WATTPAD @SIYAMAIBRAHIM
Mental stability:General Paralysis of the insane(GPI)is a psychiatric disorder produced by syphilis and is the reult of a syphilitic meningo-encephalitis.
33.Superiority.
"My lord from this brief case study,it is clearly seen and proven that throughout the 5 years + stay that this client had was a terrible one very chaotic and tragic,and also the clear definition of my point "Domestic violence and abuse" is demonstrated in the life of this client,my lord,may i seek the honour of this court to grant me permission to have a word with mallaka Adamu the gate man of Bahago residence"?gyaɗa kai alkali yayi..
"Thank you my lord"..sai ta fuskanci mallam Adamu fuskar ta a dan daure babu alamar wasa ko wargi ta jefo mai unexpected question.
"Mallam Adamu kotu na tuhumar ka da laifin kisa,kisan kuma na uban gidan ka wato marigayi Asim idris Bahago,ya lamarin tuhumar take"?a rude mallam adamu ya hau barin jiki yana share zufa jin tambayar da ya daga mai hankali..
Cikin barin baki da kaucewar kalamai ya hau bayanin abin da ya sani a karshe ya dora da
"Ba ni na aikata wannan laifin ba kuma ina da tabbacin ba Hajiya ce tayi wannan kisar ba dan ba zata aikata hakan ba halin ta mai kyau ne"!gyada kai Saima tayi tana dora wata tambayar again da yayi thrilling mallam Adamu..
"Mallam Adamu idan har ba kai ka aikata kisar ba kenan ka yarda har a gurfanar da kai Noor ba ita ta yi kisan ba kenan"?idanun sa a waje yana kallon Saima ita kuma tana dage mai gira alamar shi take sauraro ita da kotu..
"Ran ki ya dade ki min rai sanin asalin wannan lamari sai lillahi ba zan iya ce maki eh ko a'a ba amma na fi inganta wannan zargi da da wani abin amma Hajiya bata da wannan zuciyar,zuciyar ta mai kyau be"!!kuma girgiza masa hankali tayi da wata tambayar...
"Mallam Adamu in ba ita tayi kisar ba kuma ba kai ka yi sa ba toh hakan na nufin da hadin kan ka aka yi hakan dan babu yadda mutani uku na gida daya ya rasu kuma duk biyun a ce babu saka hannun su,idan daya ya wanke kan sa dayan ma ya wanke toh wa ya aikata kisar?dole daya na da masaniya akai kuma that has to be you,kai,kai ne matsalar ta taso daga gare ka mallam Adamu"!!pausing ta dan yi duk aka zuba masu ido,sai bayan wani lokaci sannan ta cigaba
"Idan na yi amfani da rashin sanin ingancin aikin ka kar ka ga na maka karan tsaye but i must say,mallam Adamu baka san aikin ka ba,firstly kana da yawan shekaru wanda a matsayin mai kare rayukan jama'a a cikin gida irin wanda kake aiki shekarun ka sun rinjayi aikin ka dan idan mutani biyu zuwa uku ko ma daya mai jini a jika ya dumfare ka yana iya kawar da kai a tashin farko,ka ga kenan aikin ka tun fari hadari ne ga rayuwar jama'ar gidan madadin ka kare sai ka bada hanya aka far ma jama'ar gidan wannan rashin sanin ingancin aiki ne ciki har da laifin uwargidan ka Hajiya Sifa'u,secondly gangancin ka da kawar da kai ya sa ka bari kisa ya gudana a cikin gidan da kake tsaro ba tare da ka san wa yayi sa ba,laifi na uku ana tuhumar ka kuma kana jayayya ya kake so kotu ta yarda da kai a matsayin yardajjen dan tsaro kuma amintaccen mai kare jama'ar dake karkashin sa"??..
Lauyan dake kare Hajiya Sifa'u ne ya tashi yana nemar a gargadi Barrister Saima Aliyu dan tana shiga hurumin da bai dace ba tana firgita mallam Adamu tana son saka sa yarda da abinda ba shine ba hakan ya take doka da ka'idoji..
