WATTPAD @SIYAMAIBRAHIM
Mental stability:Mental Retardation is an organic disorder which is present at birth or early childhood usually characterized by limited intelligence.
19.Family goals
Kamar barawo ya rinka bin hanya a hankali har ya kawo sashen nata ya bude kofa ya shiga,karo yayi da yan aikin gidan zasu fara aikin su na safe.
Gaida sa zasu yi amma yayi saurin tarar su yana mai yi masu alama da mahaifiyar sa ta tashi..
Da kai suka amsa mai dan haka ya haura saman ya nufi dakin ta direct da sallama a bakin sa..
Ko da ya shiga bata ciki dan haka ya hau barbaza idanun sa ko zai yi katari ya ga waya ko da ba nashi wayar bace..
Yana tsaye yana kan kalle kalle sai ya ga wata karamar waya dan haka yayi saurin karasawa ya dauko wayar,yana tsaye kamar yayi abin da yake son yi ya mayar da wayar but wani tunani ya fado masa dan haka ya fita kawai ya dawo nasu sashen...
Phone book din sa ya dauko ya duba wata number yayi dialing cikin sauri sannan ya kara a kunnen sa..
Jim kadan aka daga wayar,kafin a yi wani magana ya riga fara yi ta hanyar gaisuwa daga bisani ya hau labarta abin dake faruwa da shi da kuma barazanar dake fuskantar rayuwar auren sa da matar sa.
Ko me aka ce,sai ya amsa da sanyin murya kamar bai so amsar da aka bashi ba.
Kashe wayar yayi ya fita ya kama hanyar sashen mahaifiyar sa nan ma still bata nan,so he returned back the phone and left...Wanka yayi ya kimtsa kan sa ya shirya da zumar tafiya wun aiki with the hope of whiling off his problems ko ba duka ba.
A nan part din mahaifiyar sa yayi breakfast shi kadai sannan ya tashi ya kuma haurawa duba ta,sai a sannan ya gan ta suka gaisa ta mai ya jiki ya amsa sai ya ce mata aiki zai tafi ta mai fatar alkhairi game da kara jaddada mai accounts din sa are freeze dan haka kar yayi wasa da ita ta hanyar zuwa ya sa a bude masa wasu dan zata mugun saba mai,gyada mata kai kawai yake ta yi dan ba kan ta hankalin sa yake ba,tana gamawa ya tashi ya mata sallama ya fita,motar sa ya shiga ya ja ya fita hankalin sa a rarrabe...★★★★
Wuraren 7pm amare da tawagar ta suka iso gidan ta dake federal locust wanda gida ne na gani a fada dan dai yayi kyau sai dai in jealousy zai hana mutum zumudin kyawun sa...
Tun daga tsayuwar motar da amaryar ke ciki aka fara rangada guda sai hayaniya ya kaure aka rinka dokin shiga ciki dan ganin yanayin tsarin gidan..
A daidai lokacin da aka yi ma amarya iso izuwa gidan ta a same time aka bata izinin yin addu'a a zuciyar ta da fara shiga da bismillah hade da saka kafar dama,hakan ne kuwa ya faru dan cikin natsuwa da kamun kai ta gabatar da abin da aka umarce ta da yi sannan tayi sallama ta shiga ciki...
Kyau da tsarin gidan ba a magana sai ga wanda ya gani alhamdulillah tun daga waje har daga ciki cikin gidan komai MashaAllah tsari da zamananci ya sami mazauni a cikin gidan amarya Saima Aliyu..
Bayan an gama zumudin gidan amarya aka natsu aka kawo abincin daga gidan iyayen ango inda mutanin amarya suka hau cin abincin aka ci aka koshi..
Wani sashe ne far apart from sashen amarya aka kai baki dan su kwana kafin komawar su,kawayen amarya kuwa wani daki ne a nan part din but kofar sa is not facing the brides room..
Bayan an nutsa wuraren 10pm su Ummitah da Fadilah suka rankaya dakin amarya dan jiran zuwan abokan ango kafin su tafi..
Tsokana babu irin wacce basu yi mata ba,ita dai tana ta jin su ta kasa magana dan jikin ta ciwo yake mata su kuma basu daina ba har wuraren 10:12pm da tawagar ango suka shigo aka hau cracking jokes da raha daga bisani aka bada kudin siyar baki cikin girma da ilimi,daga haka abokan suka fita suka bar matan a karshe suma matan suka fita suka ma amarya sallama su Ummitah ne a karshe wadanda suka mata albishir da gidan iyayen su zasu kwana sai washegari zasu dawo...
Abin ya taba ta ta so ta ce da su su zauna su kwana a nan amma suka mata nuni da sun matsu su ga iyayen su but washegari InshaAllah as early as possible zasu zo mata,da haka dai suka yi hanyar GRA...Tunda Ummitah ta yo kwanar babbar gate din estate din GRA din nan ta ji babu abin dake mata dadi sama da kuka,kukan dadi ne ko na tunowa da ranar da aka fitar da ita daga gidan da sunar an aurar da ita?ta rasa wace iri ce,ganin sauyin yanayin ta ya sa Fadilah riko kafadar ta tana fadin
"Ummitah i thought this will make you happy but kamar kina cikin wani yanayi"!saurin girgiza mata kai tayi tana fadin
"No not at all wallahi Lilah am just eager to see her"!murmushin gamsuwa Fadilah tayi tana gyada kai game da fadin
"Yanzu kuwa InshaAllah i just pray basu kwanta ba kin san halin auta yanzu kila ta garkame ko ina kar a fita kuma kar a shiga dare yayi"
Dariya suka sake a lokaci daya tunowa da dramar da ake kwasa a gidan da zarar duhu ya fara mamaye estate din..
YOU ARE READING
TAMBARI[The dark hunt]
HumorPeople round the world are being taunted and looked down on due to the feeling of misery and low self worth that is caused as a result of direct and indirect factors which gradually leads to so many social negligence and harassment in many situation...