Loyalty

262 54 11
                                    

WATTPAD @SIYAMAIBRAHIM

Mental stability:Dysgraphia is difficulty in the physical act of writing,mental activity,involving comprehension and sensitization of information.

48.Loyalty.

  Tana zaune rike da wayar a hannun ta tana ta juya sa ita kadai a dakin tana tunanin kalaman sa na karshe.
"Think about it,just give it an extreme thought"..
  Kuma Juyawa tayi a kan kujerar sofa dake dakin nata tana nazarin kalaman nasa..
  For good 2 weeks kenan kusan kullum sai ya kira ta ya mata hira,ita dai tana sauraron sa amma bata daukar abin da wani muhimmanci until yau da tun safe yake ta mata kalamai cikin siga daban daban har dai yau ya bayyana mata abinda ke zuciyar sa da nufin sa a kan ta..
"Am not ready for another relationship,no..,i can't involve myself in another mess,not possible,marriage"!!ta girgiza kan ta tana mai kwantawa akan sofan ta ajiye wayar a gefen ta saman wata translucent mini table...

  Lumshe idanun ta tayi tana fatan bacci ya dauke ta sai dai abin ya ci tura,she just can't spot out dalilin sa na son yin tarayya da ita after knowing her past..
  Kamar wasa haka ta raba dare tana tunanin sa a wani part zuciyar ta na son yarda da shi while a wani part kuma tana tsoron involving kan ta a matsalar aure dan tayi a baya bata ji dadi ba..
  Sai misalin karfe biyu da rabi lokacin har idanun ta sun yi luhu luhu sun kumburo sannan ta fara jin bacci na fizgar ta..

★★★
She woke up very late da safe dan ko da ta bude idanun ta da nufin gyara kwanciyar ta sai ta ga a inda baccin ya dauke ta sannan agogon dake manne a bango ita yake kallo directly hakan ya sa tana bude idanun ta sai ta ga karfe tara da mintuna kusan goma..
  Saurin tashi zaune tayi tana addu'ar tashi daga bacci hade da yin mika,ba sallah take yi ba shi ya sa lattin bai daga mata hankali can can ba..
  Duk jikin ta ciwo yake mata ba kadan ba sakamakon bacci bisa sofa da tayi a takure..
  Da kyar ta taka duk tana jin jiri jiri ciwon kai haka,ta isa bathroom tayi striping kan ta,kasa tsayuwa da kyau tayi sai ta shige bathtub kawai ta kunna ruwa babu foam babu komai ya mata yadda take so sai tayi kwamciyar ta ciki kawai...
  Da haka wani sabon bacci ya sace ta ba tare da ta sani ba,bacci ne mai dadi take yi sai dai wani mummunar mafarki da tayi da Asim ya tsorata ta har ta tashi a firgice tana sauke ajiyar zuciya cikin zuciyar ta take addu'a..
 
  Sauri sauri ta fito daga tub din tayi wanka sannan ta fito daga bathroom din..
  Gaban mirror ta isa tayi tsaye duk ta rude dan mafarkin ba mai kyau bane,daha bisani ta sauke ajiyar zuciya ta zauna bisa stool din mirror din ta fara shafa..
  Dan kwalliya tayi marar yawa sannan ta nufi closet din ta,duk ta gama dube duben ta bata ga wanda ya mata a ran ta ba..
  Tsaki ta ja ta koma kusa da akwatin ta da ba kasafai take amfani da kayan ciki ba ta bude dan ko zata ga wani ta saka..
  Tana budewa wasu set din sweet girl suka mata haske a fuska,saurin ciro su tayi,riga ne da wando,rigar peach da touches din pink sai wandon dark blue..
  Sakawa tayi ta dau peach kimono ta dora a kai ta yafa karamin mayafi ta saka takalmin ta ta fito hannun ta rike da waya..

