Judgmental act

261 53 8
                                    

WATTPAD @SIYAMAIBRAHIM

Mental stability:Hallucination is refer to perception of external object when no such object is present.

28.Judgmental act
9am

  "Qurratul ayn tashi ki ji wani labari mai dadi da na zo maki da shi kar ki ce a'a"!!Barrister Imran kenan yayin da yake ta tapping matar sa Fadilah akan ta tashi ta saurari abin da ya zo da shi..
  Fadilah da ke faman baccin huce gajiyar aikin da mijin nata ya saka mata tun jiya har dazu sai ta juya position din baccin nata tana fadin
  "Imran ka rabu da ni haba kai baka tausayi na ne wai?tun fah jiya ina ta aiki har dazu instead of you as a good husband to pamper me wai kuma kai ke nemar takura ni,kai Imran tausayin ka gare ni ya ragu"!!da kyar ta ida sentence din daga nan kuwa shiru Imran ya ji sai yayi dariya yana mai juya channel din dan an gama abin da yake so ya nuna mata...
  Dawowa bayan ta yayi ya fara massaging mata kafafun ta yana ta tsokanar ta ta hanyar yi mata tafiyar tana but bai ga tayi responding ba sai ya cigaba da yi mata tausar yana dan kallon tv din time to time...
  A cikin baccin take ta jin relieve a hankali sai ta dan bude idanun ta ta juyo ta gan sa,kashe mata ido daya yayi yana dage mata gira saibta ki yi mai godiyar ta kyale sa ta koma ta kwanta,dariya ya kuma yi mata yana mai cigaba da yi mata tausar...

  Har baccin ya kuma fizgar ta sai ta ji ya dakata,da kyar ta ce mai
  "Imran me kake yi ne wai haka?dakatawa kuma ka yi ne"?sai ta ji shiru nan ma cikin bacin rai ta juyo da nufin masife sa amma sai ta ga hankalin sa ba a kan ta yake ba sai kan tv..
  Jijjiga shi ta rinka yi sai yayi firgigit ya juyo a rude yana kallon ta,ta bude baki kenan dan tambayar sa me ya sa ya daina yi mata massage sai ta ga ya kawo hannun sa da sauri yana lalubar remote ita kuma ta cigaba da bubbuga sa ko kafin ta sani kunnuwar ta suka jiyo mata wata suna da ya daki kirjin ta...
  Juyawar da zata yi ga tv din sai ta ga americans ne suka yi appearing a screen din,abin da ya daure mata kai kenan,nan take brain din ta ya bata wani perception da sauri ta kalli Imran din tana zazzaro idanun ta waje hade da furta
  "Me na ji yanzun nan Imran?sunan wa na ji a tv di nan yanzu yanzu?ina channel din"? a rude Imran ya hau in ina yana son sauya akalar tambayar nata amma ta riga ta ji sunan dan haka ta fizge remote din dake hannun sa ta hau yin gaba amma bata ga komai makamancin hakan ba sai ta fara dawowa baya ta ga Newsline sai ta dakata ta maida hankali da idanun ta ga news headlines din dake wucewa a kasar screen din...
  Riko hannun ta Imran yayi amma ta fizge hannun ta tana banko mai harara tayi saurin maida duban ta ga screen din..
  Natsuwar ta duk ta maida kan screen din tana karantar news headlines din idanun ta cike da hawaye..
  Bata tsinke da lamarin ba sai lokacin da ta ga headline din da take son gani an yi mai inkiya da "Wife killed husband last night at 12:45am in the Bahago's residence"..

  Dum!!!gaban ta ya bayar hankali tashe ta sauko daga kan gadon ta fara laluben wayar ta tana son ganin last call din ta da Ummitah dan sanin ko ita ce ko ba ita ba ce..
Shi kam Imran ya gani kuma baya bukatar wani tabbatarwa ya san ita ce dan har hoton ta aka nuna gefe kuma hoton Asim..
 
kiran layin ta hau yi haka yayi ta ringing ba a daga ba abin ya dada rikita mata lissafi,Imran na kallon ta dan bai isa ya hana ta ba yanzu yanzu sai ta sauya daga Fadilah his noble wife zuwa wata irin wild Fadilah..
Jefar da wayar tayi a kasa ya fadi ya kwankwatse,take Imran ya matso ta ya janyo ta jikin sa kar bacin ran yayi yawa ta aikata abin da ya fi wannan muni..
  Kuka ta fashe da shi tana cukwuikuye masa rigar sa tana ihu tana sambatu kamar zautacciya..
"Imran amma ka san ai Ummitah ba zata taba aikata wannan abin da ake tuhumar ta da shi ba ko?aka ce wife killed husband kuma a Bahago's residence toh in ba Ummitah da Asim dake cikin gidan a matsayin ma'aurata ba wa ke gidan?mother In-law din ta bata nan tayi tafiya,Adam mai gadin gidan matar sa na garin su toh in ba Ummitah ba wa ake zargin zai yi hakan?Imran ai ka dai san sharri ake son yi mata ko?duk fushi da zuciyar ta ba zata taba aikata hakan ba,ko karamin halitta Ummitah bata son kashewa ta yaya za a mata sharrin kisa,kisan ma na dan adam kuma wai mijin ta"!!duk bata san me take fada ba sai da Imran din shim ya taro jarumta ya bata magana..
  "Fadilah i know,i know it's not real,definitely an sami akasi,coincidence do occur na san an sami coincidence ne ba ita tayi kisar ba,yanzu ki taimake ni ki kwantar min da hankalin ki ni zan tafi in yi sourcing informations da full details akan abin da ya faru kin ji"!?
  Girgiza mai kai kawai ta rinka yi akan ba zata jira sa ba sai dai su tafi tare,bai da zabi da dai zata haukace me is better ya tafin da ita in ya so sai ya kulle ta a mota..
  Raba jikin sa da nata yayi ya nemo mata hijab din ta ya miko mata ya fito zuwa dakin yaran da ya sama suna ta wasar hide and seek ya tattaro su ya saka a mota sannan ya dawo ya riko Fadilah suka fito zuwa motar..
  A motar ma yana tuki amma sai complaining take ta yi akan baya sauri,in ta tuno wasu events din kuma sai ta hau sa da fada akan ai ta dade da sanar da shi plan din ta akan ya shigo lamarin aminiyar nata tun abin bai yi muni ba amma ya ki shigowa saboda ba matar sa bace ita..
  Shi dai yana tukin sa yana jin ta dan baya bukatar a mai bayanin wacece Fadilah in tayi fushi,shi fargabar sa bai wuce kar sai sun tafi gidan ta birkice mai ba ya kasa yin abin da zai yi..

TAMBARI[The dark hunt] Where stories live. Discover now