Calling attention din ta alkali yayi sai ta ce ta ji kuma zata gyara,daga haka ta hau zafafa tambayoyin ta akan lallai lallai sai mallam Adamu yayi providing ma kotu amsar wanda yayi kisar karshe dai sai da tayi losing temper din ta akan mallam Adamu ta daka mai tsawa da sai da ya firgice ta jefar da pen din hannun ta ta koma ta zauna ta dau ruwa cikin glass cup ta sha tana huci dan abin ya bakanta mata rai sam bata so case din nan ya dare yau ta fi so a yi sa a gama Ummitah ta sami freedom..Takaitaccen bayani alkali yayi yana tambayar ko akwai wasu hujjoji da shaidun da za a yi presenting ma kotu ta bangaren suspect,nan Barrister Imran Yarima Majidadi dake ta sauraron case ba tare da ya tanka ba ya tashi yana gyara rigar sa ya ce da alkalin akwai wasu shaidun da ba directly zasu fadi abinda ya faru a ranar ba amma suma shaidu ne akan abubuwan da ya faru a rayuwar auren Ummitah so alkali ya bashi iko..
"Kotu na bukatar ganin Ammarudden Kallamu da Mrs Bianca José"!!gaban Hajiya Sifa'u ne ya fadi dan bata san da wadannan mutanin ba ya zata kare kan ta yanzu...
Duk sai da kotun ya natsa sannan Ammar dake zaune tsawon awowi yana sauraron shari'a cikin mamakin irin bakin rayuwar da Ummitah ta kasance ciki,bai taba sanin asalin sunan ta ba sama da Mrs Bahago toh yau ya ji sunayen ta duka _Noor da Ummitah_ har da surname din ta abin ya bashi mamaki ba kadan ba..
Zuwa yayi ya tsaya a inda aka tanadar dan masu bada shaida,Ummitah kan ta na kasa amma jin sunan da aka kira sai ta dago dan ganin wani Kallamu ne,wanda ta sani mai tsare ta a harabar wun aikin su ne ko dai wani Kallamun ne..
Tantancewa ta dago fuskar ta dan yi sai ta ga shine abin sa sai ta bi sa da kallo har ya kai inda zai tsaya ya bada shaida.
Hada ido suka yi da ita sai ya mata murmushin da zai karfafa mata gwiwa sannan aka tambaye sa sunan sa da alakar sa da suspect..
"Sunana Ammarudeen Kallamu ban da wata alaka tsakani na da wannan matar sama da alakar staff and client dan a eatery din su nake siyan abinci nake kuma placing order"!shiru yayi yana sauraron wata tambayar sai lauyan Hajiya Sifa'u ya jefo masa tambaya
"Menene a tsakanin ku da juna da har ka ga ya dace ka zo ka bada shaidar ka akan ta bayan ka ce baka san ta ba"?amsa Ammar ya shiga bashi..