  Hango su tayi suna cin abinci a dinning ban da Nana wacce ta tafi makaranta tun dazu,karasowa tayi ta gaida su tayi joining din su suka cigaba da ci tare..
  Sai da suka kammala sannan Abban nata ya tashi zai fita dan akwai sa da meeting da yake son yayi attending..
  Sun yi sallama har Ammah ta raka sa ta dawo ta zauna a dinning din ta kurawa Ummitah ido,daga dukkan alamu tana da matsala but zurfin ciki ya sa ba zata fada ba ita kuma tayi alkawarin ba zata kuma bari diyar ta tayi going through heartache kamar na baya ba. 
  Matsowa tayi kusa da ita tana duban ta daga bisani ta riko hannun ta cikin nata,wanda ya ba Ummitah damar kallon mahaifiyar nata..
  "Me ke damin ki Noory"?Ammah ta mata tambayar sai ta kasa bata amsa har sai da ta kuma maimaitawa sannan ta amsa mata murya a dan disashe..
  "Ammah wani ne ke son shigowa rayuwa ta,ni dai ina tsoron yin wani relationship da wani,bana ji a jiki na am set for another serious relationship da zai yi leading ma aure,not now,am scared i just can't involve myself again,is too soon"!
  "And who said that is too soon"?Ammah ta mata tambayar immediately bayan ta gama nata bayanin..
  Kallon ta tayi sai ta kasa amsa mata ta dai yi shiru nan Ammahn ta mata bayanin yanayin rayuwa a halin yanzu kuma ta mata nuni da shekarun ta dake ja a matsayin ta na mace kuma tana zaune a gida,almost 8 months kenan da faruwar abinda ya faru da ita game da mutuwar Asim,so it's high time ta kuma bude zuciyar ta coping with the heartbreak she went through a last few weeks na discovering biological father din ta,dole tayi accepting wani a rayuwar ta dan ya dauke mata hankali daga stressors din dake nufo ta..
.
Godiya ta ma Ammah sannan ta tambaye ta me ya kamata tayi,nan Ammah ta bata shawarwari da suka dace,suna tsaka da magana kiran sa ya shigo sai ta kashe wayar ta saka a silent  gabadaya..
  Murmushi Ammah tayi ta ce mata ta daga wayar mana sai ta ji kunya ta kama ta ta ki daga wayar har dai suka gama hirar su sannan ta tashi ta bar wurin..
  Da murmushi Ammah ta bi ta yayin da take haurawa staircase din tana mai kara wayar a kunnen ta.
  Nothing can make her happy sama da tayi witness farincikin diyar ta wanda ta hanya daya hakan zai samu,kuma shine auren masoyin ta da take so har cikin zuciyar ta.
Auren Asim ya zo ne da gaggawa ba tare da ta shirya ta kuma yi shawara da zuciyar ta ba but daga dukkan alamu wannan din,ko ma waye shi,it seems like zuciyar diyar ta yayi na'am da shi and she is rest assured that zai bata farincikin da bata samu ba a auren ta na fari..
 
