Lonley Hearts

259 46 0
                                    

WATTPAD @SIYAMAIBRAHIM

Mental stability:Child Abuse and Neglect is any form of physical,sexual or emotional maltreatment of a child due to failure of  parents or other persons with the responsibility to produce needed food,clothing,shelter,medical care or supervision to the extent that the child's health,safety and wellbeing is threatened.

15.Lonely Hearts

"Noorul qalbi ni ka tashi..ka tashi ka ji da ni...yanzu shikenan dan Allah bai bani haihuwa da kai ba har yanzu shine wai ka fara kosawa da ni kana nuna min halin ko in kula tun shekaranjiya kake dauke min kai kake. Sha min kamshi har nemar mata kake yi a cikin gidan nan cikin daki na kan gado na Noorul qalbi ka kyauta min kenan?sannan ba ni ba ce da aka yiwa laifin ke fushi ba sai kai da kayi sanadin laifin"?..
  Duk surutan ta ya ji kuma ya san da gangar ta mai furucin wai yana neman mata a dakin ta a kan gadon ta duk dan ya tanka ta ne sai ta sako maganar da take da niyar sakowa tunda dai waya ta gan sa yana yi but ta juya maganar,wannan in wani na wurin sai yayi zaton da gaske matan ya kawo mata har dakin har gadon kamar yadda ta ce din..
  Ganin ya share ta ai kuwa ta saka kuka kamar marar hankali,ko kallon ta bai yi ba sai da ta ishe sa ya mike ran nan a hade kamar baya dariya,dama babu riga a jikin sa tun da yayi sallar subhi ya tashe ta ta yi bayan ya dawo daga masallaci dan kar ta ishe sa da magana shi yasa ya bari sai da ya dawo daga masjid din ya tashe ta,toh da zai kwanta sai ya cire jallabiyar ya kwanta haka nan babu riga sai dogon wando ash colour mai siffar sport wear..
  Mika yayi irin ta masu zuwa gym,ya wani share ta ya tashi yana kara yin wani mikar alamar kwalelen ki sannan ya wuce toilet...
  Zaune take but sai da jikin ta ya mutu ganin rashin hakurin ta ya janyo mata ita da mijin ta amma tana shakkar tunkarar sa bare ta rike ko da hannun sa ne har a kai ga ta hada jikin ta da nasa,dan yanzu ta san da zarar ta yi gigin zuwa kusa da shi kallo kadai in ya mata sai ta sha jinin jikin ta,tun da take da shi a rayuwar auren su sau daya ya taba bata irin wannan gwale gwalen kuma ta haukacen ta birkicen karshe danganawa tayi da mahaifiyar sa but still bai saurare ta ba sai da ya ji yin hakan on his own bayan weeks sannan ya shirya da ita lokacin da bata yi tsammani ba,kuma tun daga ranar har rana mai kamar ta yau bai sake yi mata wannan burgewar ba sai dai tana gani kamar abin da yake da niyar yi mata kenan kuma in hakan ne ita ta janyowa kan ta ruwan dafa kan ta indeed...
  Ko da wannan tunanin ya zo mata sam bata yi rawar kan zuwa kai kara ba tayi shiru tana addu'ar Allah ya sa kar ya birkice mata Allah ya sa ya sauko ya shirya da ita dan ba jin dadin zaman take yi ba tun shekaranjiya har yau mijin ka kuna kwana daki daya amma kun haramtawa kan ku junan ku akan me....
  Fuskar ta taf hawaye,har ya sauya launi dan ita din mai kyau ce kuma fara ce,but damuwar nan ya sa tayi kamar ba ita ba da take yar gayu da kwalisa ba...
  Tana nan zaune tana share hawayen ta sai ta ji budewar kofar sa,dago kan ta tayi ta juyo tana kallon sa,this time around ma babu wandon,towel yayi wrapping around his waist yana wani shassafa sajen fuskar sa da ya gyara da kan sa dan da duty din ta ne gyara mai fuska toh yau shi ya gyara kayan sa..
  Abin ya taba ta wato shi yana nuna mata ko a jikin sa fadar tasu gashi nan har gyaran fuska yayi,wani zuciyar ya hau ayyana mata ai tafiya wun masoyiyar tasa zai yi shi yasa yake gyaran fuska haka wani zuciyar kuma na ce mata toh tashi mana ki hana sa ai kina da right,take kan ta ya dauki zafi ta kasa aiwatar da komai...
  Sadaukin Hajiya kenan dan duniya,zare towel din yayi bayan ya juyo yana fuskantar ta sannan ya hau shirin sa a gaban ta har ya gama shirin nasa sannan ya hau feshe perfs din sa da ya saka Saudat tarin dole,dama da gangar yayi dan ya dada kular da ita ganin yadda ta sume a zaune da kallon da take masa tun da ya zare towel din...
  Ai ko yana ganin ta shake sai tari take ta yi ya dau wayar sa da makullin bike din sa yayi waje...
  Kasa tashi tayi tana nan zaune tana kallon sa har ya fice kamar ta kirawo sa sai dai ta rasa dalili tsoron sa ne ko shakkar sa ne suka hana ta dakatar da shi....

