Emerald

248 56 31
                                    

WATTPAD @SIYAMAIBRAHIM

Mental stability:Pica is an eating disorder that is characterized by an appetite of non nutritive substance like chalk,sand etc.

49.Emerald.

  Yana gaban mirror yana kallon ta tana ta turo baki gaba tana maganganu can kasa kasa sai yayi kamar bai gan ta cikin muryar bada umarni da jin kai ya ce da ita
  "Na gaya maki,kafin satin nan ya kare kiyi evacuating nan gidan ki koma gidan da na ce Amjad ya kai ki ki gani,kar ki bata min rai"!!ai kuwa a wannan karon da ya kuma nanata mata kalaman da yayi ta yi mata baitin sa tun dazu sai ta tunziri ta tashi ta zo ta tsaya mai tana jijjiga jiki ta ce
  "Ammar ka ji rantsuwar musulmi?toh ni kam Saudat Haris Matawalle babu inda zan tafi ni da gidan nan zama daram,oh so kake in koma can dan kai da amaryar ka ku rinka musguna min kuna min abinda zai rika bata min rai ko?da ka san babu su Hajiya a can in na koma right?toh ka je can ka mori gidan kai da amaryar ka amma banda ni Saudat dan ba zan tafi ba"!!tana gama fadan nata ta fita..

   It's been while da magana mai tsayi marar dadi irin haka ta shiga tsakanin su,toh mai dadin ma bai san rabon da su yi ta ba,a hakan ma marar dadin ya jima basu yi ta doguwa haka ba sai yau da ya mata maganar komawa sabon gida..
  Dage kafadun sa yayi shi dama yi mata yayi a matsayin ta na babba uwargida to become kafin Ummitah ta shigo dan kar ya fara rashin adalci tun kafin ta shigo gidan but kamar she is not interested ma tayin nasa so damuwar ta shi babu ruwan sa..
Karasa shiryawar sa yayi dan dama a dakin nasa ya kira ta dan a sami magana daya but aka ida da fada dan haka ya karasa shirin sa for long a cikin gida yake cin abinci dan irin fushin da yake yi da Saudat ba fushin da za a iya rarrashin sa a yanzu farat daya bane sai an jima..
  Mariam ce mai bashi abincin but itama tunda ya dauko maganar kara aure wa aunty ta Saudat sai ta daina girka mai,ya san dalilin ta amma ya kyale ta baya jin yana da lokacin ta da na kannen ta sai ya fita harkar su all he is after yanzu shine ya mallaki Ummitah and nothing but that. 

  Bayan ya fito ya karasa sashen iyayen sa ya masu gaisuwar safe sannan ya juya ga mahaifiyar sa ya dube ta sai tayi kamar bata gan sa ba..
  To her greatest surprise sai Ammar ya mata wani magana da ya saka ta juyowa ta dube sa..
  "Hajiya ban taba saba maki ba kuma bana fatar ranar da zan saba maki ta zo,in har auren nan bai maki ba,ina iya hakura amma zuciya ta zata cutu haka ni kai na zan cutu dan jihadi nake da niyar yi and nayi tsammanin zaki taimaka min mu yi tare,amma tunda auren bai kwanta maki ba,ban isa in cigaba da neman sa ba maybe ba alkhairi bane a gare ni"!!..
  Wani sanyi jikin ta yayi dan dama duk cikin yayan ta in aka cire Amira babbar yaya sai Ammar a hankali da hakuri kuma bai taba saba mata din ba kamar yadda ya ce but what if akwai alkhairi a auren amma ita take yunkurin tauye masa nufin sa na alkhairin?anya tana mai adalci kuwa?shin har ina matakin assurance din ta ya kai na zai iya cigaba da zama ba tare da ya bibiyi mata ba?tunda har ya sakawa ran sa toh mafi alheri shine ta bar shi ya je yayi abinda yake so ita kuma ta dage mai da addu'ar kwatanta gaskiya ko da ya auro yarinyar da yake da burin aura...
  Mahaifin Ammar ne ya dubi Hajiya Fulani sai ya bude baki da nufin fadin wani abin but yayi shiru ya bar ta kar ya shiga tsakanin ta da dan ta ya fi so tayi deciding da kan ta kuma bai gama tunanin ba sai ya ji muryar ta tana cewa
  "Allah ya sanya alkhairi Sadauki ya sa yin auren ya zama alkhairi ba akasin sa ba,kar ka manta baya kuma kar ka manta hallaci,Saudat mutumiyar arziki ce kai kan ka ka san da hakan,toh zai zama abu marar dadi a ce dan ka yi aure shikenan sai ka manta da ita,ka ji tsoron Allah ka kwatanta gaskiya Allah ya maka jagora kuma ya mana baki daya"!..
  Saboda jin dadin kalaman ta da addu'ar ta sai ya tsinci kan sa da fadada fara'ar sa ya amsa da amin sannan ya sallame su ya fita yana jin dadi ya hau bike din sa..
  Ya tayar kenan zai tafi sai ya ga Mariam ta fito ta nufi wurin motar ta nan kusa da shi,iya abinda ta iya ce mai shine
"Good morning"..baya mood din tsawatar mata dan farincikin da yake ciki tare da Ummitah ya kamata yayi sharing so he ignored her greetings ya ja bike din sa ya tafi...
  Ita kuma sai ta ga kamar fushi yake yi da ita dan haka a dame ta karasa beauty spa din ta,ranar tana abubuwa tana tuno yayan nata dan rashin amsa mata gaisuwar da bai yi ba ya taba ta..

TAMBARI[The dark hunt] Where stories live. Discover now