WATTPAD @SIYAMAIBRAHIM
Mental stability:Phobia is an exaggerated or irrational fear or dread of a particular object or situation,it occur on it own or in association with other neurotic symptoms.
For u my YorubaFulani sweetheart Àjóké Aisha Aliyu,my hrt dey beat lyk Dúdúke Du-du-ke for u😍🌹
14.Trip to Zariya
Da azababben ciwon kai ya tashi kamar ba a jikin sa kan yake ba,idanun sa runtse ya tashi yana rike kan da hannun sa biyu,sai a lokacin yake kara jin zafin radadin ciwon kan dan haka ya dan dakata ya jingina da gadon yana mai dora tafin hannun sa bisa goshin sa..
For a moment yayi shiru yana tariyo kalaman mahaifiyar sa na jiya kafin su rabu,ba komai yake tunowa ba sai barazanar da ta rinka mai akan zaman sa da matar sa because ya fi kowa sanin halin ta in har ta juye zuwa mood din yoruba din nan toh da kyar ba za'a tsinci sakamako ba,in hakan ya faru kenan zata iya cutar da ita kan ta Noor din..
Tuno hakan sai yayi sauri ya sauko daga kan gadon forgotten that kan sa na masa ciwo..
Wani irin mugun jiri neya dibe sa ai ko bai ankara ba sai gashi a kasa yana numfashi da kyar kamar zai gangara..
Nishi yake yi yana yunkurin tashi but jiri ya mamaye mai idanun sa dan haka ya rinka kame kame..
Turo kofar dakin aka yi sai yayi ido hudu da mahaifiyar sa da abincin safe ta kawo masa dan ganin kamar jiya tayi overreacting masa,shi yasa ta zo da kan ta dan ta bashi hakuri ta rarrashe sa in ya so sai su tafi a nemo Noor din...
Da sauri ta karaso ciki ta ajiye tray din abincin a gefe ta karaso gare sa tana ta addu'a a zuciyar ta kar Allah ya dauke mata ran shi shi kadai gare ta a halin yanzu..
Da zuwan ta ta durkusa ta rungumo sa jikin ta tana ta shafa fuskar sa tana jijjiga sa hade da magana cikin yaruka uku tana fadin
"Oluwafemi kílódé?ehn?tõfúmí kílón sélé?Femi talk to me noww??me ke damin ka ne wai?is it me?ehn?ni ce?akan maganar da na maka ne jiya?na janye ka yi hakuri ka tashi kar ka tafi ka bar ni na rantse maka zan saka a nemo maka Noor i promise you Femi,please don't leave me kai kadai ne gare ni daga kai sai kai,duk yan uwa na ba so na suke ba,har mahaifiya ta ba so na take ba she contributed to your fathers dismay she is responsible for my husband's death,her dark hunt is now hunting me,ta bar min bakin Tambarin da na zan iya manta shi ba,da na Asim...,ka tashi kar ka tafi"!!!ko kafin ta gama maganar hawaye ya wanke mata fuska kamar me..
Shi dai yana sauraron ta but wannan narrating labarin da ta masa ba shi bane a gaban sa dan ya taso da sanin mahaifiyar nasa na da raunin imani,ita duk abin da ya same ta a rayuwar ta toh ba yin Allah bane definitely yin wani ne dan ta taso a ahalin da suka daukaka man made disaster akan natural disaster(meaning ko da abu ne ya faru da mutum ko karayar arziki ko kaddara toh sam basu alakanta hakan da yin ubangiji ne sai an rinka tracing mutani har a gano makiya daga nan a fara sabon bincike da dube dube akarshe a lakabama wani a ce ai shine sanadi sam basu yarda da Allah ba)..
A sanyaye ya dago kwayar idanun sa ya dora bisa fuskar mahaifiyar sa yana kallon ta duk damuwar sa shine ta zamo sanadin silar haduwar sa da matar sa..
Magana ya fara kokarin yi da raunanniyar murya yana son ta bashi full attention din sa dan sami hope.
"Momma...Momma please..stop all these incantations...i need a way out,,just find my wife please..ki nemo min ita dan wallahi hakkin ta ba zai bar ni ba,i never for once have the intention of bullying her after our marriage,,i swear...my wife...my wife"!!!..
Kamar zautacce haka ya rinka magana yana nanatawa wanda hakan ya ankarar da zuciyar Hajiya Sifa'u ta ji duk duniya babu wacce ta tsana sama da Noor kenan ita ce silar hargitsewar tunanin dan ta daya tilo?lallai zata gwadawa Noor farau farau bata shayi...
Rai bace ta sauke kan sa daga jikin ta ta tashi tsaye tana huci tana kallon sa kamar ta zaro zuciyar sa ta cire duk wani part da sunan Noor ya taba ta wanke sa tas sannan ta mayar mai da shi,sai dai duk da hakan ba zai faru ba a zahirance,she will make sure ta yi hakan a badini in dai ta haifu cikakkiya a zuri'ar mahaifiyar ta na yoruba kuma akwai blood din a jikin ta..
Fita tayi tana mai banging kofar dakin kamar zata balla,a haka ta rinka tafiya kamar kububuwa har ta iso sashen ta ta hau laluben wayar ta..