  A dakin ta ta dangana bayan rufe kofa da tayi ta zauna bisa gadon ta da bata ma sami damar gyara sa ba yau..
  Shiru tayi tana sauraron sa yana ta wanke ta da salon nasa soyayyar da bata taba gani ko jin irin sa a jikin ta da kwakwalwar ta ba..
"I don't know if i am ready for another relationship,ina tsoro"!!ta fada tana leaning bayan ta da gadon..
  On the other side of the phone,Ammar ne ya gyara zaman sa bisa kujerar sa a boutique din sa bayan ya gama digesting amsar tambayar sa da ta bashi sai ya ce da ita
  "Me ya sa kike tsoro"?shiru Ummitah ta mai sannan ta ce mai
  "Saboda wanda nayi na farko ban ji dadin sa ba ya bar min Tambari mai muni kuma har yanzu ban farfado ba"!!ajiyar zuciya yayi sannan ya ce
  "Ban san wa zai shaide ni ba a gare ki,amma ni Ammaruddin na san am a loyal fellow,na san hakkokin dan adam ga dan uwan sa haka na san hakkin zaman tare kuma i pray that after owing you as my wife,in kokarta kwatanta maki hakkokin ki da ya zama tilas a kai na ba tare da kin yi kukan rashin wani abu daga gare ni ba,wannan shine shaidar kai na da zan iya baki for now,sauran kuma sai Allah ya sa kin zo kin gani da kan ki"!murmushi tayi ta ce
  "Are you like bragging about yourself"?darawa ya dan yi yayi juyi a kan kujerar sannan ya ce
  "Not at all iya gaskiyar kenan,ki yarda da ni"!daga wayar ta ji ana cewa ina Ammar yake sai ta ce mai
  "Nemar ka fah ake yi"gyada kai yayi sannan ya amsa mata da
"Eh masu siyayya ne kin san halin wasu in suka zo sai su ce lallai lallai sai ni zasu gani,abin na annoying Saudat sosai but i pray that ke zaki iya controlling jealousy din ki"!!murmushi tayi ta ce mai
  "Toh sai anjima,go and attend to them first sai anjima".saurin kashe wayar tayi tana murmushi shima ya bi wayar da kallo yana murmushi..
  That day was so sweet to both Ummitah and Ammar dan ita har ta shaida ma Fadilah wacce kwanan ta biyar kenan da komawa dan Imran ya riga ta komawa gida saboda aikin sa ita ce ta tsaya dan kuma kwantarwa mahaifin su da hankali..
  Ita dai Fadilah gargadi ta mata akan ta yi a hankali dan ta iya giving in completely in tana soyayya,kar ta bari yayi breaking mata zuciya kamar yadda Asim ya mata..
  Sai da ta warware mata ko waye shi mai bibiyar nata sannan Fadilah ta saki ran ta har da addu'ar Allah ya sa kar a dibi lokaci mai tsawo wun saka bikin dan dai ta matsu Ummitah ta zo kusa da ita a second time..

★★★★
  Da dare bayan Justice Sulaiman Abdullahi ya dawo ne Ammah ke shaida mai hirar su da Ummitah sai yayi murmushi ya ce Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi.
  A washegari yayi kiran ta akan maganar ta da Ammar,inda ya mata tambaya akan zuciyar ta ya yarda da shi ko a'a,amsar ta dai shine eh dan ta san ko a'a ta ce toh shi eh zai ce dan baya son ta cigaba da zaman gida ya fi so a ce yau tayi aure itama ta fara ajiye family din ta dan su kara yawa from four to more greater number..
  Dadi ya ji da ta amsa da eh dan haka ya bata time range akan su fahimci juna sosai in the next 2 months kafin manya su shigo lamarin.
  Amsa mai tayi ta tafi sai ya kira Ammah ya fada mata yadda suka yi har ya dora da a bar Alhaji Sabitu yayi assuming responsibilities din sa as her father ta wurin involving kan sa a wannan bikin nata but Ammah ta ki yarda ta ce ai bai san zafin ta ba ta yaya zai zama uba a gare ta a wannan lokaci..
  A takaice dai sai da Justice Sulaiman yayi da gaske kafin su yi drawing conclusion akan Alhaji Sabitu shi zai zama uba ga Ummitah in maganar auren ta ya taso...

  ★★★
  Lokaci na ta tafiya har tsawon wata guda da satittuka,relationship din su Ummitah na kuma bunkasa,while tsakanin Ammar da Saudat abin sai a hankali,because zafin da ya dauka da ita har ya kai matsayin da sai da tayi involving mahaifin ta a maganar ya kuwa bata laifi ya mata fada sosai hade da nuna mata bacin ran sa sannan ya kira Ammar ya bashi hakuri..
  Bai boye masu ba ya shaida masu burin sa na kara aure tun ma kafin yayi discovering abinda Saudat tayi sakamakon tausayawa wacce zai auran..
  Ita dai uwa uwa ce,duk inda aka ce uwa,toh dole sai ta ji wani yanayi a yayin da ta ji za a wa diyar ta kishiya but da yake professor Lubabatu mai ilimi ce sai ta danne zuciyar ta ta kuma kira diyar nata ta shaida mata komai hade da tursasa ta daurewa ko ya zata ji dan tunda yayi niya toh fah sai yayi bata isa ta hana sa ba..
  Shi kam Ambassador Haris fatar alkhairi ya mai da addu'ar zama da su su biyun lafiya..

