Throw back I

406 60 2
                                    

WATTPAD @SIYAMAIBRAHIM

Mental stability:Selective Autism is a condition in which a person who is normally capable of speech is unable to speak in certain situations.

7.Throw back I

FADILAH'S HISTORY..

Fadilah Sabitu Umar,shine asalin sunan ta haifaffiyar garin gombe ce cikin yankin Yemaltu Deba a yaren Tera,haka ta kasance diya ta hudu a zuri'ar Alhaji Sabitu Umar mai hula..
  Hajiya Aziza Sabitu Umar mai hula ita ce mahaifiyar Fadilah,kuma ita ce mace ta biyu a wun mahaaifin Fadilah..
Allah ya azurta ta da yara dai dai har hudu kasancewar uwargidan Alhaji Sabitu Umar mai hula Allah bai albarkace ta da arzikin yaya ba kusan shekaru ashirin da biyar da auren su,wannan dalili ya sa Alhaji Sabitu mai hula tuntubar uwargidan nasa mai suna Hajiya Safinatu akan ta bashi shawarar abin da ya dace sakamakon kun ji kun ji da yan uwan sa ke yi akan ta na ta zama juya bata haihuwa..
  Da fari shawarar kara aure ta ba shi amma sai ya tubure dan haka ta rabu da shi har lokacin da abin yayi tsamari duk da kuwa akwai alaka ta jini tsakanin Alhaji Sabitu mai hula da uwargidan sa Hajiya Safinatu dan mahaifin Alhaji Sabitu mai hula da mahaifin Hajiya Safinatu uwa da uba daya ne a inda mahaifin Alhaji Sabitu mai hula ya kasance babba sai mahaifin Hajiya Safinatu mai bi mai,dama iyakan su kenan su biyu,ganin basu da wani yawa su biyu ne kadai sai suka yi shawarar me zai hana su hada yayan au aure in Allah ya nufa sun haifi mabambantan jinsi wato mace da namiji,.
Sana'ar hula shine ainihin hanyar arzikin su dan a cikin ta suka taso wato shi sana'ar hular dan haka sai suka gada duk da a zamanin su akwai boko sukan hada da karatun bokon sannan in sun dawo su tafi kasuwa wun sana'ar iyayen nasu..
  A haka dai har mahaifin Alhaji Sabitu mai hula da mahaifin Hajiya Safinatu suka kai munzalin aure aka masu auren gida duk dai cikin dangin abokan mahaifin su kuma a nan cikin gomben suke kuma suke rayuwar su...
  Da yake sun sami ilimin zamani sai suka bunkasa nasu kaauwancin suka koyo sabbin samfurin sarrafa hulluna irin na zamani..
  A haka dai har Allah ya azurta mahaifin Alhaji Sabitu mai hula da samin karuwar shi Alhaji Sabitun a inda bayan kamar shekaru tara shima kanin mahaifin Alhaji Sabitu mai hula ya sani karuwar diya mace a inda aka saka mata suna Safinatu..
  Tun daga kan su ba a kuma haihuwa ba sai bayan shekaru da dama inda aka masu kanne bibbiyu,biyu maza biyu mata inda aka sami mix genders a each family..
  Tun suna yaran iyayen suka dage dan ganin sun shaku da juna kuma kaunar dangantakar jinin su ya fadada fiye da mere blood bond,hakan ya faru dan suna girma suna dada wayo hade da karatu shakuwar su na karfafa...
  Da yardar Allah duk suka sami ingancin rayuwa sun sami karatun boko da na arabi daidai gwargwado dan har sai da Alhaji Sabitu Umar mai hula ya kai matakin karatun degree a fannin kasuwanci a Gombe State University a GMB ita kuma kanwar sa Hajiya Safinatu tayi attending wani state polytechnic a Bajoga Funakaye inda ta karanci Mass com..
  Gata iyayen nasu suka masu bayan kammala karatun nasu aka samar masu abin dogaro da kai dan shi Alhaji Sabitu mai hula ya kwana biyu da fara kasuwamcin sa a babbar shagon da mahaifin sa ya bude masa kuma alhamdulillah komai na tafiya yadda ya kamata haka bayan kammala karatun Hajiya Safinatu itama aka nemo mata aiki a wani gidan radio ta kama aiki...

Ba jimawa aka fito da batun aure hade da saka lokaci kankani,wata biyu aka masu aure kuma yayi daidai da lokacin tafiya aikin hajji dan haka bayan bikin nasu suka tafi aikin hajji..
  Rayuwar su na kan tafiya yana nasa kaauwancin tana nata aikin,abu kamar wasa tun ana saka rai har abin ya faskara ya kai an fara cece ku ce akan rashin haihuwar Hajiya Safinatu dan haka mahaifiyar ta ta rinka bata hakuri akan ta toshe kunnuwan ta ta rufe idanun ta wataran in da rai da rabo Allah sai ya albarkace ta da karuwar..
Toh tun bayan wannan ba a kuma tayar da zancen ba sai bayan wasu shekaru kannen shi Alhaji Sabitu suka kuma taso ta gaba yaran da take ganin su kamar nata kannen amma haka shi namijin da yake karatu a uni da ita kanwar sa da aka ma auren wuri dan tana kammala secondary school aka mata aure sai a gidan mijin ta cugaba toh ita Allah ya bata yaya biyu,haka suke haduwa su zazzagawa Hajiya Safinatu buhun rashin mutuncin su sai dai tayi kuka..
  Ko mijin nata yayi fada a banza dan bayan kwana biyu sai sun dawo kuma ba daga wun kowa suke samin goyon baya ba sai daga wun mahaifiyar su dan ita ma wai ta gaji so take ta ga jikokin ta,duk wasu dangantaka da alakar dake tsakanin su ta saka kafa ta shure haka yanuwan ta na gidan iyayen ta suka taso Hajiya Safinatu a gaba akan lallai lallai ko ta haihu ko bar musu kurwar da ya kara aure...
  Duk wannan abin bai taba bata ma Hajiya Safinatu rai ba irin na ranar da suka mata gorin haihuwa sannan suka dora da yi mata lakanin mayya mai hana cigaban arziki..
  Wannan dalili ya sa da ya zo mata batun shawarar da yake nema daga gare ta bata yi nauyin baki ba ta ce mai ya kara aure,toh ko da ya ki yarda daga baya haka ta bi sa tana ta kuka da rokon sa akan ya yarda yayi ko zata sami sassaucin bakin cikin da take kwasa a wun yanuwan sa tunda su kan su iyaye mazan sun yi maganar har sun gaji amma kamar shan ruwa haka mahaifiyar Alhaji Sabitu zata murzawa idanun ta toka akan ita dai haihuwa take son dan ta yayi jikoki take son gani...

TAMBARI[The dark hunt] Where stories live. Discover now