"Kimanin shekara daya kenan da na san wannan matar hasalima ban san sunan ta ba sai yau da na ji ana fada,duk zuwa placing order din da nake yi ban taba lura da ita ba sai a wata tafiya da nayi na siyo abinci sai da na zo fita muka hadu a kofar fita sai na ga kamar fuskar ta na bace ne da shaidar duka,hakuri na bata na wuce,toh tun ranar sai na rinka tunanin kamar daga inda take aiki ne ake takura ta sai na tuntubi matar amma ta shaida min ai haka kusan kullum take zuwa aiki tun daga lokacin na fuskanci daga gida take zuwa da wadannan Tambarin dukan sai na rinka bibiyar ta tun bata sauraro na in na mata magana har ta kai ta kawo in na gan ta da wani tabon nakan tambaye ta bata wuce ni takan tsaya ta saurare ni sai dai bata taba amsa min ba kullum sai na tafi na duba ta dan sanin halin da take ciki amma bata yarda wata magana mai karfi ta shiga tsakanin mu a haka ne na rinka fuskantar takura ke damin ta a gidan mijin ta sai wataran haka na ga ta kwana biyu bata je aiki ba nayi tunanin tambayar madam din su sai ta sanar da ni duk wani abin da zan bukata zan samu daga wun abokin mijin ta da haka na rabu da matar na roki daya daga cikin ma'aikatan wurin ta min monitoring din abokin mijin wannan matar hade da bata number na akan in ya zo ta sanar da ni,but haka kullum tun ina saka rai har na hakura,sai kuma rannan na shirya na koma dan rokor madam din akan ta sanar da ni toh kafin in tafi ne na ga labaru akan wannan matsalar sai na tafi na sami madam din ta itama ta sanar da ni abinda ta sani akan case din,tun ranar na rinka kai kawo dan samin wasu update akan lamarin,ranar na tafi zan wuce kenan sai na hadu da wannan Barrister din a nan na san cewa shima evidence yake tattarawa akan case din sai na sanar da shi nima ina son shiga case din sakamakom sanayyar da na yiwa suspect din,ana haka ne sai na kai mata ziyara ana saura kwanaki a zo nan kotu,a ranar ta sanar da ni abinda ya faru a ranar,iya abinda na sani kenan kuma ni ina da tabbacin ba ita ta aikata wannan abin ba dan bata da wannan halin a iya sanin da na mata sai dai in akwai wata a kasa amma wannan kisar bata da masaniya akan sa kamar yadda ta ce"!!yana direwa Hajiya Sifa'u ta hau bala'i ita duk babu ruwan ta tunda dai an gama zagaye zagaye an zago babu wanda ke da tabbacin wannan kisa ba ita ta yi sa ko mahaukaci ya ga lamarin dole zai san ita ce so all she wants is justice for her late son..Da kyar aka yi calming nata su kam masu shaidar Ummitah suka rinka mata kaskantaccen kallo har alkali ya gama rubuce rubucen sa yet yayi granting another chance a kawo shaidu idan da akwai su nan Barrister Imran ya kuma gabatar da Mrs Bianca tayi nata bayani irin zaman mutuncin da suka yi da juna da kyawawan halayyar Ummitah itama ta dora da sam bata yarda Ummitah zata aikata hakan ba..
Still Hajiya Sifa'u ta tayar da rikici ita sam bata yarda ba sai dai a yi mai yiwuwa nan kuma kotu ya rikice ya hargitse ana ta tafka muhawwara with much disparity akan ba a ma Ummitah adalci ba so a samo mata saukin zuciya a yi shari'a daidai da doka..
Haka muhawwara ya rinka gudana cikin kotun nan karshe alkali bai da zabin da ya wuce dage zama zuwa sati biyu masu zuwa..
Sam wannan shari'a bata yiwa Hajiya Sifa'u ba dan haka ta fadawa alkali ita sai dai ya bar ta ta kai kara inda za a share mata hawayen ta wato appeal cout since this is a federal high court..
Wani rikicin ne ya kuma kaurewa a kotun dole alkali ya yarda da burin Hajiya Sifa'u wanda su kan su Barristers din hakan ya masu dadi dan suna da target akan Hajiya Sifa'u wanda bata san da shi ba ita kan ta dalilin da ya sa suka ki karasa bayyana shaidun su suka tanadar ma appeal court dan dai su azabtar da hankali da zuciyar Hajiya Sifa'u ba wai dan basu da abin yi ba a nan din..
In conclusion haka aka dau Ummitah aka yi hanyar mota da ita dan maida ta zuwa cell tunda ba a gama case ba kuma Hajiya Sifa'u ta ce bata yarda a bada belin ta ko da na second daya bane,basu ja da ita ba aka bar batun..
Fadilah dai kamar zata haukace ma mijin ta da aminiyar su Saima sai ta rinka fada wai sun hadu a wuri daya sun kasa aiwatar da komai ita da ta san haka zasu mata da ba zata saka hope din ta akan su ba....