Tana hango wayar ta saka hannu ta dauka ta shiga sashen contacts inda a nan ta fara nemo wata number..
Ba jimawa tayi arriving kan numbern da aka saka mata "TEMI TOPE"...
Kira tayi yayi ringing na farko har ya katse ba'a daga ba sai da ta sake kira sannan aka daga daya bangaren aka ce
"Elo,,ékáro mummy"!.bata tsaya jin cigaban gaisuwar ba ta hau maganar ta
"Tope,,kanin ki Femi ya fada a tarkon wannan élegusí beach din nan,he has fallen completely in her trap,can you believe that tun safen jiya har safen yau Femi couldn't put him self together"?tayi maganar tana karasa shi da yoruba tongue..
Daga daya bangaren wace suke wacce suke wayar tare mai suna Temi Tope ta ce
"Kílòn sé?níbó?báwó ní mummy"...
Nannauyar ajiyar zuciya Hajiya Sifa'u ta sauke sannan daga bisani ta hau warware mata komai ba tare da shakka ko dar ba...
Tsaf Tope ta gama sauraron zantukar ta har ta dire sannan ta ce
"Mummy toh ya kike so a yi yanzu"!!..da zafin rai ta ce
"Anything Temi Tope anything"..cikin karaje Tope ta ce
"Ótí tó mummy in specific what did you want us to do"!?babu jira ta ce
"We are travelling to Ogbomosho"!!wani irin ihu Temi Tope tayi tana fadin
"Ahhh..mummy...nooo haba mummy..rárá...I can't ba zan iya ba ehhhn no mummy ki canza tunani no i can't"!!!wani tsawa Hajiya Sifa'u ta daka mata tana fadin
"Tope...is it me you are responding to like this??are you mad??ni kike ba amsa haka??ba zaki tafi ba in canza tunani kika ce"??jiki na bari Tope ta amsa mata da
"A'a mummy..ba nufi na ba kenan"!!cikin katse hanzarin ta ta ce
"Then me kike nufi da you can't da kika ce"?da sauri ta ce
"Mummy am pregnant...you know i can't go there..."!!still katse ta Hajiya Sifa'u tayi cikin tsawa
"And so if you are pregnant"?da sauri ta amsa mata
"Mummy fadin ancestors din mu ne fah me ciki ba a yarje mata ta rinka visiting wurare irin haka ba musamman in tana da tsoho ciki dan is very possible ana iya amfani da abin dake cikin ta a sami biyan bukata shi yasa nayi wannan maganar"!!rai bace Hajiya Sifa'u ta ce
"Ke har kin yi girman da zaki na tsare lafiyar dan dake cikin ki akan biya min nawa bukatar Tope?yaushe ke na gama rainon ki har kika yi auren?ohh i see..hahh ni Sifa'u...hmmm Tope ki kiyaye ni if not sai na maki mugun abin da baki taba tsammani ba i swear on my husband's grave"!!!da sauri Temi Tope ta tare ta ta hanyar fadin
"Mummy ki yafe min...ki yafe ni i take back my words ki yafe ni"..kwafa Hajiya Sifa'u tayi tana mai revealing ma Temi Tope plans din ta da yadda zata cire ma dan ta soyayyar matar da ta ma lakabi da élegusí beach(mai siyar da miyar egusi a beach)..
A karshen batun nata ne tayi wani irin mugun shahada da sai da Tope ta ji abin ya girgiza ta dan kuwa cewa tayi
"Tí mì o bá fí ódí kéjimi hón Noor àjéwipe éjé Alaja Kudiratou Olayinka kó nímí,Móma só ómò yè nú"(meaning in ban nunawa wannan yarinyar dayar fuskata ba toh ni ba jinin Alaja Kudiratou Olayinka ba ce,na rantse na tabbatar sai na batar da yarinyar nan)...
Kara dorawa tayi da shahadar nata na fari
"I'll lost that girl"..da huci ta ida maganar kamar ga ta ga Noor din duk da irin mugun shirkan da Temi Tope ke yi she has never ever tried this in her life wai tana da ciki sannan ta yi mugun tafiya but yau gashi uwar goyon ta na mata barazanar ko ta bi ta da lumana ko ta gwada mata mugun hali,wannan kankani ne cikin bakaken zuciyar Hajiya Sifa'u ta sani dan haka ta yarda kawai dan ita kan ta tasowa tayi ta gan ta cikin wannan halin toh dan me zata bari uwar goyon ta salwantar mata da baby...
"Mummy yaushe zamu tafi"?Tope tayi mata tambayar..
Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta amsa mata da
"Gobe"!!gyada kai Tope tayi kamar Hajiya Sifa'u na kallon ta kafin ta ce
"Toh Mummy sai goben bari in fara shiryawa"daga haka suka yi sallama Hajiya Sifa'u tayi cilli da wayar tana ayyana yadda zata wulakanta Noor dan ta shiga rayuwar dan ta da yawa..
"Zaki gani mu zuba ni da ke,haifaffe shi ke karbar kambun nasarar gasa"...
YOU ARE READING
TAMBARI[The dark hunt]
HumorPeople round the world are being taunted and looked down on due to the feeling of misery and low self worth that is caused as a result of direct and indirect factors which gradually leads to so many social negligence and harassment in many situation...