Ravel

266 53 6
                                    

WATTPAD @SIYAMAIBRAHIM

Mental stability:Temper Tantrum is a sudden outburst or violet display of anger,frustration and bad temper.

39.Revel

Saudi Arabia

  Life is as clear as a revel for Ummitah,komai take bukata tana samu at her door step,mahaifiyar ta,kanwar ta are really trying their best dan ganin su kawar mata da wani doguwar tunani marar asali a tattare da ita,dama tun da aka kawo mata kayayyakin ta daga gidan su Asim ta sauya layin wayar ta ta saka sabo dan bata son wani abinda zai hada ta da Niger state da sunan zama bare dawwama again sai dai ko in ziyara zata kai..
  Rayuwar ta na mata dadi yadda take gudanar da shi sannan wata shakuwa da kaunar da ta shiga tsakanin ta da Ammah tana iya cewa ko lokacin tana budurwa hakan bai faru ba,wani kula ta musamman Ammahn ke bata dan tana ganin ya kamata ta saurari diyar ta ta san damuwar ta sannan ta magance mata damuwar,a wurin ta gani take kamar wani golden opportunity ta samu da zata yi amfani da shi wisely ta gyara relationship din ta da na diyar ta..

  A rayuwa yanzu ba abin da take so sama da komawa makaranta dan kara karatu ba dan wanda take da shi bai wadace ta ba sai dan kar ta yi ta zaman gida ko da sun koma Nigeria,plan din ta shine sanar da Ammahn ta akan wannan shawar nata.
  Kamar kullum sun dawo daga zagaye ita da Nana sai suka tsaya a waje dan daukar hotuna bisa tsarin Nana..
  Suna daukar selfie din kenan suka hango wata mota na dumfaro su sai suka dakata dan ganin wa ke motar..
  Ganin ana firfito da kaya ya sa suka kuma saka ido dan ganin wanene.
Bude motar ke da wuya sai ga justice Sulaiman wato Abban su. 
  Rige rigen rungume sa suka yi Ummitah da Nana sai ya rinka yi masu dariya yana kallon su a matsayin kananan yara kamar dai lokacin yarintar su..
  "Abba na welcome baka sanar da mu zaka zo yau ba da ni da Nana mun maka special dinner"!Ummitah ta fada sai yayi dariyar manya yana amsawa Ummitah da
  "A'a,kece dai da kanwar ki baku san da zuwa ta ba amma ita Ammahn ku ai ta sani baku ga shi ya sa yau bata bi ku zuwa yawon zagaye ba"?sai yanzu kan su yayi ringing sai suka rinka dariya..

  A tare suka shigo gidan dan ba a hotel suka yi lodging ba wani gida ne da kusan ko da yaushe in dai Justice Sulaiman da matar sa Hajiya Firdausi suka zo Saudiyya din suke zama ciki..
  Tana fito da sauran kayan abincin da ta dafa ne suka shigo.
  Sassanyar murmushi Hajiya Firdausi ta aikawa mijin nata shima sai ya karba yana maida mata martani har na sa ya so ya zake nasa abin sai ya ba yayan nasu kunya musamman Ummitah da ta jima da barin gidan su sakamakon aure so ta jima da ganin sun yi wannan outward love din but for Nana,she is used to it tana gani kullum sai dai in bata kusa..
  "Welcome hubby"kalmar ta fito daga bakin Ammah sai Nana ta juya ta kalli Ummitah itama ta kalle ta sai suka kuma kallon su Ammah take suka danne dariyar su suka yi gyaran murya..
  "Na same ku lafiya Ammah Noory ta"!a yanzu abin kam sai da ya saka su darawa ba kadan ba,kallon su suka maida kan yayan nasu sai su ma suka yiwa kan su dariya dama da gangar suka yi hakan gaban yaran,all these are part of their family goal and relationship.

   Welcoming Abban aka yi properly sannan aka bar sa ya je yayi freshen up sannan ya dawo su yi dinner kamar yadda su ma suka tafi yi..
 
