Break free

251 61 41
                                    

WATTPAD @SIYAMAIBRAHIM

Mental stability:Hypochondriasis is a mental health condition that is characterized by 6 months/more of general and non delusional preoccupation with fear of having/the idea that one has serious disease base on the person's misinterpretation of body symptoms.

46.Break free.

Suleja Niger state

  Wayar dake hannun ta ta bi da kallo tana murmushi duk da akwai damuwa sosai a fuakar nata amma ba yadda zata yi sai hakuri kamar kullum..
  Tashi tayi ta saka mayafin ta ta fito ta rufe kofar apartment din ta ta nufi na in-laws din ta..

  Da Mariam tayi karo wacce take sauri zata fita,mayafi a hannu,takalma a hannu,ga jaka ga car key,duk ita kadai sai ta ba Saudat dariya har ta dara ta kalle ta daga sama zuwa kasa tana fadin
  "Ke kam Mariam me ya same ki yau da kika fito a hargitse kamar wacce aka turo daga cikin gidan a firgice"!dan yamutsa fuska Mariam tayi ta dubi Saudat da fuskar tausayi ta ce
  "Aunty Saudat latti nayi ina da appointment da wasu brides guda hudu duk gida daya ne kuma ko wacce da yadda take son a mata shirin ta,sannan ina da appointment at 11am da wasu couples but just look at the time,10am wace irin boss lady ce ni?na tsallake time"!!
Murmushi Saudat tayi ta riko kafadun Mariam tana bata assurance dan ta rude da yawa..
  Godiya Mariam ta ma Saudat da karfafa mata gwiwa da tayi sannan ta sallame ta ta wuce ita kuma ta shiga ciki suka gaisa da Hajiya a inda Hajiyar ke tambayar ta ko ta ji motsin Sadauki,nan Saudat ta sanar da ita daga dawowar sa da yayi daga yau zuwa gobe..
  Addu'ar nasara Hajiya ta mai da fatar dawowa lafiya,a nan sashen Saudat ta kai har zuhur sannan ta koma sashen ta tayi abinda zata yi around 5 ta fita a motar ta zuwa gidan iyayen ta dan duba lafiyar mahaifin ta..
  Ko da ta tafi closed friends ne a kusa da mahaifin nata suna zantawa akan al'amuran ta'addancin da ya addabi kowa a kasa..
  Ganin diyar nasa ya sa abokan nasa yi masa sallama da fatar samin lafiya,gaida su Saudat tayi ta zo ta zauna kusa da mahaifin nata tana mai ya jiki..

  Sosai ya ji dadin ziyartar sa da tayi dan dama tana ran sa ta kwana biyu bata zo gidan ba,tambayar ta mutanin gida yayi ta tabbatar mai komai lafiya lau..
  Suna hiran nasu ne mahaifiyar ta ta zo ta same su a wurin suka gaisa ta zauna itama tana sauraron hirar tasu kafin daga bisani su biyun suka haura zuwa dakin mahaifiyar Saudat din suka cigaba da hirar su ta yau da kullum..
  Damuwa sosai Saudat tayi na rashin samin wanda ya aikatawa mahaifin ta wannan abin but ta san ko a jima ko a dade gaskiya zata bayyana.

Sai bayan isha'i ta fara shirin komawa gida bayan an mata nasiha kala kala na kara hakuri da zama da mijin ta da yan uwan sa da iyayen sa karshe mahaifiyar ta ta kara kwantar mata da hankali akan matsalar ta na rashin haihuwa tana mata nuni da lokaci,in yayi Allah sai ya azurta su da shi..
  Jikin Saudat yayi sanyi matuka but ta daure ta dawo gida hankalin ta baya jikin ta,tunanin rashin haihuwar duk ya dame ta amma zata cigaba da rokon Allah da ya kawo mata karshen wannan damuwa nata,ana aure ne dan cika ibada sannan ana fatar in aka yi Allah ya albarkaci auren da albarkar aure wato haihuwa,har yau bata cire ran haihuwa da Ammar ba lokaci kawai take jira Allah ya tabbatar mata da shi..

★★★
  Danna wayar yake yi amma ya rasa wa zai kira cikin su,yayi kiran layin Fadilah har ya gode Allah but bata daga ba,haka ita kan ta Ummitah,yayi kiran har ya gaji,sannan yana fargabar kiran iyayen nasa kar su ce mai bai da kunya...
  Gajiya yayi da zaman motar sai ya fito ya tunkari hanyar cikin gidan dan dama bai da nisa da gidan,har ya kawo gate din gidan sai ya juya kawai ya shige mota ya ja ya nufi hanyar gida..
  Tunanin sa maybe an gama komai abinda ya rage shine su dawo dan ya san yaushe aka saka bikin...

  On reaching home sai ya ji ashe ba a kira yan gidan an sanar da su komai ba,sashen Hajiya Safinatu ya shiga inda ya gan ta zaune kamar wacce aka sanar da ita abu marar dadi..
  Bayan ya mata sallama ta amsa mai sai ya fara tambayar ta ko lafiya su Abban su basu kira ba..
  Bin sa da kallo kawai tayi ta girgiza mai kai sai ya kasa fahimtar ta dan haka ya tambayi ko lafiya take nan be ta ce mai zazzabi ke damin ta tana so ta kwanta,addu'ar samin lafiya ya mata sannan ya sallame ta ya je ya sallami Hajiya Karama kafin ya tafi...

TAMBARI[The dark hunt] Where stories live. Discover now