Imposter original page

375 60 0
                                    

WATTPAD @SIYAMAIBRAHIM

Mental stability:Jamaisvu is an illusion of unfamiliarity which occur in people with temporal lobe epilepsy and exhaustion.

6.Imposter

   Tun da ta ji shiru sai tayi concluding cewa he is gone dan haka ta hada bayan ta da kofar ta hau rusa kuka ita dai a iya sanin ta ba auren dole ko na kiyayya suka yi ba ita da Asim amma bata san yadda aka yi ya rikide ya zamo ainihin imposter haka marar tausayi da imani ba...
  Ko da za a ce mata Asim zai gwada yiwa wata mace ba ma ita ba kwatankwacin abin nan da yake mata ba zata yarda ba but yau ita ce bolar sa da in ya kwasa sharar sa akan ta zai zo ya dire sa haka mahaifiyar sa duk masifa da fitinar ta akan ta ake sauke sa...
  Tayi auren soyayya but yanzu zama babu auren shi ya fiye mata a'ala dan wannan aure bata ga amfanin sa sai illar sa,ita ce jaka tunkiya da ta zamo abin dukar Asim ita ce abin hutun Asim dan irin yadda yake performing matrimonial relationship da ita ko mistress din sa ce wadda babu aure bare mutunci a tsakanin su sai haka,kawai shi dan tsantsar ya kuntata mata yake mata wannan abubuwan ba damar tayi magana sai ya ce ai haihuwa yake so tayi dan mahaifiyar sa na bukatan jikoki kuma ta ce in bata haihu ba toh sai dai ya rabu da ita shi kuma ba so yake ya rabu da ita ba...
  Tana nan zaune shiru tana whipping silently hade da zubda hawaye mai ciwo sakamakon tunowa da ta yi da rayuwar su a baya shekaru kusan shida da suka wuce wanda da za a ce mata wannan ranaku zasu zo toh zata musanta...
  From no where kawai ta ji an bankado kofar dakin an hau ta da duka ba kakkautawa kamar dai jaka,tun tana ihun da karfin ta har karfin nata ya kare ta shiga kakkare kan ta dama ba gama warwarewa tayi ba toh ga wani sabon lalurar da aka kara bisa kan na da...
  Ko da ya tabbatar ya mata lilis sai yayi wurgi da skin leather belt din da ya gama tarwatsewa a jikin ta ya zauna kusa da ita yana kashe mata warning..
  "Bari ki ji in fada maki Ummitah ba zan dau raini da rashin da'a daga wun kowa ba musamman daga gare ki da na san a karkashi na kike,saboda ina sake maki ido ya sa jiya kika kalli kwayar idanu na kika yarfa min maganganu son ran ki irin ga galabon namiji da bai san darajar kan sa ba,oh ban ga laifin ki ba,bayan kin tafi gidan wannan kawar taki da bata san darajar nata auren ba sai kika koyo sabbin sigogin fitsara da tijara ko?ni kike ce mawa in tafi ba zaki biyo ni ba uhum?magana nake maki kin min shiru kamar kurma"!!haka ya daka mata tsawar da ya firgita ta..
Jiki na bari idon ta baya gani sosai ta durkusa ta hau bashi hakuri dan ko ta bayar ko kar ta bayar anjima sai ya kuma bugun nata sannan yayi forcing nata into accepting his desired wish,toh saukin daya, in ta dage da rokon kamar wani ubangijin ta toh zata sami sassaucin bugun anjiman...
  Yi yayi kamar bai san an halicci mutum a wurin ba haka kamar da dutse take maganar har ta cire tsammani sannan ya mike a zuciye a fita ya bar mata dakin ta cigaba da kukan...
 
