Way back

346 58 2
                                    

WATTPAD @SIYAMAIBRAHIM

Mental stability:Stammering/Stuttering is a speech disorder in which the flow of speech is disrupted by involuntary repetition and prolongation of sounds,syllable,words or phrases.

21.Way Back

9am
  Cikin shigar doguwar riga mai siffar dinkin buba simple babu adon komai ta fito kan ta lullube da mayafin maryam kalar kayan jikin ta wato lemon green,fuskar ta babu ado sai lips din ta da ta sakawa chapet dan yayi lubricating da moisturizing lips din,kafar ta sanye cikin wani posh swiss half cover shoe very flat,hannun ta na dama rike da car key na hagu kuma rike da wayar ta...
  Da walwalar ta ta sauko daga kan step din benen,idanun ta na kan Ammah tana ta sakar mata murmushin wanda ke da nasaba da ganin kan ta kwance a dakin Ammahn ita kadai babu kowa kenan bacci ya sace ta ba tare da ta sanar da Ammahn labaran da ta ce mata zata sanar da ita ba...
  Duk da cikin dare ta farka daga baccin nata amma bata ga kowa ba sai tayi tunanin sanar da Ammahn damuwar ta ne ko dai tayi shiru,abin da ya dade yana kai komo cikin zuciyar ta kenan throughout last night sai daga karshe ta yanke shawarar saurin kai Fadilah gida dan kar ta fadawa Ammah abin da take ciki tun kafin ita ta shirya fadawa Ammahn...

Nana ce ta taso ta zo da gudun ta ta rungume Ummitah tana fadin
  "Aunty Ummi kin ga yadda kika yi kyau kuwa?ni shi ya sa nake ta kewar ki nake ta kewar ki amma kika ki zuwa ki gan ni"da sakalci na yaran da suka yi girman parlor ba tare da brain din su ya gama developing ba Nana tayi maganar..
  Fadada murmushin ta Ummitah tayi tana mai jan kumarmatun Nanan sannan ta ce
  "Common auta sauri nake je ki taya aunty Lilah kwaso kayayyakin ta zan kai ta gida"!da sauri Nanan ta ce
  "Aunty Ummi zan bi ki".a wannan lokacin dariya ta ba Ummitah ganin desperation all over her face gashi ya nuna a muryar ta alamar yawo take son zuwa..
  "Toh jeki ki kwaso kayan ki saka a mota ki ce da sambo yayi starting min motar kafin in fito"ta karasa maganar tana mai miko mata car key din..
  Karba tayi ta haura sama dan fara aiwatar da abin da aka saka ta yi,ita kuma Ummitah ta karaso wun Ammah dake sanye cikin doguwar bakar arabian Agyad abaya mai adon sea blue pattern flower ta manyan mata da gyalen sa da ta mai nadin dankwali...
  Da zuwan ta instead ta zauna sai ta kwantar da kan ta a kafadar ta tana mai yin kasa da muryar ta tana furta
  "Ammah ina kwana"shafa kan ta tayi tana mai amsa mata cike da kulawa da kewar ta..
  "Ammah shine kika min wayo kika baro ni ni kadai ina ta bacci kuma fah na fada maki zan baki labarai"!murmushi Ammah ta mata tana cigaba da shafa kan ta kafin daga bisani ta ce
  "Noory na san halin ki sama da kowa,shi ya sa na bar ki ki huta dan na san ba zan ji labarin nan ba har sai yau"dariya Ummitah tayi ganin mahaifiyar nata bata manta da ko kankanin halin ta ba...
  Suna nan a haka Nana ta fito da akwati mai taya guda daya while kafadar ta na sagale da madaidaicin jaka..
  Wuce su tayi babu jimawa sai ga Fadilah na saukowa hannun ta rike da baby Azma yayin da Aziza da Ubaidullah ke tafiya suna gaban ta..
  Daga kai Ummitah tayi ta kalle ta tana mai sallamar Ammah akan yanzu zasu tafi dan kar tayi dare wun dawowa saboda akwai tazara sosai daga nan cikin gari zuwa wurin su Fadilah..
  Tashi tayi tana mai karbar baby Azma ta mikowa Ammah tana tsokanar ta ta hanyar ce mata
  "Bye bye Azma mun bar ki da granny zamu tafi"sai ta riko hannun Fadilah kamar da gaske tafiyar zasu yi,tun yarinyar na wal wal da idanu har ta fasa kuka da ya saka su yi mata dariya suka dawo..
  Gaisawa suka kuma yi da Fadilah dan sun gaisa tun safe kafin Ummitah ta farka daga bacci,addu'ar kiyaye hanya Ammah ta masu da sakon gaisuwa zuwa ga yan gidan su Fadilah tayi sannan ta mikawa Ubaidullah wata well packaged bag pink colour tana fadin
  "Tunda kai baka min cefane ba toh ni na maka dan gwara miji da kishiya,ke kam Aziza babu ruwa na da ke dan na ga in nayi sake toh sai ki kwace min miji"wata dariyar suka kuma yi Fadilah ta rinka yi ma Ammah godiya tana mai ce da yaran su ma granny godiya..
  Daga haka suka fita daga parlorn zuwa farfajiyar gidan inda wata dramar ta so kaurewa tsakanin Fadilah,Ummitah da sambo dan kuwa tsare su yayi yana masu tambayar dalilin da ya sa basu sanar zasu zo ba sai kawai suka masu bazata har ya tsorata ya dauka yan bindiga dadi ne..
  Fadilah ce ta tsaya sauraron sa har suka rinka exchanging kalamai yana tambaya tana biye mai,Ummitah dai wuce su tayi ta shige motar tana kallon su tana dariya,sai da Nana ta gaji ta zaku ta mai wani irin ihu tana hararar sa..
"Samboo hab,ka rabu da mutani mana,da wanne mutum zai ji?da gajiyar sa ko da surutur ka"?shiru yayi yana kallon ta hade da fadin
  "A yi hakuri Hajiya Nana"tsaki ta ja a yayin da Fadilah ke shiga cikin motar sambo ya je ya bude gate suka fita daga gidan yana waving nasu da hannu..
  "Mutum sai maganar tsiya da son shisshigi fadi ba a tambaye ka ba kai sambo Allah ya shirye shi"dariya Fadilah tayi tana fadin
  "Ni kam auta kamar dai da sambo za'a yi Ammah dole ta hakura a baiwa sambo,irin wannan kallon soyayya da aka rinka mai dazu uhum"saurin kallon Fadilah tayi ta kyabe fuska game da cewa
  "Aunty Lilah ni...ni...ni dai bana so"daga Fadilah har Ummitah duk dariya suka saka ita kuma tayi kicin kicin da fuska alamar an taba ta..
  IPad din ta ta kunna ta shiga wurin videos ta saka wani matured cartoon movie mai ma'ana mai suna Moana wanda tayi rotating iPad din dan su ji dadin kallon movie din ita da yayan Fadilah tunda ta ga kamar tsokanar ta su aunties din nata ke jin yi...

TAMBARI[The dark hunt] Where stories live. Discover now