_1 hour later_
  Wuraren 8pm suka hallara wun cin abinci inda suka saki jiki suna cin abinci suna hira har suka kammala suka dawo parlor inda kujeru suke suka zauna sai Abba yake ba su labarin wani abin mamaki da ya faru a kotu bayan tafiyar su..
  Wai wani na tambayar sa ko shine mahaifin Ummitah ciki har da sauran judges dake kotun sai ya kyale su dan tambayar tasu bai da amfani an rigada an yi hukunci. 
  Mamaki suma suka ji su ma sai suka yi addu'ar kariya sannan suka koma hirar abinda ya dame su daga nan ne Ummitah ta sako zancen son komawar ta makaranta sai ta ga Abban nata ya gyada kai ya dube ta ya ce
  "InshaAllah zaki koma sai dai wani hanzari ba gudu ba,idan mijin da zaki aura kuma ya ga ba zai iya barin ki ba fah"!?wani irin fadi gaban ta yayi jin an kira mata sunan miji,ta tsani jin sunan sai ta dubi Abban nata idanun ta sun kawo ruwa ta ce
  "Abba ni ban kuma sake yin aure"!murmushin manya yayi ya dubi matar sa ya dubi Nana sannan ya dube ta ya ce
  "You have to,i and your Ammah need grandchildren,your sister have to become an aunty before she gets hers,you have to be called a mother ko da sau daya ne dan kema ki yi alfahari Ummitah uhum!?dan haka ke da aure dole ku kuma haduwa we need an extension in our family,ko baki ga numbers din mu bane,we were just three sai da kika dawo muka zama four,ba burin mu ba kenan zama a mu hudu muna son mu fi haka yawa,sanin kan ki ne we don't count on our other relatives daga mu sai mu so we have to stretch our family bond hakan ba zai faru ba sai mun yawaita,Nana bata gama girma ba,bata kai matsayin aure ba she is still young akwai karatu a gaban ta dan haka kar ki ga tana nan ki saka ran ai zata yi aure itama,no,ba yanzu ba a kalla she have 10-11 years of study awaiting for her,so you have to focuse and settle down da wani a matsayin mijin ki not all men are as worthless as your first husband ok"?kasa danne hawayen ta tayi sai ta bar su suna zuba..
Muryar Abban nata ne ya datse mata hawayen nata inda yake fada mata
  "Wannan yaron me sunan sa!?AbdulHakam,ya dawo kuma ya ce da gaske auren ki yake son yi a second time kuma,i was about scolding him but sai na ce mai ya je zan neme sa"..da sauri ta dubi mahaifin nata tana mamakin hirar sa da AbdulHakam din..
  Last time da suka hadu wasn't a good meeting dan har threatening nasa Abban ta yayi akan sai ya sa an kai sa prison in ya kuma tunkaro mai gida it wasn't an episode that one will like to see again..
  Ta yi mamakin hakan sai dai bata ce komai ba tana ji da rarrashin zuciyar ta akan wannan batu da mahaifin ta ya dauko mata daga tsakiya..
  Ko kallon ta mahaifiyar ta bata yi ba dan ta san da kwanan zance ya sanar da ita tun a waya..
  Nana kam cat face ta saka jin an yi batun aure ga yayar ta ita kam bata so kuma bata son su sake rabuwa..
  Sai kawai ta fashe da kuka wai Abban su na so ya siyar da yayar ta,tsakanin ta da Allah take kukan shi kam kallon ta yayi ya girgiza kai ya dubi matar sa ya ce
  "Tashi mu tafi they are no longer kinds anymore sun san me ke damin su musamman Ummitah"!tashi Ammah tayi suka bar Ummitah a zaune cikin halin tunani da nazarin ina makomar rayuwar ta zai dosa kuma..
  Nana ce ta matso kusa da ita tana rungume ta daga gefe hade da yi mata kalamai masu kwantar da hankali har ta dora da.
  "Kin ga aunty Ummi ai Abba ya ce ba duka suka zama daya ba,you see i never liked your ex-husband shi yasa ban taba zuwa gidan ki ba but kin ga in yaya AbdulHakam ya aure ki a nan gombe zai aje ki kusa da gida duk dai nisa na san ba zan dau sati guda mai kyau ban zo ganin ki ba bare Ammah ai kin ga baki da tsoro kuma,no one will ever harm or molest you anymore ki yarda kawai da yaya AbdulHakam kin ga shine first love din ki ya hakura bai same ki ba yanzu kuma ya dawo please give him a second chance kin ji"?kallon ta Ummitah ke ta yi jin kalaman manyan matan dake fitowa daga bakin ta. 
  Hugging nata back tayi tana silent weeps sai kuma ta tambayi Nanan...  
  "Kina ganin in yarda in kara shiga hannun da namiji Nana?a ganin ki ba zan kuma cutuwa ba"?da sauri Nana ta amsa mata da
  "No sister,kin manta ne?mu fah ke da Abban mu the chief Justice Sulaiman Abdullahi Mai sa'a wa ya isa ya kuma tempering da ke bayan yanzu an san ke din wacece,ai ko ni na ishi wanda ke kokarin harming naki bare Abba"!!dariya maganar nata ya ba Ummitah sai ta dara while tears are rolling down her cheeks,cikin hawayen ta tambayi Nana.
  "Did you think i am yet ready for another relationship"?gyada mata kai ta yi sai ta kuma tambayar ta
  "But why didn't he call or contact me"?wato shi AbdulHakam din kenan sai Nana ta amsa mata da
  "Maybe he couldn't reach you kin san kin sauya layin wayar ki kuma kin gargadi aunty Fadilah da kar ta ba kowa numbern maybe shi ya sa"!reasoning tayi da dalilin sa da Nana tayi assuming har tayi mata instance da shi..
  "Okey let's see ko zai neme ni ko cigaba da boye boye zai na min"!dariya Nana tayi tana rungume ta hade da tsokanar ta da
  "I can't wait to become an aunt"!dan bige ta Ummmitah tayi tana mai ture ta daga jikin ta ta mike tana fadin
  "Ki zo mu kwanta da wuri gobe in Allah ya kai mu zaki raka ni gidan su Yasmin"!tabe baki Nana tayi tana fadin
  "Ni dai aunty Ummi da kin rabu da wannan Yasmin din sam bata min ba ga rawan kai da iyayin tsiya ai wallahi kar ki yarda Abba ya san kin kulla abota da ita dan in ya kalle ta kawai ko a hanya kuka hadu ta rinka gudun ki kenan kin ga ai sai ta ja maki magana a rinka ganin kamar wani mugun abu gare ki"!dariya sosai zantukar kanwar nata ya bata dan tun da suka iso Saudiyya suka hadu da Yasmin a airport suka dan gaisa toh ganin duk daga Nigeria suke sai Yasmin ta sake sosai da Ummitah dan ita Yasmin irin mutanin nan ne da ake kira da open minded people basu boye damuwar su ko abin farincikin su,so Nana na mata kallon mai iyayi da rawan kai ne dan su Abban su tun yarintar su bai masu sakewar da zasu taso da iyayi ba dan wai suna yayan sa. 
  "Nana ki zo ki kwanta da wuri we are visiting Yasmin tomorrow inshaAllah kuma kika bari na ji pim!!wai Abba ya hana mu zuwa ni da ke ne"!!turo baki Nana tayi tana gyara zama hade da fiddo chicken shawarma din da suka dawo da shi tana niyar fara ci dawowa da baya Ummitah tayi ta fizge shawarma din tana hararan ta hade da fadin
  "You ate more than 1000 calories today,just today ta yaya kike son ganin positive result din exercise da kike yi"!?ta dalla mata harara sannan ta wuce zuwa dakin baccin su da shawarma a hannun ta,tana shiga ta bude karamin mini fridge din dakin ta saka ta rufe..
  Wanka ta shiga ta yi sannan ta dawo ta sauya zuwa kayan bacci ta kwanta abin ta..
  There is one thing jumping up and down in her heart kuma ba komai bane illa AbdulHakam yayan aminiyar ta Fadilah..
  Juye juye ta shiga yi a gadon tana tunanin shekarun baya yadda suka gudanar da soyayyar su mai tsafta da karamci,zuwar Asim rayuwar ta komai ya sauya she never knew zata kuma samin yancin kan ta sai yanzu,ta san ko da auren AbdulHakam tayi toh ba zata yi kuka da shi ba dan shi din ne masoyin ta na asali..

