Awaken memories

280 50 2
                                    

WATTPAD @SIYAMAIBRAHIM

Mental stability:Depression is a pathological disturbance of mood towards sadness and pessimism.it is seen to others as an affective psychosis in which there is psychomotor retardation.

18.Awaken memories

  Kwance take ita dai idon ta biyu but hankalin ta ba a tare da ita yake ba sai kallon wuri daya take ta yi tun dazu,juyin ma kasa yin sa tayi sakamakon ciwo da zafin da zuciyar ta ke mata..
  Sallama ta jiyo a kan ta,bata san sa'ilin da aka shigo ba bata kuma san wanene ba..
  Dago kan ta tayi ta ga mother in-law din ta ce dan haka ta mike zaune a hankali hade da amsa sallamar tana gyara hular kan ta hade da saukowa kasa sabanin da da akan gado take..
  Kare mata kallo tayi ta ga kamar tana cikin damuwa da dogon zullumi sai tayi kamar ta tunkare ta directly amma ta fasa ta sako wani maganar..
  "Lafiya dai ko yar nan tun dazu na aika a kirawo min ke mu ci abinci kuma Baban ku na son magana da ke ya ce wayar ki bai shiga ba amma shiru shiru baki fito ba me ke faruwa"?shiru tayi kan ta a kasa,ta san in ta tsawwala yiwa Hajiya doguwar bayani definitely hawaye ne zai zubo mata in kuma hakan ya faru toh dole sirrin da take boyewa zai fallasu dan haka tayi takaitacciyar magana..
  "Lafiya kalau Hajiya jikin ne ke dami na kuma tun dazu bacci nake yi wayar na a flight mood shi yasa"!ajiyar zuciyar samin relief Hajiya ta sauke sannan ta ce
  "Toh yanzu fah,ya jikin naki"?gyada kai tayi sannan ta amsa da
  "Na ji sauki wanka nake son yi Hajiya in na gama zan zo"!kallon tausayi Hajiyar ta bi ta da shi tunanin ta kewar mijin ta ne ya sa ta zamo suku suku haka..
  Mikewa tsaye tayi tana kare ma dakin kallo sai ta ga komai kamar a hargitse,kada kai tayi tana fadin
  "Zan aiko maki Bella ta zo ta gyara maki wuri dan komai ya sauya kamanni".tana gama fadin haka ta juya ta fita..
  Saudat dake zaune a kasa ta gyara zaman ta,sai a sannan hawaye masu zafi suka fara zubo mata,bata cuci kan ta ba ta zage tayi kukan ta sosai sannan ta je tayi wanka ta shirya ta cikin casual dress din ta da ta saba saka ire iren su in tana gida sannan ta nufi sashen in-laws din nata..
  A zuciyar ta ta san ta yiwa mijin ta laifi but bata san hanyar da zata bi dan bashi hakuri ta san ko gigi take ba zata tunkari mahaifin ta da zancen ba dan ya rigada ya sanar da ita mace ita ke gyara gidan ta haka kuma ita ke bata shi dan haka zaman aure ibadah ne duk abin dake cikin ta ibadah ce kar tayi sakaci da ibadar ta,a yamzu da abubuwa suka kacame mata ta rasa madogara sai take tunano kalaman mahaifin nata duk da ta san bata da courage din fuskantar sa beside he has so many things to deal with toh ita a wa da kara mai matsalar ta..
  Isowar ta part din in-laws din nata sai ta ga kusan duka gidan ne a inda ba kasafai aka fiye zama ana cin abinci sai lokaci lokaci...
  Farinciki ne ya mamaye ta har ta manta da damuwar ta dan haka da murnar ta ta karasa gare su tana ta furta
  "Wow,wow what a brilliant surprise whats the special occasion"?kallon ta suka yi suka saka mata dariya ganin wai ta manta abin dake faruwa a gidan,basu ga laifim ta ba sai suka dangana mantuwar nata da tafiyar da mijin ta yayi dazu..
  Ja mata kujera Amjad yayi yana fadin
  "Zauna ke dai aunty"zaman tayi tana mai gaisawa da su bata juyo ga Mariam ba ta ga ana turo wata medium size cake da candle lights a gefen cake din..
  Dafe kai tayi tana girgizawa sannan ta dago ta kalli Hajiya da itama ita take kallo..
  Kasa magana tayi sai kawai ta rungume Mariam tana fadin
  "Forgive me dear ba mantawa nayi ba i was carried away ne so sorry"dariya Mariam din ta mata tana fadin
  "I know and i understand auntyn mu it's not easy so na yafe maki"murmushi Saudat tayi ta raba jikin ta da na Mariam...
  Kawo cake din aka yi aka ajiye saman family sized dinning table din inda a nan aka yi lighting sauran candles din aka hau yi mata waka sannan ta hura candles din ta yanka cake..
  Mahaifiyar ta Hajiya ta fara sakawa cake din a baki sannan ta sakawa babbar yayar su aunty Amira,daga ita sai Saudat sannan ta bi kowa da shi,da ta gama itama suka bi ta da shi bayan an gama aka fara presenting mata gifts kala kala a karshe dai Saudat komawa sashen su tayi ta dauko ma sister In-law din nata gift din ta da kuma na Yayan ta ta taho da su...
  Bayan ta bata nata gift din sai ta ce mata ta rufe idon ta bayan ta rufe sai ta saka mata key a hannu,ita dai Mariam ta shafa ta kara shafawa ta ji kamar key,cikin sauri ta bude idanun ta ai kuwa ta ga car key..
  Wani irin tsalle ta daka mai dauke da ihu ta dire kasa tana nunawa mahaifiyar ta tana fadin
"Hajiya ki ga Yaya kyautar da ya bani,aunty Amira kalla,Ama duba ki gani my birthday gift"..dariya aka yi aka taya ta murna da sanyawa kyautar albarka ita dai murna har cikin zuciyar ta..
  "Motar na gidan gona in kin shirya..you can go tomorrow"..cikin farinciki ta ce
  "A'a aunty yau zamu tafi Amjad ya raka ni"!tsawatar mata mahaifiyar su tayi tana fadin
  "Baki ganin dare yayi ne,rawar kai har ki jawo ma kan ki matsala"!zama tayi ta ce toh ta yarda sai goben..
  Daga haka shagali ya kankama ana ta hotuna ita dai Hajiya ta tafi ta bar su suna ta sha'anin su wanda ba su suka nutsa ba sai 10pm..
  Saboda annashuwa ma a nan part din Saudat ta kwana tare da big Sis wacce dama weekend ta zo yi dan mijin ta baya nan kuma tana da niyar zuwa ziyara amma saboda clashing da yayi da birthday din kanwar su sai ta yanke hukuncin kara kwanaki akan wanda zata yi,ita dama Amatullah yar gari ce dan haka bayan an gama shagali mijin ta ya zo suka tafi...
  Hira sosai Saudat da big sis suka yi kafin su kwanta bacci wanda kafin baccin har ta manta da wani wai Ammar....

TAMBARI[The dark hunt] Where stories live. Discover now