin nata hade da sakar mata murmushin da ta jima bata gani ba daga gare sa..
Ba tambayar da tayi zaton zai yi mata ya mata ba wata tambayar dabn ya mata mai kama da tambaya..
"Kin ba Mariam gift din ta da zan bata ne"?kallon kwayar idanun sa tayi sannan ta gyada mai kai,sai ya lumshe idanun sa yana kara jin tausayin ta kafin ya ce da ita
"Zan tafi masallaci me zan samu na tanadin da aka min in na dawo"?takaitacciyar dariya ce ta kufce mata jin tambayar da ya mata dan ta san abinci yake nufi because shi kam baya wasa da cikin shi..
Shima dariyar ce ta kufce mai yayi ta yar kadan yana mai sakin fuskar ta hade da yi mata sai ya dawo..
Ba karamin annashuwa Saudat ta tsinci kan ta a ciki ba ganin addu'ar ta ya karbu hankalin mijin ta ya fara dawowa gare ta..
Harkokin ta ta cigaba da yi cikin jin dadi da farinciki kamar bata dade cikin bakin ciki ba...
YOU ARE READING
TAMBARI[The dark hunt]
HumorPeople round the world are being taunted and looked down on due to the feeling of misery and low self worth that is caused as a result of direct and indirect factors which gradually leads to so many social negligence and harassment in many situation...