WATTPAD @SIYAMAIBRAHIM
Mental stability:Encopresis is the voluntary passing of faeces into clothing after an age in wic continence is expected to have been achieved.
38.Nature
Around 7pm Ammah ta zo ta kira Ummitah da ta zo su yi having dinner already Abban su ya dawo har Nana ta hallara kan dinning..
Tasowa tayi suka fita tare zuwa dinning din inda da zuwan ta ta tarar da Abban nata na zaune sai kawai ta karasa ta je ta rungume sa tana kuka..
He knows the pains she is going through sai ya rinka calming nata yana bata magana Nana na ta kallon su Ammah na share nata hawayen itama..
"Is ok you are back to your family now kar ki ji fargabar komai".zama ta yi kusa da shi tana gaida sa da yi mai ya hanya..
Daga bisani suka fara cin abincin bayan Ammah tayi serving kowa,Nana ce mai dan bada dariya itama dan dai yau Abban ya so ne if not in suna cin abinci bai cika son ana magana ba sai ya zama dole..
Ko da suka kammala cin abincin lokacin prayers yayi sai Abba ya tafi masallaci akan in ya dawo zai yi magana da Ummitah..
Su ma sallar suka tafi yi da ya dawo ya aika aka mai kiran Ummitah dan ya san she is affected emotionally and psychologically..
Fara yayi da yi mata brief bayani akan matsayi da matakin rayuwar aure sannan ya kawo mata constitutional laws dake guiding zaman aure inda ya rinka nuna mata kura kuran ta a rayuwar aure wanda babban kuskuren shine yin shiru da ta yi bata furtawa kowa ba ciki har da mahaifiyar ta wanda shirun ne yayi leading ma abubuwan nan duk da suka faru but ya karasa bayanin nasa ne da nasiha mai sanyaya jiki a karshe ya mata albishiri da cewa da zarar ta gama iddah zai fitar da ita zuwa duk kasar larabawan da take son tafiya dan ta sami kwanciyar hankali ta dawo normal self din ta..
Murna sosai ta yi da wannan albishir dan dama ko bai yi mata shi ba ita tana da niyar sanar da shi dan she is traumatized tana bukatar quite environment to calm her self kuma ta fara saka hope a al'amuran rayuwa..Sai da suka yi hira sosai sannan ya rabu da ita ta koma sashen Ammah inda ta labarta mata duk yadda suka yi da Abban nata itama ta ji dadi sai dai murnar nata takaitacce ne dan ta so su fara rayuwa tare da diyar ta ta bata kulawar da ta jima tana muradin bata amma bata sami damar bata shi ba,but wannan din ma is a nice idea a can din ta san diyar nata zata sami sukunin zuci..
Haka nan rayuwar Ummitah ya kasance a gidan iyayen ta sam babu hantara babu fargaba babu tsoron kowa ko komai,duk wani fear da anxiety din ta ta kawar da su ta sake jiki da ran ta dan ta san tana rightful place ne da ko motsi tayi ta ce auch za a tambaye ta me ke damin ta.
A kwana a tashi ga mai yawan rai har Ummitah ta gama iddar ta Abban ta yayi presenting mata visa din ta bayan ya cike mata account da kudade sai ta karba tana murna kusan tana iya cewa tun dawowar ta gidan bata taba leka waje ba iyakar ta farfajiyar gidan sai gobe da take saka ran fita ba iya gidan ba ma har kasar gabadaya..Tana kwance tana chatting da Fadilah tana sanar da ita kasar da zata tafi wato Saudiyya ita kuma ta mata murna da fatar alheri daga bisani ta kwanta bacci dan Ammah ta gama arranging mata komai nata..
The next morning ta tafi dakin Ammah dan gaida ta sai ta tarar tana hada kayan ta abin sai ya bata mamaki me hakan ke nufi..
Ammah da ta san ma'anar kallon mamakin da Ummitah ke mata sai ta dan yi murmushi ta ce
"Tare zamu tafi ni,ke da Nana"!!wani runguma ta kaiwa mahaifiyar nata na jin dadin wannan al'amari dan tayi tunanin ita daya zata tafi ashe surprising nata Abban ta yayi..Tare suka yi breakfast as family ta rinka yiwa Abban nata godiyar barin Ammah da yayi su tafi tare dan ba kasafai yake yarda tana nesa da shi ba sai ya kama dole..
Yi mata nuni yayi da ai yanzu ita Ummitahn ta fi bukatar kulawar Ammahn sama da shi shi ya sa ya bar su su tafi tare..
Abin ya mata dadi ba kadan ba tayi ta murna kamar bata taba zaman kunci ba,duk da a baya kafin zuwan wannan rana takan zauna tayi ta tunanin rayuwar ta na baya wato rayuwar aure,in ta gwada ta auna a mizani sai ta ga auren nan kamar halting kai ne a lifetime prison da fitar sa wani babban karatu ne mai zamar kan sa..
YOU ARE READING
TAMBARI[The dark hunt]
HumorPeople round the world are being taunted and looked down on due to the feeling of misery and low self worth that is caused as a result of direct and indirect factors which gradually leads to so many social negligence and harassment in many situation...