Hidden truth

258 55 31
                                    

WATTPAD @SIYAMAIBRAHIM

Mental stability:Neurasthenia is a condition that is associated with the nervous system concerning exhaustion wic is characterized by fatigue,headache,insomnia and vague Somatic complains.

45.Hidden truth.

  Kasa bacci Ummitah tayi a daren ranar ba dan komai ba sai tunanin da Ammar ya saka ta ciki kafin ya tafi,ta san ya damu da ita sosai sai dai hakan ba yana nufin yayi playing games din sa da labarin ta bane..
  Juye juye take ta yi a gadon ita kadai ta rasa me ke mata dadi tunanin Ammar ya tsaya mata a kai ga fargabar faruwar saka bikin su da za a yi gobe ita da AbdulHakam..
  Da ƙyar ta samu ta rintsa bayan ciwon kai mai tsanani ya addabe ta sosai..

★★★
Da safe da farinciki ta tashi ba dan komai ba sai sakon Fadilah da ya mata morning greetings akan suna nan a gombe kuma tare da su za a zo saka ranar dan Imran ma ya biyo su a wannan zuwar..
  Kiran AbdulHakam ne ya shigo,da murmushi ta daga wayar tana mai yi mai sallama.
  Bayan ya amsa sun gaisa sun gama romantic talks din su ya ce mata kar ta kuskura ta gudu yau sai ya hadu da ita ko da a cikin dakin ta ta boye zai saci hanya ya zo har dakin..
  Dariya sosai ya bata sai kuwa ta dara din ya cigaba da nanata mata sai fah sun hadu yau din nan ita dai jin sa take but ta san ba zata iya hada ido da shi ba yau sai dai bayan komai ya lafa..

  Wanka tayi ta dau ado mai daukar hankali ta saka native ta yane kan ta da babbar mayafi ta zauna a dakin ta saitin window ta yadda zata na ganin komai dake gudana a farfajiyar gidan..
  Hotuna ta shiga yi ma kan ta kala kala tana ta turawa Fadilah dake mota tare da mijin ta,ai kuwa tayi forwarding ma yayan ta ango to be..
  Zumudi da shaukin ganin amaryar nasa ya saka sa gaba duk gani yake kamar mai jan motar bai iya ba,abin mamaki shi da zai zauna a gida but ya dage wai da inda zai tafi nan kusa da gidan su Ummitah..
  Iyayen nasa sun gano sa so kyale sa suka yi already ya gaya masu he is serious about his wedding da Ummitah,so sai da suka tabbatar suka yarda sannan suka mutunta maganar nasa kafin Hajiya Safinatu ta kira matar AbdulHakam har gidan ta ta mata nasiha ta kuma bata hakuri akan auren da mijin nata zai yi,ta ji ba dadi but ta san masoyiyar sa ce ta fari da bai samu ba sai a wannan karon so bata isa ta hana sa ba dan gidan mijin nata ba a rikici ko samin rashin fahimtar juna so ba zai kyautu ba a ce ta daga hankalin ta akan bikin da za a yi ba. 

12pm
  A cikin gidan su Ummitah motocin da ba zasu haura biyu ba suka yi parking,da jin karar motocin Ummitah ya tashi tana leken su haka daya bayan daya suka rinka fitowa suna shiga ciki bisa jagorancin sambo..
  Murna sosai ne ya kama ta,ta rasa inda zata saka kan ta wai yau za a saka mata bikin ta da first love din ta abinda bata san zai faru nan kusa ba..

  A nan main parlor kuwa an cike gaban su bakin da kayayyaki kala kala kamar dai yadda aka saba yi in aka zo zuwa ta musamman irin wannan..
  Gaiggaisawa aka yi na manya cikin mutunci da girmamawa,sai da aka bada hakurin abinda ya faru a shekarun baya wato rashin fahimtar da ya ratsa tsakanin Justice Sulaiman Abdullahi Mai sa'a da AbdulHakam..
  Sosai  abin ya basu dariya dan ba karamin yarinta AbdulHakam yayi ba a lokacin so an yi basing hakan a matsayin haukar so wanda shi Justice din ya sanar da su ai shima ba karamin wahala ya sha a kan mahaifiyar Ummitah ba da ya nuna mata son da yake mata..
  Dariya duk aka yi daga haka aka dan taba hira kafin a koma fannin abinci aka ci aka sha daga bisani aka maida hankali ga abinda ya dace..

  Nan dakin Ummitah kuma Fadilah ce ta gama cika mata kunne da surutai da kwadaita mata kyawun gidan ta da yayan ta ya gyara mata..
  Ummitah dai ban da murmushi babu abinda take yi har Fadilah tayi connecting video call da Saima wacce ke hanya itama zata zo ma Ummitah taya murnar dawowar first love din ta..

  Nana ce ta shigo da murmushi a fuskar ta cikin shigar riga da skirt na atamfa tayi daurin ta na zamani ta yafa mayafi a gefe daya sai tayi kama da matar manya dan girman jikin ta ya sa ta so fin Ummitah kyau da fitowa. 
  Zama tayi kusa da yayar nata tana murmushi murya kasa kasa ta ce
  "Aunty Ummi guess what"?da fara'a Ummitah ta ce
"Me ya faru kin san am not good in guessing".da fara'a a fuskar ta ta ce
  "Yaya AbdulHakam na wajen gate wai in zo in ce maki yana jiran ki"dariya duk suka yi su ukun..

TAMBARI[The dark hunt] Where stories live. Discover now