WATTPAD @SIYAMAIBRAHIM
Mental stability:Johari Window,this can be viewed as an aspect of ones self which completes that individual,it consist of four aspect wic gives a total description of ones personality.
9.Throw back III
SAUDAT HARIS
Mace ce mai tsananin son ado da kwalliya hade da tsafta,kwata kwata shekarun ta a duniya ashirin da tara wanda lokacin da ta kai shekaru ashirin da biyar daidai ta yi aure dan kwana uku ne cif tsakanin ranar bikin ta da ranar murnar zagayowar ranar haihuwar ta wanda nan ma mijin nata ya zage ya nuna mata farin ciki da taya murna ta hanyar providing nata da wani cute mini decorated cake..
Saudat Haris shi ne cikakken sunan ta,diya ta biyu ga Ambassador Haris Muhammad Matawalle da Professor Lubabatu Salami Matawalle.
Ambassador Haris Muhammad Matawalle mutum ne mai ilimi da ya sha gwagwarmayar rayuwa kuma ya taso cikin rashi da rashin gata sai dai free learning da aka kai masu yankin su na jam'are karkashin jagorancin gwamnatin garin Bauchi ya zamo masa garkuwa a rayuwar sa..
Duk da hali na babu da suka taso a ciki,hakan bai hana sa maida hankali ga karatun ba dan ya ba karatun muhimmancin fiye da yawon kiwon da yake fita yi tare da mahaifin sa a lokacin..
Duk kauyen an gama zunde da kushe masa dabi'ar da ya dauko ta karatun bature amma mahaifiyar sa ta rufe kunnuwar ta ta cigaba da bashi kwarin gwiwa ganin yana so kuma ta ji irin nasarori da aka ce wadanda suka yi karatun ke samu a nan gaba a rayuwar su sai ta ma dan nata kwadaiyin samin wadannan nasarori dan bata so ya taso kamar dabba da dabi'u irin ta mutanin yankin..
Da haka tun ana hantarar sa har aka daina aka cigaba da bin sa da ido dan abin ya shammace su a ganin su ai in suka taso sa gaba dole ya hakura ya bar bin tsarin baturen mutum ya dawo su yi ta zaman kiwo da kidahumanci kamar yadda suka taso suka ga ana yi a yankin nasu..
Da haka har yayi karatun sa ya kammala ya sami chance din cigaba haka ya karba sai dai wannan ya bambanta da na farkon dan wannan ya zame mai dole ya bar yankin nasu ya fita,inda a wannan lokacin yankin Ningi aka kai sa karatun gaba da primary da yayi,kaaancewar ba wani yawa gare su ba da suka yi karatun a kauyen nasu dan baau fi su biyar ba toh a yanzu su uku suka yarda su cigaba dan haka su ukun aka kai Ningi dan dora karatun su daga inda suka tsaya...
Rayuwar haka ta rinka tafiyar masu su ukun nan aka sami shakuwa mai karfi tsakanin su har suka yi karatun su suka kammala,kafin su baro makarantar sai da aka kwadaita masu cigaba da karatu dan an nuna masu ingancin sa dan haka suka yi shawara a tsakanin su akan in sun koma gida su nunawa iyayen su son cigaba da karatun suke dan suna sane da cewa jiran su ake su koma a hada su auren dangi da yanuwan su a zuri'ar su su kuma sun dandani boko burin su bai wuce su ga kididdigen abin da bokon ya kunsa ba...Da fari mahaifin Ambassador Haris Muhammad Matawalle ne da mahaifin daya abokin nasu mai suna Salihu ne kadai suka yarda yayin da daya abokin nasu mai suna Umar ya sanar da su mahaifin sa bai amince ba toh dama duk cikin kauyen mahaifin sa mai tsattsauran ra'ayi ne game da zafin rai,wannan karatun ma sai da aka sha fama sannan ya lamunta toh yanzu ya juye ya ce bai yarda ba..
Da aka nemo masu makarantar gaba da secondary after a successful result din su zuwa jami'ar Bauchi shi Umar na gida an mai aure da yaruwar sa an bashi garken shanu daya dan mahaifin sa akwai arziki in dai fannin dabbobi ne dan haka ya bashi garken akan ya rike gidan sa ba sai yayi dogaro da shi ba,duk da bai so ba bai da yadda zai yi haka ya aje karatun nasa ya koma kamar kowa a kauyen ya zamo makiyayi cikin makiyayan kauyen nasu...
A fannin su Ambassador Haris Muhammad Matawalle da abokin sa Salihu kuwa karatu ne tukuru a gaban su dan shi suka saka gaba inda shi Ambassador Haris Muhammad Matawalle yake karantar political science shi kuma Salihu yake karantar Economics..
A kwana a tashi ba wuya wun mai rai aka wayi gari suka kammala karatun su cikin nasara da sa'a dan sun fito da sakamako mai kyau,da farin ciki suka koma gida suka sanar da iyayen su aka rinka taya su murna,a karon farko a tarihin wannan kauye nasu an sami masu degree a karatu abin da ba'a taba samu ba sai dai a ji ana yi a makotan yankin..
YOU ARE READING
TAMBARI[The dark hunt]
HumorPeople round the world are being taunted and looked down on due to the feeling of misery and low self worth that is caused as a result of direct and indirect factors which gradually leads to so many social negligence and harassment in many situation...