WATTPAD @SIYAMAIBRAHIM
Mental stability:Alcohol addiction is an illness which gives rise to physical,and social problems,centred on chronic excessive intake of alcohol.it is a cause of several kinds of mental illness and may itself be caused by an underlying psychosis .
24.Wishes
10amZaune suke a kan dinning table suna breakfast duk hankalin su na kan abincin su,ka'ida ce in har aka fara cin abinci toh ba a magana sai an kammala dan suna ba table manners muhimmancin sa..
Karar spoons da plates kadai ke communicating da echoing a wurin sai daga bisani suka kammala suka yi hamdala sannan duk suka dawo main parlor suka zazzauna aka fara hira wanda mostly ya shafi rayuwar zamantakewar Ummitah ne a gidan mijin ta..
Duk da yadda ta so dodging hirar amma abin ya ci tura sai da Ammah ta saka ta amsa tambayoyin da ta rinka yi mata a karshe ta dora da sako mata zancen kai ziyara zuwa wun kakannin ta..
Ta tsani jin an dauko wannan zancen dan ba alheri ke faruwa ba in har ta kai masu ziyarar shi ya sa tun bayan auren ta bata taba yarda wata alaka ta shiga tsakanin su ba kuma bata so..
Canza kalar walwalar fuskar ta tayi ta daure fuska hade da kokarin maida hankalin ta ga kallon wani indian movie da aka saka mai suna Bajirao mastani,film din ya zame mata one of the best indian movies da take so da kauna cikin indian movies da take kalla...
Ganin ta sauya akalar ta sai Ammah ta kyale ta dan ba kasafai ta cika son takurawa yayan nata ba musamman ita Ummitah da ta kasance eldest..Nana ma maida hankalin ta tayi ga kallon duk kuma suka bar Ammahn a tsaka,ita dai ba kallon take yi ba ta so a ce sun natsa sun zanta sosai da diyar nata akan matrimonial home da relationship din ta sai dai ita diyar nata is not willing to voice it out..
Ko da kallon yayi nisa sai Ummitah ta tashi ta dawo kusa da Ammah tana tambayar ta..
"Ammah da karfe nawa kika ce Abba zai dawo yau"?shafa fuskar ta tayi tana amsa mata da
"By 6pm zasu yi arriving InshaAllah after his today's assignment,me ya sa kika tambaye ni"!?murmushi tayi tana fadin
"Kawai so nake ni da Nana mu shiga kitchen tare mu yiwa Abba best delicious meal"!dan bude ido Ammah tayi in amusement ta ce
"Oh wow,MashaAllah am amuse,fada min me zaku ma Abban naku"?jin an kira sunan girki kuma an kirawo sunan ta sai ts juyo ta ce
"Aunty Ummi Allah da gaske kike tare zamu shiga kitchen"?dariya tambayar nata ya ba Ummitah sai ta gyada mata kai kawai..
Dawowa kusa da ita tayi tana ta tambayar me da me zasu girka sai suka maida ta abin dariya daga bisani Ummitah ta tambaye ta yaushe zasu koma makaranta sai take fada mata ai a online take karatu,jin haka sai Ummitah ta kalli Ammah cikin mamaki zata yi tambaya amma Ammah ta riga ta ta hanyar tarar numfashin ta..
"Don't ask me,Abban ku ne ys biye mata"!!kallon Nana tayi tana mamakin ta..Kalar fuskar ta ya tabbatarwa Nana tambayar ta yayar ta ke yi akan dalilin karatun online alhali ana karatu a makaranta..
Cat face ta saka kalar tausayi ta marairaice sannan ta ce
"Aunty Ummi bana jin dadi ne,kin ga makarantar mu yanzu under sanction yake,almost 2 weeks after resumption aka gano wasu illegal students a cikin makarantar mu toh tun bayan hakan school authority ke ta son gyara komai na makarantar toh ni kuma Aunty Ummi bana son in gama school a makarantar da keda bad past shi ya sa na cewa Abba ya maida ni online classes in exams ya zo kawai in tafi in yi in mun gama in dawo gida ko bai yi ba aunty Ummi"?kallon tuhuma Ummitah ta rinks yiwa Nana dan ta san wannan silly excuse ne irin nata da ts saba kirkira da zarar ta ji abu bai mata ba sai ta fara hado wasu irrational reasons da words shi kuma Abban nasu haka zai biye mata wai nsn sunan mahaifiyar sa gare ta shi ya sa ko tari tayi in dai yana kusa toh sai ya tambaye ta lafiya,wannan ne dalilin da ya sa sai huruwa take yi kamar an kumbura ta da oxygen ko ina ya cika,hatta mahaifiyar su da ta haife su bata kawo kurkushin ta a kiba ba..."Nana kin san cewa you are becoming over obese kuwa"?kara marairaice fuska Nana tayi kalar tausayi ta ce
"Aunty Ummi me kuma na yi?duk morning and evening exercises din da nake yi kenan baya working out"?hararar ta tayi tana fadin
"Who knows Nana?am serious the moment Abba gets back here am gonna talk to him about you"jin haka sai Nana ta saka kukan wofi tana fadin
"Ammah ki ba aunty hakuri wallahi na daina Ammah ni dai ba zan bi aunty Ummi ba zuwa garin nan,bana son in bar ki"!!sai hawaye dan ta san the moment ta bi Ummitah toh ka'idoji da dokoki ne zai biyo baya dan duk jin dadin nan bata isa tayi shi a gidan auntyn nata ba kuma ita bata shirya dakatawa daga cikin wannan rayuwar ba,Abban ta bai hantarar ta Ammah ma bata hana ta yin abin da take son yi..
YOU ARE READING
TAMBARI[The dark hunt]
HumorPeople round the world are being taunted and looked down on due to the feeling of misery and low self worth that is caused as a result of direct and indirect factors which gradually leads to so many social negligence and harassment in many situation...