Back in time

255 52 8
                                    

WATTPAD @SIYAMAIBRAHIM

Mental stability:Exceptional child is refer to those with one or more behavioural problems,children with physical disability or sensory impairment and children who ate exceptionally gifted or have a special talent.

40.Back in time.

"Saudat kina zargin wani ko wata da aikatawa Abba wannan mummunar ta'adin ne ki fada dan a samo mafita"?kallon sa tayi sai ta girgiza masa kai..
  "But yawa yawan mafarke mafarke da kike yi a kwanan nan yana wuce misali ona ga in da wani abu a ran ki ki fitar dan a samo matsaya daya"!!kuma kallon sa tayi sai ta fada jikin sa ta fashe da kuka..
  Rarrashin ta ya rinka yi yana bata magana har ta dan sarara daga kukan nata ta fara fada mai wadanda take zargi yana nadar maganganun nata a brain din sa har ta gama sannan ya ce da ita
  "I doubt cikin wadannan mutanin akwai mutum daya da zai akata hakan kin san mutani a yanzu ba a shaidar su they can disappoint you"jan hanci tayi tana mai dagowa daga jikin sa dan ta dube sa da kyau..
  "Ammar am not lying na san me nake yi cikin abokan Abba na aka sami mai kosasshen zuciyar yi masa hakan but me ya masu da zafi haka?he never betrayed anyone,he never harmed anyone,ko dabba da kananun halittu Abba na yana basu hakkin su bare mutum sannan a zo a mai wannan irin abin definitely akwai mutum daya cikin wasu na kusa da shi dan Umma sai da ta gargade ni da kar in fadi inda suka kai Abba dan samin kula na musamman,me ya masu da suke son raba sa da duniyar"?ta karasa tana mai zubda hawaye sai ya kuma rungume ta yana rarrashin ta..
  "Is okey zamu gano ko ma waye kuma dalilin sa duk zamu gano ki daina kukan nan da dagawa kan ki hankali please,kin ji".shiru ta mai tana zubda hawaye sai da ya manta da idon ta biyu dan dare ya tsala yayi tunanin tayi bacci sai ya ji muryar ta a hankali..
  "Ammar menene alakar ka da yarinyar nan da ka ce kana siyo mana abinci a wurin su"?shiru yayi yana juya tambayar nata dan direct attacking question ne wannan ba sigar irin tambayar da ta saba yi mai bane..
  Numfasa yayi ya kuma maimaita mata kamar yadda ya maimata mata a baya ranar da wannan tashin hankalin ya riske su..
  Tana sauraron sa har ya dire sai ta hadiye wani abu marar dadi a throat din ta sannan ta daure ta bude baki cikin faduwar gaba ta ce mai
  "Kana son ta ne"?wani irin zabura yayi ya daga ta daga jikin sa yana mai tashi zaune daga kishingiden da yake yana fadin
  "Hell no"!!a dan tsawace sai ta gyara zaman ta ta rinka bin sa da kallo,ta san akwai abubuwa da dama a duhu dake boye,ta fi kowa sanin miji ta waye shi kuma abinda zai iya yi akan abinda yake so..
  Hawaye ne ya zubo mata daga idanun ta bata goge ba ta gyada mai kai dan zuciya ta tafarfasa yake yi ta san ko a jima ko a dade dama watan watarana sai ya bijiro mata da wani abin wanda ba komai bane sama da batun kara aure dan babu wanda zai so yayi aure kuma bayan shekara har zagayowar wata shekarar zuwa shekaru ba tare da an sami albarkar aure ba,dole abin ya dagawa mutum hankali musamman namiji da yake ganin yana da dama da yancin karo auren sa daidai har hudu toh a kan me zai cigaba da zama da mace daya da bata haihuwa...
 
  Kukan ta ne ya fito fili sosai sai ya jawo ta jikin sa yana rarrashin ta hade da bata magana..
  "Saudat kar ki sake yi min magana related to this lady,ever again,na san me nake yi a yau da son ta nake yi me zai saka ni zama in fada maki abinda na sani dangane da rayuwar ta?me ma zan yi da wata macen bayan ina da nawa matar"!?katse shi tayi ta hanyar ce mai
  "Ammar da baka son ta me zai sa ka rinka biniyar ta har ka daga hankalin ka dan baka gan ta ba a rana?me zai sa ba zaka so wata macen ba tunda kai dai namiji ne kuma kana bukatar haihuwa haka zalika kana da dama da yancin karo matan har uku bayan ni,ya kake tunanin ba zan damu ba kuma ba zan saka zuciya ta a zullumi ba"!?kallon ta yayi for a moment sai ya sauka daga kan gadon ya fito zuwa parlor ya zauna..
  Biyo sa tayi zuwa parlorn tana kallon sa har ta zauna a opposite direction din da yake zaune ya zama suna fuskantar juna kenan sai ta zauna shiru har na wasu mintoci sannan ya dago ya kalle ta suna kallon juna cikin ido..
  Dan kawar da kan sa yayi daga duban ta yana kallon wani sashen,ita da kan ta ta fara maganar..
  "Ammar kar ka gujewa conversation din mu,it's not yet done and you are very good in fun of doing this always,running away from an incomplete conversation"!tsawa ya daka mata yana tashi tsaye..
  "Saudat ki fitar min a ido idan har yau baki san abinda ya dace ki yi da wanda bai dace ki yi ba then ban san har sai yaushe zaki yi realizing abinda ya kamace ki da yi ba,am fed up with all these unusual attitude of yours,just check this out,when last kika saurare ni a cikin gidan nan?huh?baki sani ba,when last kika sauke hakkin ki a matsayin ki na mata ta a gidan nan?baki sani ba,yaushe rabon da ki bar ni in rabe ki a gidan nan?you can't tell,yaushe rabo na da tunkara ki da bukata ta a cikin gidan nan?baki sani ba dan baki ba aure na dignity ko kadan kuma,i never complained but yau kuma ke ce mai complaining da attacking di na,please,i don't want anything again this night ki bar ni in yi bacci"!yana kaiwa nan ya kwanta bisa three seaters ya juya mata baya..
  Kasa cigaba da zaman wurin tayi ta tashi ta koma cikin bedroom din ta ta lalubo wayar ta dan kiran mahaifiyar ta not minding lokaci ya tafi..

TAMBARI[The dark hunt] Where stories live. Discover now