Da kyar Imran ya tausa ta ta shiga mota wai ko zata natsu ya mata bayani amma ina sai kara bircike mai take yi he had no choice but to start the car ba tare da ya gana da su Ammar ba yana gaba Barrister Saima na bin sa a baya da motar ta har suleja kasancewar a gidan Fadilah zata kwana har washegari da zata koma gombe..
Ranar sai da aka kai ruwa rana da Fadilah kafin a sami kan ta aka mata bayanin technique din da aka yi adopting ba dan komai ba sai dan a nunawa Hajiya Sifa'u kudi ba zai mata komai ba ciki har da bata burin ran ta da take muradi na yankewa Ummitah hukuncin kisa..
Da kyar ta iya bacci a daren bayan koke koke da tashin hankali,Saima da Imran sai a late hours suka kwanta dan zafafa binciken su da suka kuma yi akan case din dan sun san ko nawa Hajiya Sifa'u zata kashe zata yarda ta kashe sa kawai dan ta sami biyan bukatar ta su kuma sun fi son haka if possible in suka tafi nan din ma su kuma zafafawa ta tunzira ta kai supreme court inda suka san tas kusan duka kadarorin ta zata karar,wannan wata dabara ce ta punishing din ta silently tunda ta fi karfin Ummitah a zamanin zaman su kuma ta zalunce ta zalunci mai muni toh wannan ne kadai hanya mafi sauki da zasu hukunta ta ba tare da an san tana azabtuwa a cikin zuciyar ta ba...★★★
Tun bayan barin su Ammar court suka kama hanyar komawa gida,hankalin sa baya tare da shi dama a flight mood ya saka wayar sa dan kar Saudat ta kira sa,shi dai Amjad yana ganin ikon Allah yayan sa involved in court case abinda bai taba gani ba amma who is he to confront him akan me ya sa yayi involving kan sa a wannan shari'ar..
Har suka dawo gida Ammar kamar kurma,tambayar duniyar nan Saudat ta mai akan me ya same sa da ya fita amma haka ya kyale ta da ma ta dame sa sai ya sauya kayan sa zuwa na bacci ya wuce zuwa daya dakin yayi kwanciyar sa,kwatakwata brain din sa ya tsaya da aiki,ta yaya a ce mutum mai rai da jini a jiki ya tsaya yana enduring irin wannan hardship da torture din dama irin haka na faruwa a duniya,bai taba gani ba...
Ba karamin daga mai hankali wannan case din yayi ba kasa baccin arziki yayi sai tunanin ya rayuwar Ummitah zai kasance ko za a yanke mata hukuncin ko zata tsira,ya iyayen ta zasu ji in wannan labari ya riske su,also he is disturbed akan dalilin da Ummitah ta kira da shine dalilin da ya sa take hakurin zama da mijin nata,ya damu da son sanin menene wannan abin kamar yadda Hajiya Sifa'u tayomi tagging abin da Tambari..
Sai da ya fuskanci kan sa na gab da bugawa sannan yayi forcing kan sa baccin tilas ba dan ya so ko ya shirya ba ai ko yayi mafarke mafarke marasa dadi a baccin,da Allah ya bashi ikon farkawa kuwa bai tsaya wani tunanin ba ya je yayi alwala ya zo yayi sallah ya rinka addu'ar rahama da ni'imar ubangiji ga Ummitah dan tausayin ta da yake ji baya ganin yana iya enduring ganin hukuncin da za a yanke mata,he just pray for Allah mercy for Ummitah,all night prayers yayi har subhi kafin baccin asali ya dauke sa....#GPI has an onset between the ages of 30 and 45 years,it clinical features include sexually and emotionally disinhibition,lack of initiative,irritability,memory defects etc,the management include early detection in other to arrest the progress of the disorder,use of drugs,occupational and social adjustment,prevention of pitiful state of physical enfeeblement..the earlier the treatment the better the outcome..
YOU ARE READING
TAMBARI[The dark hunt]
HumorPeople round the world are being taunted and looked down on due to the feeling of misery and low self worth that is caused as a result of direct and indirect factors which gradually leads to so many social negligence and harassment in many situation...