WATTPAD @SIYAMAIBRAHIM
Mental stability:Mongolism is a mental disorder that is associated with brain defect wic usually developed from intrauterine life that posts an issue of concern in later life.
51.His care(my remedy).
Da sallama Ammar ya shiga parlorn Ummitah na bin sa a baya,yayain da Hajiya Fulani ke zaune ita da Mariam suna hira,gefe guda kuma,mahaifin su Ammar ne zaune yana karatun wani jarida,jefi jefi yakan saka baki a hirar tasu..
Sallamar Ammar ne ya ankarar da Mariam dake kokarin ba Hajiya amsar tambayar da ta mata..
'Wa'alaikumul salaam yaya na"..ta fada tana kokarin leka wacce ke bayan sa.
Karasa shiga parlorn yayi yana ma Ummitah iso,nan Hajiya Fulani ta maida duban ta ga bayan Ammar tana son ganin Ummitah itama..
Kai a kasa Ummitah ta yi sallama muryan ta na kasa,amsawa duk suka yi suna jiran zaman su..
A natse Ummitah ta zauna a kasa tana mai gaida Hajiya Fulani,ba yabo ba fallasa ta amsa tana tambayar ta ya jama'ar biki ya bakunta..
Amsa mata Ummitah tayi kan ta a kasa tana murmushi sannan ta gaida mahaifin Ammar nan shima ya amsa mata yana mata barka da shigowa ahalin su hade da yi masu fatar alkhairi da zaman kumana mai dorewa..
Sai da ta gama gaisuwar sannan Ammar yayi nasa daga nan Mariam ta gaida sa ta gaida Ummitah tana leken fuskar ta babu kunya wai ko zata ga makutsar ta sai dai bata sami damar ganin fuskar nata ba dan bata daga kai ba bare a kare mata kallon.Yar hira suka yi da Ammar ita dai tana nan zaune bata ce komai ba,abinci aka kawo masu Ammar din ne dai ya ci ita bata ci ba,har suka gama hirar tasu suka shiga ta kasuwancin daga bisani ya tashi yana sallamar su dan zasu koma gida.
Nan kuma iyayen suka masu nasiha suna nuna masu muhimmancin aure da sanin darajar sa da daukaka sa..
Har sashen Saudat Mariam ta raka su tana baya baya kusa da yayan nata tana tambayar sa wai me ya sa matar nasa bata bari sun ga fuskar ta ba..
Dariya ya mata yana mamakin dalilin ta na matsuwa da tayi akan lallai lallai sai ta san ya kamannin Ummitah yake..
"Mariam yaushe kika fara son auntyn naki har haka!?i thought kina taya Saudat fushi da ni ne"?nan kuma tayi shiru dan ta rasa abin cewa sai ta zame jiki ta wuce ta koma sashen su..
Matsowa kusa da Ummitah yayi zai riko hannun ta sai ta janye tana girgiza masa kai,alama ya mata da ido akan ta bari mana ita kuma ta share sa dan ta san inda zasu tafi wato wun uwargidan sa,in kuma a haka yake so su shiga toh bakin tambari zai janyo mata a idon Saudat ita kuma ba haka ta shirya fara sabon rayuwar ta ba..
Sai da suka zo dai dai kofar parlorn Saudat sannan Ammar ya kama kan sa ya hade fuska ba kamar dazu ba..
Ita dai Ummitah ba wani kallon sa tayi ba,yana gaba tana bin sa a baya ya mata jagora suka shiga ciki..Babu kowaa parlorn sai tv dake kunne dan haka ya ce da ita ta zauna bari ya je ya kirawo Saudat din..
Zama Ummitah tayi a kujerar zaman mutum biyu tana gyara lullubin ta a kan ta..
Tura kofar bedroom din ta yayi sai ya hango ta tana cire dan kunne,tsura mai ido tayi daga mirror din da take kallo..
Admiring mijin nata take yi wanda yanzu ya zama su biyu ke sharing nasa ba ita kadai ba..
Hawaye ne ta ji yana son zubo mata sai ta kawar da idanun ta daga kallon sa ta maida wani gefe sannan bata cigaba da abinda take yi ba..
Likewise a nasa fannin ma,zuciyar sa na masa wani iri na haramta mata kan sa da yayi ta yi for long,sai ya ga kamar hukuncin da ya mata yayi tsauri da yawa,tausayin ta ya kama sa sai ya karaso dakin ya zo daidai bayan ta ya durkuso ta yadda zai iya hugging nata daga bayan da kyau..
Ji tayi ya bata tight hug yana shinshinar gefen wuyan ta,lumshe ido tayi hawauen ta na son fallasa sirrin zuciyar ta.
Kasa furta ko da uffan tayi sai shirun da ta mai tana sauke ajiyar zuciya,sun jima a haka kafin ya ce da ita cikin kunnen ta.
"Yafa mayafin ki ki zo mu tafi parlor tana jiran ki"!!wani bugun dalma ta ji a kirjin ta yayin da ya kira mata sunan wata da inkiyar "tana jiran ki"..
Daurewa tayi kamar yadda Ummin ta ta koya mata akan in tana so ta ci ribar zama da Ammar kuma ta more sa ya cigaba da ganin ta da kima kamar da ko fiye da da toh dole ta kama ajin ta ta san girman ta zai daukaku ne a idanun Ummitah da mijin ta in har ta kama kan ta ba wai tayi ta fushi da nuna kishi kamar wacce bata yi karatun boko da na islama ba...
YOU ARE READING
TAMBARI[The dark hunt]
HumorPeople round the world are being taunted and looked down on due to the feeling of misery and low self worth that is caused as a result of direct and indirect factors which gradually leads to so many social negligence and harassment in many situation...