Story of love

301 62 12
                                    

WATTPAD @SIYAMAIBRAHIM

Mental stability:Confabulation is d filling in of lost memory gaps with manufactured details.

50.Story of love.

  Shigowar Nana dakin ne ya farka da Ummitah completely dake bacci sai ta dago ta dubi Nanan ta ce mata
  "Har kin dawo kenan"?gyada mata kai Nana tayi sai ta mike ta karbi sakon hannun nata da ta aike ta...
  Bude packaged bag din tayi sai ta ga wasu jewelries ne masu kyau da tsada nan ta kuma bude wasu pack din ta ga ring ne,ko da bata sani ba ta san wannan din expensive ring ne..
  Murmushi tayi ta dubi Nana tana tambayar ta inda mai sakon ya tsaya,nan ta fada mata ai yana mika mata ya wuce..

  Mayar da packs din tayi cikin bag din da aka zo da su ciki sai ta mike tsaye ta ta sauko ta tafi wanka Nana kuma ta fita daga dakin..
  Bayan wasu mintuna ta fito ta nufi sashen Ammah ta sanar da ita gift din da yayan nata ya aiko mata da shi,taya ta murna tayi sannan ta fita ta wuce dakin da ake mata gyaran jiki..

  Kasancewar bikin saura kwana hudu so a yau ma Fadilah zata dawo nan gidan su Ummitah dan tun kusan 3 days ago ta zo duk kuwa da yadda Imran ya mata magiyar ta hakura har in ana saura kwana uku bikin ta zo amma ta ki ta ce mai a wannan bikin ya bambanta da na fari because wannan a matsayin blood sister zata taka rawa unlike na farko da tayi playing best friend role..
  Ana tsaka da kalailaye mata fuskar da mixed mask sallamar Fadilah ya doki kunnen ta..
  Bata sami damar juyowa ba sai ganin ta tayi a gaban ta tana tafe tana nishi,dariya ne ya kama Ummitah sai ta dan dara ta ce
  "Lilah anya kina iya tsinana min wani abin kirki a bikin nan kuwa?wannan big tummy naki haka"!!murmushi Fadilah tayi kawai ta zauna a gadon da Ummitah ke zaune ana shafa mata mask din. 
  Dan cige baki tayi ta ce
"Zaki gane ne,ai kadan ya rage kema ki shiga layi ba ga Saima nan ba,wani irin tsokana ce bata min ba but yanzu wa ke cikin halin da nake ciki"?ta ida tana kwafa..
  A wannan karon har da mai shafa mask din sai da ta dan dara sakamakon maganar da Fadilah tayi..

Suna hira ana shafa mata,yayin da angon ya kira kusan sau uku har abin ya ba Fadilah mamaki wai wannan wani irin marar kunyar ango ne duk ya dage sai kira yake.
  Ita dai Ummitah share ta tayi ta rinka daga kiran abin ta,Fadilah ta tabbatar da cewa yar uwar nata ta sami abokin rayuwa kamar yadda ta dade tana mata addu'ar samu kuma ba zata daina ba har sai ta ga zaman lafiya ya wanzu a cikin gidan auren nata dan sanyin Ummitah yayi yawa is possible ma ita uwargidan nata ta zo har gidan ta ta mata rashin mutunci but sai Ummitah ta bata hakuri,so a wannan fannin kam Fadilah na jin sai inda karfin ta ya kare dan some times in Ummitah tayi abu sai ka rantse babu zuciya a kirjin ta tsabar sanyi da kawar da kai..

haka aka yi ta shirye shiryen bikin Ummitah da Ammar har dai biki ya rage saura kwana biyu inda aka fara shirin walimar bikin da a cikin gidan aka yi shirin sa,ko da ranar walimar ta zo,amarya tayi shigar doguwar rigar ta dinkikakke na yadin material ta dora alkyabba a sama,fuskar ta ya sha ado har ta so sauya kamannin ta dan kyau because ba wata fara bace dan haka ba a mata wani dilka ba sama da body pomade sa face mask da aka hada mata na musamman tana amfani da su kuma su suka haskaka mata light chocolate alluring skin din ta sai ta kara kyau ba tare da ta yi hasken dilka ba dan ba a mata amfani da shi ba...
 
  Already su Ammar sun iso nan garin gombe da masu karbar auren duk sun iso,dama tun kwanaki hudu da suka wuce Saudat ta sakawa kan ta ruwan sanyi dan rawar kan da Ammar yayi ta yi a bikin ko nata bikin bai yi sa haka ba,yanzu burin ta shine ta ga amaryar da kyau dan bata taba ganin ta ba ko lokacin da aka yi case din kotu bata damu da sanin ta ba bare ganin fuskar ta ba..
  Ko a ranar da suka shirya dan tafiya gombe sai da Saudat ta saka mai kukan ya daina rawar kan da yake yi ita ta san ya daina son ta but ba sai ya nuna mata ba ta hanyar barin jikin zuwa gombe dan karo mata ba..
  Shi dai bai tanka mata ba dan baya son wani abinda zai bata masa mood din sa a dai dai wannan lokaci na bikin sa.. 
  Dama mahaifiyar sa ta saka ma bikin albarka kuma yana da support din yan uwan sa haka in-laws din sa wato iyayen Saudat,ita kadai ce mai nemar daga mai hankali but bai saurare ta ba,har gori ta yi mai wai bazaura zai aura amma ji duk yadda ya kasa natsuwa,ta tafasa sauke bai ce mata ba,kalma daya ya san in ta fada akan Ummitah ba zai iya kyale ta ba sai ya hukunta ta yake ta jiran ya ji ta furta but har ranar da ya bar ta suka tafi gombe,bata fada mai ba...

TAMBARI[The dark hunt] Where stories live. Discover now