WATTPAD @SIYAMAIBRAHIM
Mental stability:Hysteria is a shifting of emotional conflict,its fear and anxiety,into Physical and mental symptoms this denote any activities that a person does in other to derive&/attract attention from others.
4.Perception
The kallamus residence
Cikin shigar mutunci da kamala ta doguwar riga wacce ta fi yin kama da kimono hade da yar cikin ta straight gown armless duk bakake ainihin exclusive classy black an ma kimono din kwalliyar duwatsu deem manya daga wuyar kimono din da ya bada v-shape har izuwa gaban rigar zuwa kasan hannayen sa ya ji duwatsu,kafar ta hill ce black as well as her veil haka wani karamin jakar dake rike a hannun ta wanda yake kamar purse,shi ma baki ne wanda hade yake da takalmin kafar ta na kamfanin Luis Vuitton,eye spec da ta saka duk black ne karshe ma perfs din ta class na black oud ne da,babu wasu much accessories a jikin ta dan bata cika aminci da su ba ta fi sabawa da wadannan da ta saka,fuskar dai ta sha ado an mata ainihin nude makeover sai dai babu artificial eye lashes din...
Haka ta fito daga bedroom din nata rike da key tana tafe tana yauki kamar dai tarwada..
Already yana jiran fitowar ta yana tsaye a tsakar parlor din yana saka links din rigar kaftan din sa da shima baki ne,..
Tsayawa yayi yana kare mata kallo dan fah mantawa yayi da abin da yake yi ya maida hankalin sa gare ta gabadaya kamar bai taba sanin ta ba abin sai ya zamo mai kamar a yau ya fara haduwa da ita...
Ita kam ganin da gaske ya rude ta ruda sa da adon ta sai ta sake sakankancewa tana tafiya kamar hawainiya,duk taku daya sai ta girgiza jikin ta haka ko ina a jikin nata sai ya san ta dogara kafar ta da kasa...
Tun da take takowar haka ya rinka kare mata kallo har ta zo daf da shi sannan ya ja numfashi sakamakon kamshin perfs din ta..
Saka hannun ta tayi ta hau gyara mai black zanna bukar dake kan sa tana yi tana murmushi dama ga spec din ya bala'in hawa kan fuskar ta sai abin ya bada wani irin ainihin kyau na daban...
So yake ya mata magana amma ya rasa dalilin da ya sa ya kasa ce mata ko da kalmar "a" ne wanda ya san ba wannan ne karo na farko da take kwalliya irin wannan ba amma kawai na yau din ya fita daban ne sakamakon nude makeover din da tayi ba tare da ta saka artificial beauty cosmetics da yawa ba...
Ganin da gaske so yake yayi magana amma maganar ta kalare masa sai tayi mai dariya cikin zuciyar hade da yin wani irin facial grimace hade da furta wani exciting sound
"Arhh"!!ankara yayi da abin da ya tsaya yi akan kallon beauty din ta dan tunda ya hadu da ita a haka take kullum tsaf tsaf ko bayan auren su babu abin da ya canza a yanzu auren su ya kai 4 good years but bata taba canzawa daga yadda ya san ta ba hasalima karuwa kwalliyar nata ke yi sakamakon tsananin kishin sa dake addabar ta kamar ta rinka lullube sa da nikabi in zai tafi wun sana'ar sa...
Jawo ta jikin sa yayi yana kallon ta daga kai zuwa kasa,abin bai mai ba dan haka ya saka hannun sa ya cire mata eye spec din ya saka kwayar idanun sa cikin nata suka sarke suna kallon juna,da abu yayi abu sai ya kawo lips din sa gab da nata da nufin hadewa ai ta ja baya tana fadin
"Oh ni Noorul qalbi yanzu yau munin nawa har ya wuce misali da ba a ko min gyaran in je in gyara wani wurin da bai yi ba?Allah ya baka hakuri"!!
Da yake a kullum in tayi kwalliyar zata fita sai ya tsaya ya yabe ta ya mata hotuna ba adadi sannan su yi selfie tare kafin duk su fita,toh a yau da ya tsaya kare mata kallon kuril sai ta tsokane sa dan ta san lallai ta gigita masa lissafi da safen nan shi yasa ta rinka abu kamar wata saint...
Murya a raunane da alamun bukatar wani abu ya ce
"Luv,am short of words,na rasa abin fadin,can you imagine"!?yar dariya tayi tana fadin
"Toh ni yau bari in fara yabon hala in nayi kai ka sami wasu lines sai ka hada naka rhyme din"da fara'a a saman fuskar ta ta hau yi mai kirari mai nuna tsantsar so da kaunar sa a zuciyar ta,kalaman kauna masu sanyaya zuciya da tsayawa a rai ta rinka rero mai har sai da ta dire da
"Miji na ina kishin ka,ina kaunar ka,ina son ka,son da ban san iyakar sa ba dan ni na san bana ma kai na kwatankwacin so da kaunar da nake maka,miji na ina maka fatan alkhairi a wun sana'ar ka Allah ya kare min kai daga sharrin abin ki ya bada nasara ya sa yadda ka tashi lafiya kake shirin fita lafiya rabbi ya dawo min da kai lafiya cikin walwala da farinciki"..lumshe idanun sa yayi yana digesting kalaman ta har ta gama kafin ya ce
"Saura daya addu'ar Luv"!murmushi tayi shima ya mayar mata da martani kafin ta ce
"Allah ya makantar min da idanun ka akan duk wata mace duk yarintar ta kuma duk tsufar ta,ya bude maka idanun ka akan sana'ar ka kawai"!!dan dariya suka yi at the same time sai ya dora da
"Ameen angle"!!muddin ya kiraye ta ko yayi addressing nata da wannan suna wato"(Angel)",toh ta san kalamai sun kauracewa brain din sadan haka angle replace all other words or poems or phrase da zai yi amfani da su dan kwada kwalliya da kyawun ta...
YOU ARE READING
TAMBARI[The dark hunt]
HumorPeople round the world are being taunted and looked down on due to the feeling of misery and low self worth that is caused as a result of direct and indirect factors which gradually leads to so many social negligence and harassment in many situation...