Dark Hunt

240 53 10
                                    

WATTPAD @SIYAMAIBRAHIM

Mental stability:Depersonalisation is a situation in which the individual experience the feeling of unrealistic things and is disconnected from himself.

44.Dark Hunt.

   Ganin kamar ba zai yi magana ba sai ta ce mai.
"Me ya faru"?tsabar mamaki da al'ajabin abin sai ya rasa me zai ce mata sai ta cigaba da maganar ta.
"Justice Sulaiman is the man behind my succession i was given a second chance again a rayuwa to enjoy all life goodies ya tsaya min a rayuwa despite knowing ni ba diyar sa ba ce but ko a slightest mistake bai taba yarda an nuna min bambanci ba i was thirteen when Ammah gave birth to Nana but duk da hakan ban ga bambanci ba life was great"
"Mun kasance muna ziyartar junan mu ni da Fadilah haka relationship din mu yana da kyau,a lokacin da muka girma ita ta tafi wani kasa karatu ni kuma na tafi wani kasar wato kasar Paris,a can na yi karatu na har na kammala inda na karanci fannin girki kamar dai layin Ammah na"
"A shekara ta ta karshe ne yayan Fadilah ya nuna interest din sa a kai na sai dai ban yarda ba dan ina gudun kar abinda ya faru da Ammah na ya faru da ni duk da na san shi din ba mai irin wannan halin bane but ban yarda da shi ba"
"Da ya ga haka sai ya bi ta Fadilah ya nemi shiga ta wurin ta,ni da Fadilah mun zama daya,i was 10 years when Ammah told me that Abba wasn't my father sannan ina 15 Ammah ta fayyace min komai so Fadilah babu abinda bata sani ba game da rayuwa ta dan haka na nuna mata fargaba na akan relationship di na da dan uwan ta but ta min nuni da ai yana sane da hakan but ya ce ya ji ya gani"
  "Ban so yarda ba sai dai ganin kamar Fadilah bata ji dadi ba sai na yarda,the first day he came was a memorable day for me because ranar da ya fara zuwa ya dasa min soyayyar sa a zuciya ta,he planted it deeply and i was like kamar son yayi yawa a matsayi na na wacce bata da gata duba da yanayin da aka haife ni".
"But gradually yaya AbdulHakam thought me how to love him and put my trust in him,sosai muka saba da shi har ya kai Ammah ta sanar da Abban mu maganar,toh dama shi Abba na haka yake so in yi aure in sama masu jikoki because bai yi auren wuri ba sai da ya jira Ammah kuma baya ga hakan ma family din sa sun so su juya mai baya but kasancewar shi din mutum ne mai karfin ra'ayi sai ya ki sauraron su yayi fastening auren sa da Ammah toh tun lokacin ya nesanta kan sa da su not because he doesn't need them but because baya son su hantari Ammah da ni".

"Ana haka ne bikin Fadilah ya taso aka maida hankali ga bikin nata sosai har muka tafi da ita garin suleja inda a nan take,so abinda ya faru shine ranar da muka kai Fadilah gidan mijin ta a washegari sai muka fito dan tafiya da ita Fadilar gidan marikan mijin nata dake nan suleja,bayan mun gama komai muka fito da niyar dawowa sai na lura da wani a wajen gidan da yake ta bi na da kallo so ban maida hankali na ga wannan mutumi ba na kyale sa".
"Abinda ban sani ba shine biyo mu a baya yayi har gidan Fadilah har aka firfito aka fara shiga cikin gidan,dai dai na fito kenan sai ya tsare ni yana tare da wani abokin sa mai suna Uzee"
  "Ban so in tsaya ba but ya tsara ni haka na tsaya na saurare sa,yayi yayi in bashi contact di na but na ki sai da abokin nasa ya saka baki sai na basu"
  "Bayan na shige cikin gidan sai nayi blocking nasa a waya ta dan bana jin zan tarbi abinda yake nufi,haka muka wa Fadilah sati daya mu uku kawaye ni,Saima da Aisha wacce ta zama diyar yaruwar mahaifin Fadilah"

