Shafi na talatin da biyu

125 23 3
                                    

🏘🏘🏘🏘🏘🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️

MATAN QUATERS

✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
Kulsum Bappah Azare
Ummu iman

Ku bini a shafi na:
Wattpad @kulsumbappa
Facebook: @ kulsum Baffah
Gmail:ukb696354.kb@gmail.com
EMAIL: Ukb696354@email. Com

🖊️🖊️BAUCHI HAUSA WRITER'S ASSOCIATION🖊️🖊️
( BAHWA 📝)

_(Matattarar zaƙaƙurai, haziƙai, fasihai, mashahurai, kuma sanannun marubuta)👌🏻

3️⃣2️⃣

Bai fahimci mi take ce mishi ba,
Hanyar waje ya kama ko zai dawo hayyAcin shi

Innalillahi wa inna ilaihir rajiun!!!

Fitar shi ke da wuya yayi tozali da MUBARAKA zuciyar shi ta bashi yaje ya shaketa kowa ma ya huta
Kawai wata zuciyar ta hana shi
Ya kare mata kallo fuskarta tamkar wanda tai wanka cikin KURKUR ( CURCUMIN ko TUMERIC) tsabar shafe shafen da tayi kasan idonta har wani tabbare tabbaren ja da baki yayi,
Xuciyar shi ta kara kuntata
Ya juya ya shiga gida shidai abincin da bai ci ba kenan,
Ya shirya ya fice wajen aikin shi
Yana ta tabka da warwara.

ZUBAIDA tace " Abba nagode sosai Allah ya kara bude,
Ya kara maka lafiya,"

Ameen hajiyata yanzu ke kayan gadon ruwan SHANSHAN BELI kika zaba wa kanki ko wa Auntyn naki???

Ammynta ce ta bada amsa da yake ita ZUBY ragowar mutanen da ce, Allah Ya yas-sare mata tana da ta ido,

ita ruwan SARARIN SAMANIYA ta zaba a madafinta da labulayyanta,
Yar uwarce ta zaba mata wannan kalar,

yauwa an karbo dinkunan kuwa hajiya?

Inason akai wa Auntyn nata da wuri saboda ta fara hidima da wuri nasan KASIMU yadda auren yazo mishi ba shiri nasan bai shirya komai ba,

Yauwa hajiyata dazu baki ga sakon kudi a wayar ki ba ce!??

"Lah Abba ai ko nagani"

To kije ki yiwa yaran na kun sayayya.
Tai godiA ta basu waje don nauyin maganar auren take mata.

AlhAji BAGUDO ya numfasa

Allah ya nufa kar yar nan hakan ya sa ta yiwa yarinyar nan dagawa wata ran,

Kai haba kasan halin yarka ai
Ba dai wannan ba.

To kinsan wani lokacin hali kan iya sauyawa,

Haba Alhaji kaine mutum na farko da ya kamata ka bawa zubaida wannan shaidar fa

Hake ne Ammy
Alhamdulilla,
larabbawa suna cewa " SHUKRAN LA FAHRAN"

Allah yasa hajiya.


Yanxu Bahijja tafiyar zakiyi?

Eh to maman salima ai mama ce tace min na koma, ta zuge zip din akwatin ta mikar dashi,
To Aunty Allah ya kyauta,

Tabbb lalle ai kuwa IMRAN sai ka gane da ruwa ake shayi,

Ta saka wancan ta kunce haka dai ta wuni cikin kunata,

Tashin hankali maimakon taji sassauci a zuciyarta amma ina!!!
Kamar wanda ake mata zuga zugi, ta fantsama falon imran ta fasa talabijin, ta zirdo shi kasa kai take wurin yayi kaca kaca,

Yayinda imran yake jiyo sautin fashewar abu yayi,
a tunaninshi tiles ne ya subuta ya fado,

Turus!

Yayi yana karewa wa wurin kallo tare da juyawa yana karantar yanayin da MA'UN take ciki,
cikin biyu za'ayi daya:
Imma dai kwakwalwarta ta samu damuwa - ko kuma motsuwar kwakwalwa da aka ce masana lafiyar kwakwalwar dan adam suka ce"ko wani dan adam a yini yakan sami tabin kwakwalwa na tsawon minti guda"
Amma akasin haka ya gani,
Tsantsar rashin mutunci ne da tashin hankali ya gani a kwayar idonta,,
Tana huci kai kace kumurci ce,
Zuciyarta tsabar kunci da kyar take fusgar numfashi.

MATAN QUATER'SWhere stories live. Discover now