Throw back IV

364 61 1
                                    

WATTPAD @SIYAMAIBRAHIM

Mental stability:Bipolar Affective Disorder(BAD),is a disorder characterized by mood swings from profound depression to extreme euphoria,with interval of normalcy.

10.Throw back IV

AMMARUDEEN KALLAMU

Ammarudeen Kallamu da ne na biyu ga Alhaji Kallamu da Hajiya Rashida wacce aka fi sani da Hajiya Fulani,..
Allah ya albarkaci zuri'ar Alhaji Kallamu da Hajiya Fulani da yaya dai dai har takwas wadanda suka kasance mix gender,uku mata biyar maza,..
Amiratul khairy ita ce babba sai Ammarudeen wanda ke bi mata daga shi sai Amatullah mai bi mata ita ce Mariam daga ita sai Amjad,sai Amanullah,sai Al'amin,sai auta Ahmad(Farmanullah)mai kimanin shekaru goma sha takwas yana gab da shiga 19years a duniya..
Ammarudeen ya kasance mutum mai son samin nasa na kan sa tun yarintar sa bai yarda da kwacewa yayar sa Amira abin da yake nata ba,duk da kasancewar sa namiji bai kasance mai rikici da raina yayar sa zamantowar ta mace ba,a kullum kusa cin su na karuwa da ninkimuwa because when he was 8 his sister was 13years tazarar na da dan yawa a tsakanin su,haka tazarar ta dan ja tsakanin sa da Amatullah wacce ta kasance four years ne a tsakanin ta da shi,..
Mahaifin su da mahaifiyar su sun kasance yan uwan juna ne auren dan mace da namiji aka masu da mahaifin Alhaji Kallamu da mahaifiyar Hajiya Fulani uwa daya uba daya ne,dan haka ko da suka haifi yaya sai kawai aka rinka yi masu sha'awar aure tare,toh ko da suka girma sai Allah ya hada jinin su ba tare da sun san cewa dama ana son hada su ba..
Da abin ya fito sarari sai iyayen nasu suka yi farinciki aka yi magana akan in Alhaji Kallamu ya karasa karatun su za'a yi bikin wanda a lokacin da zai kammala nasa karatun ita kuma Hajiya Fulani zata shiga aji na biyu a jami'a kenan..
  Tun asali kakannin su masu sana'ar sufurin kayayyaki ne su dauko daga wata jiha zuwa tasu jiyar,a haka har abin ya bunkasa ya koma sai su dauko kayan daga kasashen nan kusa da Nigeria kamar Togo,Congo,Somalia,Burkina Faso da dai black populace na wuraren kusa da Nigeria da dai za'a iya gudanar da sana'a mai karfi..
  A kan wannan turba Alhaji Kallamu ya taso ya ga mahaifin sa na yin nasa kasuwancin dan haka ya karkata akalar karatun sa zuwa ga karantar kasuwanci wato business,kuma a haka ya ci buri sosai kan ganin ya kawo cigaba sosai a gidan nasu ganin daga shi sai kanwar sa diyar babar sa wato Hajiya Fulani,su biyu kadai iyayen su suka haifa,shi shi kadai a gidan su haka itama ita kadai ce a gidan su,saboda haka sai shi Alhaji Kallamu ya dora mata son duniyar nan dan jinin shi ce haka matar da yake burin aura..
  Ita ma Hajiya Fulani abin da take karatawa kenan a jami'ar wato business wannan kuma ya biyo baya ne bayan zugin da shi yayan nata Alhaji Kallamu ya rinka yi mata akan su hadu su bunkasa arzikin family din su tunda iyakan su kenan su biyu,dan haka ko da mahaifiyar ta ke mata maganar ta karanci medicine ta tubure akan sam ita in ba business ba toh sai dai ta hakura,kasancewar ta tilo yar fari kuma auta sai iyayen nata suka bar ta suka yi supporting din ta in every way possible..
  Rayuwar su was good and smooth babu kiyayya ko tsangwama,time to time sukan kai ziyara ma kakannin nasu dake zaune a can garin su ta ainihi wato Taraba a yankin Sardauna...
  A kwana a tashi ga mai rai da lafiya babu wuya,Alhaji Kallamu ya yi nasarar kammala karatun sa ya fada sana'ar mahaifin sa da kakaninnin sa kuma yana jin dadin sana'ar nasa sakamakon yadda yake gudanar da sana'ar nasa ta tafarkin da ya dace saboda bokon da yayi mai zurfi fiye da mahaifin sa,abin ya karbe sa da haka ya dada fadada shagunan su cikin kasuwa ya kuma cigaba da fita yana kawo kaya ana zubawa a shagunan nasu..
  Abin ya karbe sa dan haka hankali kwance ya fara zuwa kasashen ketare irin su dubai,Italy da india yana kwaso kayayyaki masu kyau da farashin rahusa,sai ya kawo ya zuba a shagunan su a rinka saidawa a farashi mafi sauki hakan ya janyowa shagunan nasu kyakyawar suna da _Tambari_ mai kyau da alfahari..

A gefe daya kuma jiran kammala jarabawar Hajiya Fulani ake yi dan a fara ainihin gagarumin shirye shiryen bikin nasu ita da yayan nata,.
  Soyayyar su suke yi sosai kuma duk tafiyar da zai yi toh sai ya kawo mata tsaraba ta musamman da tsada hakan na kara masu dankon kaunar su..
Da Hajiya Fulani ta kammala jarabawar ta aka shiga hada hadar biki,abu ne ta naka maganin a kwabe ka tuwo na mai na,dan haka duk a gida ake ta yin shirye shiryen cikin dangi da yan uwa..
  Da biki ya zo aka yi shagulgula kala kala na al'ada da na zamani daidai gwargwado,aka yi biki lafiya rumui aka kai amarya gidan ta da ke dan nesa da na In-laws din ta,hakan ya faru ne sakamakon ra'ayin iyayen shi Alhaji Kallamu akan zamani ya zo da ya dace a bar yara su yi rayuwar su ta sure ba tare da idanu ko takurawar surukan su ba...

TAMBARI[The dark hunt] Where stories live. Discover now