WATTPAD @SIYAMAIBRAHIM
Mental stability:Tic Disorder is a sudden rapid,recurrent non rhythmic motor movement or vocalisation. it has it's onset in childhood but may persist into adulthood.
36.Freedom.
Supreme court AbujaHajiya Sifa'u ce hakimce kan kujera tana ta girgiza kafa tana karkada kai ba komai ke mata yawo a kai ba sai ganin inda take inda ta san haduwar dangi za a mata for sure but tayi rantsuwa muddin ba a mata yadda take so ba toh bata da option sam da ta je ta tsine masu a gaban gawarwakin ancestors din su..
Tana nan zaune Barrister Imran Yarima Majidadi ya shigo daga baya Barrister Saima Aliyu ma ta shigo,bin su da wani irin kallon banza ta yi ta kawar da kan ta ta cigaba da karkada kafa tana kallon kujerun manyan alkalan da su zasu bada judgment wadanda kwata kwata kujerun biyar ne and currently akwai mutani hudu saura daya,addu'ar kar dayan da take gudu ya zo dan an sanar da ita ai ba zai sami damar zuwa ba because baya kasar gabadaya wannan dalili ya sa ta dan sami kwarin gwiwar zuwa..
Babban kotu ne dan haka yake nan shiru kamar babu creatures a cikin sa but cike yake da jama'a kowa da nasa matsalar..
Shigowa da Ummitah da aka yi ya sa Hajiya Sifa'u kare mata kallo dan son ganin me ta taka da har ta iya nasarar kashe mata da,sai dai bata sami komai ba as ana shigowa da Ummitah aka kai ta standing box din da ya dace da ita sai wani mutum ya biyo bayan ta..
Wani irin zabura Hajiya Sifa'u tayi ta mike tsaye tana zazzaro idanun ta tana jin wani sabon al'amari tuni zufa ya gauraye mata jiki ta ji duk air split dake court din bai mata ba zafin nata yayi yawa..
Har mutumin nan ya zo ya wuce mutani na tsaye ko kallon gefe bai yi fuska ba rahama babu walwala babu wasa babu raha ya je ya zauna a kujerar da yake empty tun dazu sai a sannan mutani suka zazzauna suma..
The giant and elegant chief Justice Sulaiman Abdullahi Mai Sa'a kenan wanda ko babba tsoron haduwa da shi yake bare yaro da in ya hade mai rai sai dai a gan sa yana peeing a tsaye saboda tsabar firgita,baya daukar wargi baya wasa da aikin sa babu abinda ya shafe shi da millions of naira da ka yi spending dan kawo kara court din da yake ka ce sai dai ya maka yadda kake so dan bai san wannan ba,the only language he understand is _"Justice"_ and nothing other than that...Barrister Imran da Barrister Saima kallon juna suka yi suka kalli Hajiya Sifa'u hade da yi mata wani irin wicked smile sai suka dauke kan su ita kam dama a firgice take sai ta rasa ina zata saka kan ta dan samin sassauci..
Hikimar yin salati ko addu'a a zuciyar ta duk dauke mata yayi sai ta rinka girgiza kai cikin jimami da alhini alamar abin ya shammace ta...
Tana zaune tana wannan hali sai ta ji kamshin turare ya ratsa ta,dago kan ta tayi tana kallon wacce ta wuce ta din,ai tana ganin matar cikin ta ya duri ruwa ta kalli matar nan ta kara ta kalli daya budurwar da take tare da matar ta juya ta kalli alkalin da har yanzu ko sassaucin rai babu shi a fuskar sa sai kawai ta ji kamar ta kurma ihu a kotun ta je kawai ta kashe Ummitah in ya so bayan ta yi hakan itama a daure ta dan ta san babu wanda ya isa ya saka ta cin nasarar case din nan yau...Kujerar dake gaba da nata kadan matar nan ta zauna ita da budurwar sai da suka zauna suna kallon accused client din wannan budurwar tayi whispering da
"Aunty Ummi"!!take Ummitah ta ji sautin muryar a brain din ta dan kotun is so silent babu karar komai dan haka in ma magana mutum yayi yana iya jin echo din maganar...
Dago kai Ummitah tayi ta sauke a fuskar wacce ta kira sunan ta,take hawaye ya cike mata ido sai ta kawar da idon ta daga nan ta maida kan daya matar,she can't withstand it sai hawayen ya hau zubowa daga idanun ta,matar ce ta girgiza mata kai dan tunda aka fara wannan case din tun bayan ranar da ta bada asalin labarin zamantakewar auren ta da Asim da tayi kuka bata kuma yin kuka publicly haka ba sai yau wanda kukan nata mai dalili ne..
Duk wannan abin idanun Hajiya Sifa'u na kan su tana kallon su tana ayyana abubuwa daban daban a zuciyar ta..
Jin wani murya mai kama da broken drum very strict and tough mai razana zuciya ya sa Ummitah Juyowa da sauri..
Idanun ta ne suka mata gamo da sai da ta kasa yin silent cry ta fiddo shi waje tana yi sosai..
Murya ciki ciki dan kalmar nata bai fito ba iya movement din lips din ta ne zai tabbatar da magana tayi ta ce
"Abba na"!!idanun ta na kan shi dai dai ya sauke nashi idon a kan ta yana kallon ta fuska a murtuke idanun sa kamar na mai jin bacci wanda hakan ya bayyana ne sakamakon bacin rai da radadin da zuciyar sa ke masa,kuma a kullum in har ya zo kotu bada judgment irin haka idanun sa suka juye haka toh baya dadewa da yayi glancing sauran alkalan ma suka yi glancing kawai bayar da judgment yake yi ya tashi ko ka ki ko ka so an gama sai dai ka koma ka yi ta Allah ya isar ka da ba zai bi kowa ba sai kai...
YOU ARE READING
TAMBARI[The dark hunt]
HumorPeople round the world are being taunted and looked down on due to the feeling of misery and low self worth that is caused as a result of direct and indirect factors which gradually leads to so many social negligence and harassment in many situation...