  Bai tsaya ko ina ba sai part din iyayen sa inda ya je ya kwashi morning blessings daga wun iyayen nasa ya ma kanwar sa signal wacce itama fitar zata yi but ya ja ta gefe ya mata magana..
  "Yaya yanzu wai har yau baku shirya da aunty bane"?kallon ta yayi ya ce
"Baby sis je ki min abin da na ce lokaci na tafiya ke fita zaki yi nima kuma kin ga fitar zan yi kar muyi latti"!!..haka ta juya ta dawo ciki mahaifiyar su na kallon ta shi kuma ya fita...
 
  Yana nan jingine jikin motar mahaifin sa yana jiran fitowar kanwar tasa,at same time yana tuno ina Ummitah take dan abin na bijiro mai shi tsoron sa daya kar dai a ce mijin nata tsorata ta yayi da ya saka ta yi mai wannan barazanar da tayi zaton mijin ne not knowing it was him...
  Bai lura Mariam ta zo wurin ba sai da ta buga motar ya kalle ta sannan ta ce
  "Haba Yaya na,wai dole ne toh sai kun yi fushin nan?ji yadda duk ka bi ka sauya kai kenan tunani akai akai kamar wanda aka bar maka mu aka ce ka kula da mu"?..
  Shafo cheeks din ta yayi yana fadin
  "Baby sis baki san komai ba sai kin yi auren zaki fahimci abin da nake going through"!!ita dai jin sa take but gani take Yayan nata ne kawai ke exaggerating...
  Miko mai food warmer din tayi da tayi packaging a wani food holder mai kyau,karba yayi yana wurgo mata smile din appreciation...
  Tare suka fita dan shi ya kai ta yayi dropping nata a beauty spa din ta,yana sauke ta yayi gaba sai kasuwa zuwa boutique din sa..
  Ko da ya zo an gama shirya komai a muhallin sa an gyare ko ina already mutani sun fara tururuwa a boutique din dan haka bayan sun gama gaggaisawa ya wuce gefen sa ya zauna inda a nan yayi breakfast din sa ya kammala yayi hamdala sannan ya fito aka fara business...
★★★★
  Sai 6pm ya fara haramar komawa gida dan ya san for sure loneliness ya gama sukurkuta Saudat kuma dama hakan yake so because yana so tayi understanding wani abu a aure,ba kullum ake single handed thought ba komai na da consequences din sa a rayuwar aure...
 
Bayan yayi sallama da yan boutique din nasa ya kama hanyar gida,but still haka yau ma ya ja ya tsaya a Passion Fare a tunanin sa zai yi nasarar ganin ta sai dai yau din ma duk daya because bata nan kuma bai san ya zai tunkari Mrs Bianca da batun daya daga cikin staffs din nata ba(Noor)..
  Yana ji yana gani ya wuce but intention din sa shine bayan ya koma gida zai kuma nemar layin ta maybe a dace ta daga....

TAMBARI[The dark hunt] Where stories live. Discover now