  Daukar wayar ta tayi ta kira Fadilah,har ya kusa katsewa sai aka daga,cikin muryar bacci Fadilah ta gaida ta itama ta maida mata gaisuwar har da tsokana sannan ta tambaye ta ko ina yayan ta yake ita kam bacci sai ta ce wanne ciki nan Ummitah ta fada mata sunan..
   Ai a 360 Fadilah ta mike daga kwancen da take ta wartsake ido tana kiran asalin sunan Ummitah..
  Murmushi kawai Ummitah tayi ta labartawa Fadilah komai da ya faru nan Fadilah ta rink mamakin karfin halin yayan nata sai dai ta san abinda rai ke so in bai samu ba toh bai taba samin natsuwa sai ya mallaki wannan abin..
  Yar hira suka yi kafin daga bisani suka yi sallama Ummitah ta mayar da wayar side drawer ta gyara kwanciyar ta ta rumtse idanun ta wai ko baccin zai zo amma haka ya ki zuwa.
Fargaba kala kala take fuskanta a zuciyar ta game da batun AbdulHakam ta dandana zaman aure da da namiji kuma bata ji dadin sa ba sai dacin ta da baurin ta,tsoro take ji sosai akan kara bude zuciyar ta ma wani da namiji kuma..
  Tana tsaka da tunanin ta ta ji shigowar mutum bata dai daga dan ganin wanene ba sai ta cigaba da baccin..
  Ji ta yi an bude fridge leather ya fara kara,murmushi tayi dan ta san wacece sai ta cigaba da yin shiru har sai da aka bude leather za a fara cin abin cikin leather din ta ce
  "Nana kina cin abin nan zan saba maki yau din nan sai hannu na ya kwana kumatun ki"!!a tsorace ta maida ta wuce toilet dan yin wanka itama..
  Ummitah na nan na jiran ta har ta dawo ta sauya kayan ta zuwa na bacci ta hau gadon ta kwanta abin ta..
  Sai da ta jima da kwanciyar har bacci ya fara yi mata nisa sannan Ummitah ta matso kusa da ita ta kare mata kallo yadda ta so fin ta ma a girman jiki sai ta yi murmushi hade da rungume ta daga baya,ba jimawa itama baccin ya dauke ta..