  A ranar da Saudat ta dawo gida bayan mahaifiyar ta ta fada mata batun kara auren da Ammar zai yi sai da ta kulle kan ta a daki ta ci kuka sosai sannan ta bi Ammar din dakin da ya maida nasa ta saka mai kuka tana rokon sa da ya janye batun kara auren nan..
  Ko gezau bai yi ba ta karaci kukan ta gwanin tausayi ta tashi ta bar mai dakin..
  Is not as if abin baya taba sa,but at least duk wani abinda zata yi ya kamata a matsayin sa na mijin ta ya san da shi,though ba siyan ta yayi ba amma auren ta yake yi hakan ya bashi damar mallakar kusan 90% of her life da duk wasu movements din ta,yau da a ganganci tayi wannan abin zai iya accepting kuskuren but she did it intensionally a hayyacin ta cikin rightful senses din ta..

   Haka nan tana ji tana gani yayi fowarding maganar auren sa ga iyayen sa inda Hajiya Rashida wacce ake kira da Fulani mahaifiyar Ammar ta nuna sam bata yarda ba akan wai cim fuska zai ma Saudat dan bata san abinda ya faru tsakanin sa da Saudat din ba,shi kuma mahaifin sa ya ce in har hakan ya mai kuma matar sa bata da matsala da wannan nufi nasa toh he should go ahead shi bai da damuwa..
  Haka Hajiya Fulani ta ki yarda,ba ita kadai ba har da family members din ma basu yarda ba,duk kannen sa basu yarda ba dan Saudat na masu halin dattako kuma bata jin kan ta as diyar mai kudi,elder sister din su ce kadai ta yarda ta goya mai baya wato Amira..
  Ita ce ta zo ta ma mahaifiyar nasu bayanin abinda ya faru da Saudat tayi a boye ba tare da sanin Ammar ba sannan ta fada mata dalilin Ammar na son auren Ummitah har ta nuna mata arzikin gidan da Ummitah ta fito da yadda bata da dagin kai itama kamar Saudat dan har ta fi Saudat sauki..
  Ita dai Hajiya Fulani ba wani gamsuwa tayi ba dan ta ji tarihin Ummitah haka ta san ita din bazaura ce kuma ga incidence da ya faru na kai ta prison da aka yi har aka yi zaman shari'a a kotu da ita,so Hajiya Fulani has gone wild in her thought about Ummitah..
  Big sister da ta san dama sai sun sha ta kafin mahaifiyar nasu ta amince da auren,sai ta rinka zuwa gidan a kai a kai a duk zuwan ta sai ta sako maganar Ammar,hatta da Amatullah mai bi ma Ammar din ta sauya akidar ta na kin yarda da auren dan bata san alkhairin dake cikin auren ba,Mariam ce dai ta ki kuma har yanzu bata yarda ba..
  Kasancewar ta favourite din Ammar sai kin yardar ta yayi ta sagar mai da gwiwa dan kusancin ta da Saudat duk ya fi na sauran so bata so da yardar ta a ci amanar Saudat kamar yadda take fada..
  Shi kuma iya gaskiyar sa kenan,auren Ummitah babu fashi in har mahaifin sa ya yarda kuma sisters din sa biyu na tare da shi,toh ya san mahaifiyar sa da sauran kannen sa zasu ma yarda ne..
  He just can't wait ya ji Ummitah ta furta mai an ce manyan sa su shigo lamarin su,duk kuwa da pressure da yake samu dahawun Saudat da kannen sa har ma da mahaifiyar sa,but hakan bai hana sa jin shaukin son mallakar Ummitah ba...

#The clinical manifestation of this condition include poor organisation,poor handwriting,problems learning basic concepts,etc..the general intervention include,promoting constant practice,facilitating close interaction between d nurse,teacher and other children,providing adequate diet,etc..the health issue that may possibly arise from ignoring this condition is low self esteem and psychological trauma to the individual facing this condition..

TAMBARI[The dark hunt] Where stories live. Discover now