Law

284 54 13
                                    

WATTPAD @SIYAMAIBRAHIM

Mental stability:Circumstantiality is an irrelevant repetitive method of speach that has no meaning or may be meaningful but contains diverse unreasonable words.

34.Law
7pm

Beeping wayar ta ke ta yi sai da ta farka dan dole ba dan tayi niya ba.
  Duban ta ta kai ga wayar sai ta ga sunan yayan ta na yawo a kan screen dan haka ta wartsake idanun ta da kyau ta dauka tana mai sallama..
  Mikewa zaune tayi tana gyara zama sai kuma ta tashi a hankali ta fita daga bedroom din ta dawo parlor murya a kasa kasa ta ce
  "Yaya AbdulHakam ka tsaya ka ji please kar ka daga murya kar wani ya jiyo ka,ka gane,abin ya zo ne kai tsaye toh presently halin da ake ciki shine an yi transferring case din zuwa appeal court kamar yadda ka ji toh Imran dama ya min bayanin haka yake so shi da Saima akan wai suna da dalilin su ka san lauyoyi ne su ban ja da dalilin su ba na san they can do it,so please ka yi shiru kar ka fadawa kowa ka barwa kan ka bana so family din Ummitah su ji wannan zancen ka san abin zai yi muni please ka barwa kan ka yaya ka ji"?.
  Bayan some seconds sai ta kashe wayar tana sauke ajiyar zuciya ta juya ta zauna kan kujerar ta tana mai hade kan ta da gwiwar ta tana ta sauke ajiyar zuciya same time tana ta fidda sautin "uhum" akai akai..
  Kusan 35minutes tana zaune a wurin sai daga bisani ta mike ta shiga kitchen ta fara aikin girki hankalin ta duk a rarrabe kashi kashi..
  Da kyar ta kammala abincin tayi packaging wani a babban food warmer sauran a plates tayi wrapping da transparent covers,ta saka food utensils da duk abin bukata ta lullube da wani cotton wear cover..
  Sauran da tayi serving a wasu food warmers ta hau firfito da su tana jerewa a saman dinning table har ta gama jerewa a table din sannan ta nufi bedroom dan tayar da Imran amma sai me?babu shi ga dakin nan very shattered and rough alamar fitar sauri yayi,komawa tayi da baya ta nufi dakin Saima nan ma ta ga bata nan hakan ya tabbatar mata tare suka fita..
  Komawa daya dakin tayi ta dubo yaran ta sai ta ga har an masu wanka an shirya su except baby Azma dake bacci a bedroom din su..
 
Fitowa tayi zuwa parlor ta dau wayar ta inda ta bar shi ta kira layin Imran,bugu uku aka daga cikin sauri ya ce mata yana zuwa zai kira ta in ya gama abinda yake yi..
  Haka ta sauke wayar daga kunnen ta tayi tagumi tana nazarin duniya tana nan bata yi wanka ba bare ta sauya shiga daga night wear din ta zuwa kayan gida..
  Tayi ta zaman jiran su har misalin ƙarfe goma na safe sannan suka dawo gida saibta bi su da kallo Saima ce ta mata bayanin abinda ya fitar da su da sassafen wanda bai wuce akan case din Ummi bane..
  Dinning suka nufa suka zazzauna ita kuma ta je ta fito da su Ubaid da Aziza zuwa dinning a nan suka dai kokarta suka ci abincin sama sama suka tashi inda Fadilah ta sanar da su ita zata kaiwa Ummitah ziyara dan ta so su tafi tare amma suka riga ta fita..
  Imran ne ya tambaye ta akan ko tana iya tuka kan ta sai ta ce mai a'a kuma dama ya san da hakan dan ba a hayyacin ta take ba kawai daurewa take yi..

Bata damar yin wanka yayi ta shirya suka fito tare da Saima wacce yau zata koma gida kasancewar an dage case din nasu zuwa sati biyu zaman ta a nan din bai da amfani tunda Imran na nan sai kawai tayi concentrating akan abinda ya fi muhimmanci da dole ita zata yi sa..
  Tare suka fito suka raka ta har motar ta ta shiga suka mata sallama da fatar dawowa lafiya after 2weeks din..
 
Journey din 25 minutes ne daga gidan su zuwa station din da aka kai Ummitah,ko da suka tafi kala Fadilah bata ce ba hasalima natsuwa tayi da sai da mijin ta yayi mamaki dan bata saba ba,in har abu ya same ta daga hankali take yi ba kadan ba..
  A natse ta bi bayan Imran da basket din abincin ta a hannu har Imran ya masu bayanin Fadilah a matsayin aminiyar Ummitah kuma ziyara ta kawo mata sai suka amince dan bayan an gama shari'a a kotu Hajiya Sifa'u ta sanar da su kar su rinka hana yan ziyara zuwa wun Ummitah dan tana da nata burin,wannan ne dalilin da ya sa yau basu ja ba suka yarda a gana da ita..
 
Some minutes bayan zuwan su station din sai aka fito da Ummitah da ta sauya kamanni kamar ba ita ba nan take hawaye ya hau zarya a fuskar Fadilah tana rufe bakin ta a karshe fadawa jikin Imran tayi ta sake kukan ta har Ummitah ta zauna Fadilah bata daina kuka ba sai da Imran ya rarrashe ta akan tayi shiru ga Ummitah nan ta fito su gaisa lokacin su na tafiya..
  Tana share hawaye tana jan hanci ta kalli Ummitah ta kawo hannu ta shafa fuskar ta sai wasu zafaffan hawayen suka hau wanke mata fuska ta kasa magana..
  Wannan hawayen nata ya sa dole Ummitah ta ji itama zuciyar ta ya karye kawai sai ta hau zubar da kwalla  haka Imran yana kallon su cikin tsantsar tausayin su har suka kusa cinye lokacin su sannan Fadilah ta gaida Ummitah tana tambayar ya lafiyar ta daga karshe ta dauko abincin da ta zo da shi ta dora saman table da ya raba su..
"Ummi..,ga abinci ki ci...,i am so sorry i couldn't help in freeing you but i promise inshaAllah wannan case din zai zo karshe da yardar ubangiji ki ji"!?gyada mata kai Ummitah tayi daidai lokacin su ya cika suka tashi ba dama bare su rungume juna haka aka zo aka maida Ummitah ciki su kuma suka fita..

TAMBARI[The dark hunt] Where stories live. Discover now