★★★★
Ko da gari ya waye suka shirya dan zuwa gidan su Yasmin Nana dai kamar ta fadawa Abban su amma tana tsoro haka dai tayi shiru suka tafi gidan..
  Haba haba ta tarbe su cikin sakin fuska da murna dan basu taba visiting juna ba sai yau..
  Cike masu gaba tayi da kayan alatu na dangin ciye ciye da drinks,ko daya Nana bata taba ba haka Ummitah sai hirar da suka yi..
  Suna tsaka da hirar me wani mutum da Ummitah ke gasgatawa a matsayin mahaifin Yasmin ya shigo parlorn yana kiran Yasmin din..
  Duban su Ummitah tayi tana fada masu mahaifin ta ne,har kasa suka gaida sa yana tambayar su ya yan gida..
  Ita diyar tasa ce ta mai bayanin su,ai kuwa ya kafe Ummitah da ido sai kallon ta yake yi kamar maye,tun tana basarwa har kallom ya addabe ta ta riko hannun Nana ta ce ma Yasmin gida zasu tafi..
  Har cab Yasmin ta raka su da kayan da basu ci ba bayan ta masu packaging,abin da mahaifin Yasmin ya ma Ummitah na ta damin ta dan ya manyanta zai ma girmi Abban ta amma yake mata irin wannan kallon..
  Ko da suka iso gida suka fito da gangar Nana ta bar kayan cikin cab din dan ita Yasmin bata mata ba ba wai dan bata da kyau ko aji ba a'a kawai hankalin ta ne bai bata da tarayyar su ba ita da yayan ta..

  Haka Ummitah ta rinka tsoron mutumin nan dan har kiran ta yayi wai ya ji ko sun koma gida lafiya amma ta kashe,sannan ta rasa ya zata sanarwa Abban ta dan ta san shi kadai ne maganin wannan abin,bata da zabi dole ta sanar da shi dan ita yanzu irin yadda take tsoron maza ko ran ta sai haka..
  Nana kuwa ta rinka aibata abubuwan da Yasmin ta saka masu a cab wai su ci in sun dawo gida,Ummitah dai shiru tayi tana tunanin yadda zata fadawa Abban ta yayi saurin shiga tsakanin ta da mutumin dan ta razana ba kadan ba kallon da yake ta mata ba kallon alkhairi bane....


#TT can be seen in maladjusted children and can be demonstrated in so many ways such as physical body rigidity/resistance,rolling on the ground,unnecessary screaming,aggression,banging,crying,throwing of objects,biting,etc.all these occur as result of faulty parental attendance,inadequate family environment,mentally and physically handicap condition,influence of mass media,influence of social relationship,etc..TT can be managed through different ways depending on the specific type that the child is portraying..

TAMBARI[The dark hunt] Where stories live. Discover now