  Kimanin awa guda bai dawo dakin ba sai ta ji karar sautin wayar ta dake cikin jakar ta dan haka ta kai hannu ta bude zip din ta dauko wayar ta danna wun receive ba tare da ta duba kiran ko na waye ba murya na rawa tace..
"Hello"!daga daya bangaren aka amsa da
"Kawa ta ya kike"!?sai a sannan ta gano muryar na Fadilah ne dan haka kafin ta kuma mayar mata da amsa sai ta saisaita muryar ta sannan ta bata amsa
  "Lafiya kalau nake Lilah,ya na baro ku da fatan yara na duk suna nan lafiya"?tayi wannan hikimar tambayar ce dan kar Fadilah ta sako tambayar me ya same ta muryar ta na katsewa but da yake mai wayo ce kuma matar alkali ce sai ta dago akwai wata a kasa dan haka ta ce
  "Kawa ta har yaushe wai zaki cigaba da zama a irin wannan bakar rayuwa tare da wannan imposter din"?shiru ta mata kamar bata jin ta sai da ta dau lokaci sannan ta ce
  "Lilah ba fah komai kawai saboda ban yi bacci bane a jiya sai yau da safe kuma kin ga ban jima ba Asim ya zo muka taho toh yanzu din ma baccin na fara kiran ki ya tada ni"!!shiru itama Fadilar tayi dan ta san karya ce kawai aminiyar nata ta shimfida mata but sai tayi wata hikima ta hanyar canza topic of discussion din
  "Bikin Saima Aliyu sati mai zagayowa ne kuma na san kina sane da cewa a kullum tana counting akan mu akan ko babu wanda zai tafi bikin mu zamu tafi haka in kika yi la'akari da irin kusancin mu ya kamata a ce mu ne a gaba gaba a wun bikin nan dan haka ki zauna da shiri Zariya zai karbi bakuntar mu sannan daga nan zamu wuce gombe inda a nan zata zauna kin ga daga nan kema sai ki gana da yan uwa da abokan arziki dan nima in na tafi zan kai ziyara Yemaltu Deba dan na jima ban tafi ba haka zan kai yaran nan Shangom dan ganawa da kakannin su iyayen Imran kin ga tafiyar kusan duk tamu ce dan sada zumunci mai karfi za a yi da aka dade ba a yi kuma lada duk zamu samu,ya kika gani"?shiru tayi tana nazari...
  Ita wannan tafiyar ma duk kamar domin ta aka tsara sa dan har cikin zuciyar ta tana son tafiyar a kalla shekarun ta uku rabon ta da mahaifar ta wato gombe haka zalika ta shafe shekaru hudu rabon ta mahaifiyar ta wacce shekarar ta ta farko suka rabu ta bar nan garin ta koma gombe kuma babu izinin zuwa kai mata ziyara duba da irin circumstances da take facing a gidan mijin ta wato Asim..
Rasa abin fadi tayi sai karaf Fadilah ta karanci silence din ta dan haka ta furta shi a bayyane
  "Na san nazari kike yi akan yiwuwar tafiyar mu ko imposter din nan zai bar ki ko ba zai bar ki ba right"?gyada kai tayi kamar tana gaban ta sai tayi shiru bata ce komai ba..
  Babu jira Fadilah ta dora da cewa
"Kar ki damu ke dai kawai ki zamo cikin shirin ki tun yanzu in fact na gama booking mana beauty spa da zamu tafi ana saura kwana hudu to the wedding saboda washegari mu kama hanya in ya so sai mu yi meeting sauran shagulan bikin"!shiru dai tayi tana tunanin anya shi Asim din ne zai wani saurari wannan uziri nata har ya yarda ta tafi wani biki,bata jin zai amince kuma bata son sanar da aminiyar nata negative side na Asim din dan haka sai ta ce
  "Lilah bari in kwanta bacci nake ji anjima in na tashi zan sanar da ke yadda muka yi da shi kin ji"?jin ta kawai Fadilah tayi but bata wani yarda da ita ba dan haka ta ce
"Toh shikenan a tashi lafiya"!!daga haka suka yi sallama ta ajiye wayar ta yi kamar zata mike sai ta ji wani irin zafi a gefen jikin ta kafin ta ankara sai tashin ya gagare ta haka ta rinka mammatse ido tana cije baki ta rinka rarrafe har ta shige toilet ta zauna a kasa...
  Wani irin kuka mai cin rai ne ya taso mata wanda sai da tayi sa son ran ta sannan ta karasa rarrafawa ta isa bathtub ta hau cire kayan jikin ta sannan ta daga da kyar ta shige cikin empty bathtub din...
  Sai da ta share fin rabin awa a zaune sannan ta kunna double taps din ta saisaita ruwan  yayi mata daidai yadda take so sannan ta jingina kan ta da bangon bayan bathtub din ta lumshe idanun ta a haka bacci mai nauyi ya dauke ta...