"Har na dawo gombe  ban ji kira da wata bakuwar lamba ba sai da na share sati uku sannan na ga kira da bakon numba sai na daga ina mamakin mai kiran"
  "Bayan ya min sallama ya sanar da ni sunan sa,then i began to wonder inda nayi coming in contact da mai suna irin wannan,sanin ina tunani ne sai ya ce min Asim ne daga suleja nan ya min bayanin sa"
  "Mamaki sosai nayi kamar in yi cutting nasa off amma na kyale sa har ya gama ya kashe sai kawai ya rinka kalailaye ni da zantuka kala kala tun bana murmushi har na fara murmushin dan Asim mutum ne mai barkwanci da wasa da dariya"
  "Ana haka muka dau watanni har biyu tare da Asim a lokacin ban san menene matsayin sa a gare ni ba sai dai na san ina son yaya AbdulHakam though shi Asim din ya fito min a mutum akan so na yake but ban ba abin muhimmanci ba sai na sanar da Fadilah dan a lokacin Abba ya fara maganar yaya AbdulHakam ya turo da manyan sa"
"Sosai hankali na ya tashi na shiga damuwa dan shawarar da Fadilah ta bani bai min ba ita wai bata son Asim not because yaya AbdulHakam yayan ta ne na jini but because hankalin ta bai kwanta da Asim ba musamman da ta saka mijin ta bincika mata wanene Asim ta san labarin sa sai ta ce ai mahaifiyar sa bayerabiya ce so rayuwa na na iya tangarda saboda mahaifiyar sa is too strict and a principle woman so for that bata ji ya mata ba"
"Ni kuma a nawa karamin tunanin sai nake ganin tunda shi Asim bai san yarinta ta ba haka bai san munin rayuwa ta ba kamar in sanar da shi yadda aka haife ni in ya so in zai iya aure na sai ya aure ni a hakan in ba zai iya ba sai ya bar ni in auri yaya AbdulHakam duk da ina shakkun anya ba zai zo ya wulakanta ni ba"
"So da Asim ya ishe ni haka Abba ya daga maganar sai na ma Asim magana akan ya turo manyan sa,that day was the first day i marked th dark moments of my life,a ranar da hakan ya faru a ranar na fadawa Abban dalili na sannan na roke sa da ya taya ni yiwa yaya AbdulHakam bayanin komai akan ya gafarce ni ya yafe min but ina fargaban auren sa gudun kar wataran ya goranta min"
  "Abba na mutum ne shi mai fahimta dan baya son boye boye straight forward person ne shi so ya kuma tambaya ta in na tabbatar ina son Asim din kuma na amince da shi sai na ce mai eh na amince da shi so sai ya sanar da Ammah abinda ake ciki har ta so ta daga hankalin ta but ya hana ta so sai ta zuba ido kawai amma ita kan ta hankalin ta bai kwanta da Asim ba but ganin kamar ita ta bani mummunar Tambari a rayuwa ta sai take jin bai dace tayi controlling rayuwa ta sosai haka nan ba shi ya sa ta bi ni da addu'a"
  "Ba karamin tashin hankali yaya AbdulHakam ya shiga ba jin wannan labari mai munin haka zalika Fadilah ta dau fushi da ni a ganin ta ban yarda da ita bane bana son dan uwan ta har ce min tayi ba dan ta san irin gidan da na fito ba toh da ta ce kudi na bi dan na ga dan uwan ta bai da arzikin Asim haka bai da sanayyar mutani kamar Asim"
  "I was hurt sosai da aminiya ta ta min irin wannan bahaguwar fahimtar but ban ga laifin ta ba dan ko ni ce haka zan ce ko fiye da hakan duba da irin saurin switching da nayi"
  "Yaya AbdulHakam da kan sa ya zo ya same ni akan maganar da Abba ya mai ya natse akan yana so in fiddo mai da aibu kwara daya da yake da shi da nake gudun sa,but ban da amsoshin tambayoyin nasa ko guda haka na saka kuka ina hawaye shi kuma kamar zautacce yayi ta bi na da kallo har na gaji na tashi na bar shi a wurin"
  "A ranar na so sauya ra'ayi na akan aurn Asim but na kuma yin nazari sosai sai na share hawaye na na kawar da tunanin yaya AbdulHakam a rai na ina zaune a daki na ina jiyo sa daga kasa yana ihun ban da amana ban da yarda ni maciyiya amanar sa ce ya bani yarda da aminci amma na ha'ince sa ni da iyaye na"
  "i was crying profusely dan na ji zafin saka iyaye na a shirmen da nayi da yaya AbdulHakam yayi but ban da bakin magana,toh ashe Abba na jiyo sa sai ya kira sambo ya ce mai ya fitar da yaya AbdulHakam,haka ina hango su sambo ya zo ya fitar da shi da karfi"
  "Kwanar kuka nayi sannan a washegari ya kuma zuwa gidan namu still suka yi kokuwa da sambo ya ture shi ya shigo,haka yaya AbdulHakam yayi ta fade fade da zantuka marasa dadin ji,yayi ta maimaita ai Abba na maci amana ne ya hada kai da ni mun cuce sa bamu damu da feelings din sa ba bamu san ma'anar mutunci ba bamu san karfim yarda da amana ba"
  "It was a blast,dan Abba yayi losing temper din sa har ya mari yaya AbdulHakam ya riko sa rai bace ya ingiza sa waje sannan ya ce mai in ya kuskura ya kuma biyo mai ta hanyar gida sai ya hada sa da hukuma kafin shi yayi handling nasa properly"

TAMBARI[The dark hunt] Where stories live. Discover now