Ataxia

268 58 7
                                    

WATTPAD @SIYAMAIBRAHIM

Mental stability:Ataxia is seen as lack of coordination in an individual whenever a voluntary act is being carried out which is associated with brain displeasure.

41.Ataxia

Wayar dake hannun ta ta wullar saman kujera ta juyo da sauri ta nufi bedroom din su tana ta murna,bata gan sa ba sai ta karasa cikin bathroom din tana kiran sa da pet name da ta saba in tana nishadin ta..
  "Hero..where are you come out i got a news for you"!!fuskar sa rufe da kumfa ya bude baki yana ce mata yana zuwa..
  Abin ya bashi mamaki dan rabon su da walwala a gidan tun daren da ta daga mai hankali akan zancen Ummitah..

  Ba jimawa ya fito daure da towel a waist din sa yana kallon ta yayi da ta taso a guje ta fada jikin sa ta rungume sa tana fadada murmushin ta sai yayi hugging nata back yana mamaki..
  "Abba has been discharged yayi recovering completely"!ta fada da fara'a taf a muryar ta sai ya dago ta da fara'ar shima yana murmushi ya manna mata kiss a lips din ta yana mai kuma rungume ta tsam..

  Taya sa shiryawa tayi ta raka sa har wun bike din sa zai hau ya dakata ya juyo ya kalli ko ina ya ga ba kowa sai ya manna mata kiss a goshin ta yana fadin
  "In na dawo da wuri zamu tafi tarbar su Abba ASAP uhm!?ya dage mata gira daya sama alamar ta fahimta sai ta gyada mai kai daga haka ya sa kai ya fice..
  Komawa ciki tayi ta kira mahaifiyar ta a waya suka hau hira duk yadda Abban ta yayi recovering haka ta saka mahaifiyar ta fayyace mata har karshe, abin ya mata dadi ba kadan ba har ta kasa boye annashuwar ta ta sanar da mahaifiyar nata yau da kan su zasu zo tarbon su ita da mijin ta,daga haka suka yi sallama.
  Da farinciki yau Saudat ta yini a gidan ko da ta sanar da in-laws din ta suma sun mata murna sosai haka aka rinka addu'ar bayyanuwar asalin culprit din da yayi sanadin fadawar mahaifin ta wannan halin..

★★★
  Bayan wasu awanni Ammar ya dawo daga aikin sa yayi wanka ya sauya suturar sa,a motar Saudat suka fita tana ja suna hira har suka iso filin saukar jirgi ta Abuja,trip din 45 minutes daga suleja dan speedy drive ta rinka yi..

  Suna zauna a awaiting reception almost 35 minutes jirgin nasu ya sauko,kasa natsuwa Saudat tayi har sai da Ammar ya riko ta yana calming nata dan ya san bata da sukuni a yanzu har sai ta gana da iyayen ta musamman mahaifin ta..
Ko da ta hango su,raba jikin ta tayi da na Ammar ta karasa gare su..
  Seeing her father made her whoop silently dan condition din sa ana iya cewa alhamdulillah but ta san an mai lahani internally already wanda sai a hankali in da rai zai dawo daidai kan sa..
  Rungume sa tayi dan a kan wheel chair yake zaune sai ta hau kuka mai sauti har sai da Umman ta ta dago ta daga durkushen da take ta rungume ta tana rarrashin ta akan komai ya zo karshe tunda Abban nata bai rasu ba..

  Daga baya Ammar ya karaso ya zo ya masu barka da dawowa hade da yiwa father in-law din nasa fatar cigaba da samun lafiya ingantacciya..
  Da haka dai suka karasa mota aka taimakawa Ammar aka shigar da Ambassador Haris motar,Saudat kuma ta shiga gaba ita da mijin ta while mahaufiyar ta na baya suka ja zuwa gida dan trip din ma babu wanda ya san da dawowar su gudun makiya..

★★★

Hours after

Delicacy kala kala Saudat tayi presenting wa iyayen nata wanda har shi mijin mata bai san da su ba dan bai san ta yi su ba sai yanzu..
  Liyafar su suka yi daga su sai su sai Abba yayan Saudat da ya zo da matar sa da diyar su..
  Family dinner aka yi aka yi addu'ar kariya daga wasu sharrukan boye aka yi fatar alkhairi daga haka kowa ya fara komawa gida dan Abba ya tafi da matar sa haka mahaifiyar Saudat ta taimakawa Ambassador Haris suka haura zuwa dakin sa dan yakan taka saboda rage yawan zirga zirga ya sa aka bashi supporting chair..
  Sai Ammar ya kalli Saudat yana tambayar ta ko zata kwana a nan me,dama abinda take so kenan sai ta amsa mai da eh sai ya mata warmly goodnight ya sallami in-laws din nasa akan gobe Saudat zata dawo gida..
 
  Tun yana yana hanya yake hasashen abubuwa iri daban daban a ran sa,bai san ya zai fuskanci zuciyar sa ba aka alakar da take shirin kulla masa tsakanin sa da Ummitah,never for once has he ever dreamt of a day like this in his whole life..
  Ajiyar zuciya ya sauke ya dubi driver din gidan su Saudat da shi ke jan sa a motar Saudat din dan kawo sa gida ya ce mai..
  "Ka dan kara sauri dare na yi"!amsa da toh mai gida yayi sannan ya kara saurin gudun motar har dai suka dawo gidan lafiya kalau,shi Ammar ya shige yayin da drivern ya juya ya koma..

TAMBARI[The dark hunt] Where stories live. Discover now