★★★
  Tashin farko bata tsaya bata lokaci ba tayi necessary duties din ta na yau da kullum tana kallon sa bata tashe sa ba dan tun bayan sallar subhin da ya dawo ya kwanta tana jin sa saboda cikin dare ya farka yana son gabatar mata da nufin sa amma ta ce ai ita yau monthly visitor din ta ya zo mata haka ya koma ya kwanta shiru wanda ya san babu wani visitor tsantsar son ta wahal da shi ne sai ta dau wannan bangaren a matsayin punishment da take son basa...
  Karamin gyalen ta ta dauko ta zo da fuskar ta daidai nasa ta masa side kiss a kumatun sa ta tashi tayi fitar ta..
  Bata tsaya ko ina ba sai sashen In-laws din ta inda da shigar ta aka kwashe mata da dariya wanda kannen mijin nata ne dan ko a jiyan da ta dawo ta kawo karar sa suna zaune idanun ta rufe da kishi ta zazzage duk abin da ya faru sannan ta wuce toh a yanzu kuma sai suka tuno da yadda take fara'a kuma sun ji abin da tayi a daren jiya na kare sa da tayi ssi abin ya hadu ya basu dariya...
  Bata fuska tayi ta fara da karamin cikin sigar fada ta ce
  "Amanullah dama wai akwai wasa irin haka a tsakanin mu da kai"?sai yayi shiru amma still yana dariyar ciki ciki sai sauran ma suka gimtse dariyar tasu but akwai wata dake zaune kusa da Hajiyar gidan wacce kamar zasu zo sa'a da ita,ita ce ta ce
  "Wai ni kam ya aka yi kika bari yaran nan suka dau hanyar raina ki kamar ba matar babban yaya ba"!harara ta dalla mata dan ta san duk tsokanar ta suke yi dan haka ta hade rai ta wuce straight ga Hajiyar ta durkusa ta gaida ta,..
  "An tashi lafiya Saudat"!amsa mata tayi da lafiya kalau daga haka ta zauna ta daure fuska ita kar a ce mata dadi miji kuma ta san ko ya tayi sai mother-inlaw din nata tayi teasing nata kafin ta bar wurin..
  Wayar ta ta maida hankalin ta akai ta shiga daddanawa kasancewar yau sunday ne bata bude beauty saloon din nata sai monday dan haka a nan ta shagala ta kai kusan two hours tun tana ciccin magani da kannen mijin nata har dai ta sake ran ta wanda dama sun san haka take...

Yayin da take ta hirar ta a nan shi kuma yana can yana ta faman sharara bacci not knowing that yau babu mai tayar da shi dan basu good time da matar nasa..
  Ba shi ya farka ba sai 12 noon,da mike mai dauke da addu'ar tashi daga bacci ya diro daga gadon sai ya fara dube duben inda ta shige..
  Bai gan ta ba but ya samo amsar sa dan ya ji kamshin turarukan ta kenan har ta shirya ta wuce cikin gida ba tare da ta jira sa sun tafi tare kamar yadda suka saba ba...

  Ganin haka shima sai yayi wanka yayi nashi shirin cikin kaftan ya fito parlor yana mai gyara zaman hular sa,hango set of breakfast kit din sa yayi saman wani karamin mat dan haka ya karasa ya zauna ya bude,..
  Chips ne da egg sauce sai kunun shinkafa plain ba a hada komai ba,jijjiga kan sa yayi dan ganin fushin ta karara wato har abincin bai sami albarkar hadawa daga wun wacce ta girka ba shi kenan da kan sa yau zai hada...
  Haka ya hada ya ci ya sha ya koshi sannan ya tashi ya fito hade da janyo mata entrance door din ya nufi sashen iyayen sa dan kai masu gaisuwar safe a nasa tunanin...

  Da sallamar sa ya shiga sai ya hango ta kwance bisa kujera ita kadai tana danne danne babu kowa a parlorn dan haka yayi saurin karasowa ya zo gaban ta yana mai yin kasa da muryar sa ya ce
"Kika fito baki jira ni ba,babu gaisuwar safe babu kulawar ki gare ni baki damu da yanayin da zan farka ba kawai kika fito nan ya dace Saudat"?kallon sa tayi ta ce
  "Tambaya ta kake yi"!?sai yayi shiru,mikewa tayi daga kwancen da take ta gyara gyalen ta ta dau wayar ta ta wuce sa durkushe a wurin kan sa duk ya dau zafi shi dai bata taba mai fushi irin ta yau ba,da kamar ya cigaba da maintaining position din amma sai ya mike ya biyo bayan ta yan ta kiran sunan ta yana sauri....

#Jamaisvu usually occur to people with short memory capacity,despite the fact that one is familiar with someone,but due to disease condition or long hospitalization,the individual tends to forget so many things including his/her relatives,mostly a rehabilitation counselling is advisable in other to correct the perception of the individual's brain and memory.

TAMBARI[The dark hunt] Where stories live. Discover now