WATTPAD @SIYAMAIBRAHIM
Mental stability:Oppositional Defiant Disorder(ODD) is a childhood disorder characterized by a pattern of negativism,defiant behaviour,disobedience and hostility towards authorities or parents.
11.Trapped(Back to reality(present)D Kallamu's residence)
Ko da ya zo gab da ita sai ta kara saurin tafiyar ta dan dai kar ya kamo ta amma haka shima ya rinka hadawa da gudu har da ya kamo ta suna daidai kofar parlor din su..
Cikin sauri ya sha gaban ta yana fadin
"Kin ga Saudat in akwai abin da na tsana toh fah shine silent punishment,yana min kamar na zalunce ki abu daya tun jiya ina ta faman baki hakuri amma haka kina kallo na kamar abin ma bai damin ki ni ina cikin wani yanayi,anya Saudat ba canzo min ke aka yi ba kuwa"?ya ida maganar yana mai langabar da kai cikin jimami sai ta tsaya kare masa kallo..
Ta dai san ba halin sa bane haka kawai ya bata lokacin sa yana sauraron mata ba amma abin da hsusawa ke kira da kishi kumallon mata shine kawai ke addabar ta..
Ajiyar zuciya tayi suna fuskantar juna kafin tayi kamar magana zata yi sai kuma daga bisani ta fasa ta tura kofar tayi shigewar ta leaving him there with no option but to go to his work..
Kada kai yayi yana mamakin halin matar nasa kafin ya saka kai yayi wucewar sa dan ya san ta haura sama sosai kuma bata taba yi mai fushi irin ta yau ba dan haka ya saka a ran sa zai kyale ta har dan kan ta ta sauko..
Tafiyar sa yayi ya hau bike din sa ya ja ya wuce kasuwa dan gudanar da kasuwancin sa irin ta yau da kullum..
Abin haushi da mamakin shine yadda ya kasa hankalin sa kashi kashi,rabi na ga tunanin matar sa rabin na ga tunanin Passion Fare dan ya kwana biyu yana tunanin tunkarar ta da wani kudirin dake zuciyar sa sai dai rashin kwarin gwiwa ya sa ya kasa tunkarar ta da batun,rabin hankalin sa kuma na ga business din sa dan dai kar ya tashi ne a ce mai ya zamo mai tsoron matar sa if not tuntuni da ya koma gidan duk abin da zai faru ya dade bai faru ba,but ya san yana tashi da sunan zai tafi gida ne toh fah an rinka teasing nasa kenan akan jiya matar sa ta zo ta kwance hauka ya rasa sukunin sa har yau...A haka dai ya hakura har daya na rana yayi ya mike ya dau makullin mashin din sa da wayar sa yayi gaba yana jan mashin yana tunae tunane barkatai har saura kiris a bige sa bai lura ba..
Instead ya wuce gida sai ya ja ya tsaya a bakin Passion Fare hoping to see her but bai hango ta ba dan haka ya sauko yayi takakkiya ya shiga ciki yayi tambaya aka ce da shi bata weekend duty,sai a sannan ya tuna ashe a weekend ake kuma fah dama ya san bata zuwa a saturdays and sundays but tsabar rudu sai ya manta gabadaya..
Komawa yayi ya hau bike din sa ya ja sai gida,ko da ya shiga sai bai ga motar Saudat ba wanda hakan ke tabbatar mai da cewa eh fah Saudat gudun sa tayi dan ta gaji da hallayar sa..
Ai babu tantama ko second thought ya sauko yayi hanyar cikin gidan su yana faman tambayar ina Saudat take kamar wani wanda bai girma ba..
Yana karasowa parlorn mahaifiyar sa yayi kicibis da auta Farmanullah,sai ya tambaye sa
"Ina auntyn ku take"?Farman ya kalle sa ya ce
"Yaya ban sani ba yanzu nima na shigo gidan ita nake nema ta ara min motar ta dan gobe da shi zan shiga school"..abin haushi shi ta mota yake sai kawai ya wuce sa ya wuce part din mahaifiyar sa yana mai cigaba da kiran ta amma bai ji amsa ba..
Da dan karfi yayi sallama aka amsa mai ya tura kofar ya shiga yana mai dube dube har dai ya gaji ya dawo ya zauna suka gaisa da mahaifiyar tasa sai ya hau kame kame kafin ya mike ya bar ta bisa abin sallah yana fadin
"Hajiya bari nima in je in yi sallar ban yi ba a kasuwa"..da mamaki ta kalle sa sannan ta gyada masa kai alamr toh,daga haka ya fito yana waiwaye waiwaye ko zai gan ta amma bai gan ta ba..
Barin nan sashen yayi ya wuce nasu sai ya ga kofar a bude dan haka cikin sanyin jiki ya lallaba ya karasa ciki yana addu'ar ganin ta amma shiru haka ya gama shawagin sa amma babu Saudat babu kamannin ta,kamar zai yi hauka shi kunyar zuwa gidan su yake yi ya ce ma me toh in tafi?ya ce na zo ne dubawa ko Saudat na nan??no abin bai yi tsari ba..
Haka ya rinka magana da kan sa openly a karshe dai ya dangana da zama a bakin gadon su ya tallafo cheeks din sa da hannuwar sa biyu yana nazari da tunanin ta ina zai fara nemo ta,dan dai ya san aminiyar ta daya ce in and out of suleja kuma ita ce Kausar toh ita kan ta Kausar din bata nan tana makaranta daya aminiyar ta kuwa bayerabiya ce mai suna Kabirah toh ita kan ta a cikin ABJ take in ba wani sha'ani ya taso masu ba da take zuwa yin kwalliya wun ita Saudat din ba toh da wuya su hadu..
Dan haka tunanin sa ya bashi cewa babu yadda za'a yi ta dauki jiki ta tafi ABJ da sunan ta tafi rage zafin ran ta dan bata taba zuwa gidan su da sunan wai yau sun yi fada bari tayi yaji ba,sai dai ta kulle kan ta a sashen iyayen sa ta hana ma idanun sa ganin ta har sai ta ji dan kan ta ta bar shi su hadu..
Yau kam bata can kuma bata nan toh ina ta tafi?ba dai wani hali ya saka ta ciki ba!?..
Yin wannan tunani sai da gaban shi ya fadi dan haka yayi salati a zuciyar sa kafin ya tashi yayi alwala ya zo ya fita zuwa masallacin kofar gidan su dan yin sallar zuhur because ya makara already...
A cikin masallaci ya rinka kullawa yana warwarewa akan inda zai gan ta ta ina ma zai fara,a karshe dai tashi yayi ya dawo gidan ya wuce part din su ya kwanta yana tunanin ta har dai bacci ya dauke sa bai sani ba..
YOU ARE READING
TAMBARI[The dark hunt]
HumorPeople round the world are being taunted and looked down on due to the feeling of misery and low self worth that is caused as a result of direct and indirect factors which gradually leads to so many social negligence and harassment in many situation...