WATTPAD @SIYAMAIBRAHIM
Mental stability:Enuresis is a repetitive involuntary voiding of urine during sleep whether day or night occurring after an age when continence is expected to have been achieved.
37.Affection.
It was a journey of about 9hours despite the speed,daga Abuja zuwa gombe saboda sun sami hold ups a wasu wurare shi ya sa tafiyar ta masu tsayi dan a lokacin da suka iso gombe zazabi ya gama rufe Ummitah rufe da kyar Ammah ta taimaka mata suka karasa cikin gidan da zuwan su ta nufi dakin ta da ita ta kwantar da ita aka kira family doctor dan ya zo ya duba ta..
Bayan misalin mintuna da ba su haza ashirin ba doctor ya zo ya dudduba ta yayi kokarin sa sannan ya mata allurai ya sanar da Ammah matsalar dake damin Ummitah currently wanda ba komai bane sama da shock and trauma dan haka yayi urging din su da su tabbatar sun bata kulawa ta musamman yadda ya dace dan a gajiye take tana bukatar hutu..
Godiya Ammah ta mai ya wuce sannan ta tura Nana zuwa dakin ta dan tayi wanka ta kwanta itama yau kusa da yar ta zata kwana shekaru biyar da dori basu jima da zama ba sai sama sama bata san damuwar ta ba abin da ya faru ba karamin dagawa Ammah hankali yayi ba amma in ta tuno da cewa komai ya zama sai dai tarihi yanzu sai ta ji sanyi a zuciyar ta..
Itama wankan tayi tayi sallolin ta tana yiwa Allah godiya da ya nuna mata karshen wannan musiba ya sa ya zamo tarihi a rayuwar su.
Saukowa kasa tayi ta nufi kitchen da kan ta ta hadawa Nana oat ta zuba mata milk da sugar one full cup ta saka spoon ta kai mata dakin ta..
Dama yanzu itama Nanan ta idar da sallah tana shirin zuwa dakin Ammahn dan a nan take son ta kwanta..
"Ammah kin zo ne?dama yanzu zan zo wun ki nima a nan dakin ki nake son in kwanta"riko hannun ta Ammah tayi suka zauna ta fara feeding nata ba garda Nana ta rinka karba har Ammah ta gama ta ja hannun ta zuwa gadon ta ta kwantar da ita tana shafa fuskar ta sannan ta ce
"Kwanta ki yi bacci Nana kar ki manta ki yi addu'ar bacci"!ta dora mata goodnight kiss a goshin ta ta juya ta fita..
Komawa kitchen ta yi ta hada fast soup na zallar vegetables da sardine fresh fish yayi ruwa ruwa ta juye cikin wani bowl gabadayan sa sai ta kuma dora wani ruwa ta dafa couscous da boiled egg ta juye a plate ta jere a tray,warm water ta tsiyayo daga flask ta zuba a wani jug karami duk ta dora bisa tray din..
Fitowa tayi zuwa dakin ta inda ta aje tray din a kan wani karamin table ta dawo gadon ta zauna ta kurawa Ummitah ido.
Hawaye ne ya hau sauko mata yana diga bisa kumatun ta,Allah kadai ya san kaddarar da ya hada Ummitah aure da mijin ta su basu sani kuma ko wace irin kaddara ce ubangiji ya sa iyakar sa kenan.Tana ta kallon ta tana baccin gajiya,saka hannun ta tayi ta share hawayen fuskar nata ta ja hanci ta dau wayar ta ta duba time kusan 12am sai tayi dialing wani number da aka yi saving da Amor ta saka wayar a kunnen ta..
Some seconds da kiran aka daga sai kawai ta fashe da kuka ta kasa magana har sai da aka mata maganar ta daya bangaren sannan ta ce
"Amor am happy but am sad"!!ko me aka ce mata ssi ta kuma cewa
"Am a mother,but i don't act like one"!!sai kuma ta cigaba da kukan har daga bisani ta ce
"Sai ka dawo safe trip"!!daga haka ta aje wayar tana mai cigaba da kallon Ummitah dake bacci..
Kamar bayan wasu mintuna da gama wayar Ammah sai Ummitah ta bude idanun ta a hankali tana mai Juyowa da kyau daga right lateral position da ta kwanta..
A hankali da fara'a shimfide saman fuskar Ammah ta matso tana taya ta tashi zaune,supporting nata tayi da pillow ta dan yi leaning bayan ta da shi..
Zama kusa da ita Ammah tayi tana kallon ta sai Ummitah ta ga kamar mahaifiyar nata na cikin damuwa sai ta murmusa hakan ya saka Ammah jin dadi a ran ta ganin diyar nata ta sake jikin ta..
"Noory bari in kawo maki bowl ki wanke bakin ki ki ci wani abin na san kin jima rabon ki da abinci"!Ummitah bata hana ta ba ta tashi ta je ta dauko bowl da wani toothbrush cikin pack din sa ta saka toothpaste ta zo mata da shi..
Da taimakon Ammah Ummitah ta tsaftace bakin ta sannan Ammah tayi presenting mata hot soup din da ta mata,matuka Ummitah ta ji dadin miyar ta san duk kwarancewar ta a fannin girki Ammahn ta ta ninka ta ta juya dan wannan fannin nata ne daga gare ta ta gada sai dai still knowledge din Ammah a nan yake ta lakanci girki..
"Ammah na thank you na ji dadin miyar"!ta fada da murmushi a fuskar ta sai itama ta maida mata martani..
"Toh bari in baki abinci ki ci ko"!gyada mata kai tayi Ammy ta zubo mata couscous din da sliced egg ta fara bata da kan ta,zallar couscous ce fara amma an mata dafuwar maggie da gishiri yayi wazar wazar haka sai aka yanka cooked egg a ciki round aka yi garnishing dan ya bada attractive appearance..
Dadi sosai Ummitah ta ji ganin one of her favourite dan a lokacin tana gida kusan duk dare shi take ci kafin ta kwanta bacci dalilin da ya sa Ammah ta mata shi kenan..
"Thanks Ammah"!feeding nata Ammah ta hau yi a hankali har ta koshi ta ma Ammah godiyar abincin..
Maida hankali Ammah tayi gare ta tana ta kallon ta itama ita take kallon daga bisani ta kwanta jikin Ammahn ba dadewa baccin ya kuma daukar ta,kamar 5 minutes da fara baccin nata Ammah ta tada ta tana ce mata ta tashi ta taimaka mata tayi sallah dan tun sallar zuhur har isha'i duk bata yi ba..
YOU ARE READING
TAMBARI[The dark hunt]
HumorPeople round the world are being taunted and looked down on due to the feeling of misery and low self worth that is caused as a result of direct and indirect factors which gradually leads to so many social negligence and harassment in many situation...